Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
Published: 28th, April 2025 GMT
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya.
Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi.
Hakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.
A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Asabar da ta gabata ce Fadar Sarkin Musulmin ta ba da umarnin duban watan na Zhul Qi’ida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sarkin Musulmi Shawwal
এছাড়াও পড়ুন:
Tsagin Damagum da Anyanwu sun shirya mamaye hedikwatar PDP a yau
Sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP yayin da ɓangarori biyu da ke taƙaddamar — na Umar Iliya Damagum, muƙaddashin shugaban jam’iyyar, da na Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na ƙasa — ke shirin mamaye hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja yau Litinin.
A ranar Asabar, yayin da Damagum da wasu mambobin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) suka gudanar da taro a Legacy House da ke unguwar Maitama, bangaren Anyanwu kuwa ya gudanar da wani taro daban a ofishinsa da ke Wuye, Abuja.
Majiyoyi sun shaida mana cewa bangarorin biyu sun shirya komawa Wadata Plaza, wato hedikwatar jam’iyyar PDP, domin gudanar da ayyuka daga wurin — lamarin da ya tayar da hankalin ma’aikatan hedikwatar.
Wani babban jami’in jam’iyyar ya ce, “Abin da muke ji shi ne ɓangaren Anyanwu ma zai zo ya gudanar da taro a ofishin jam’iyyar yau (Litinin).”
Ya ƙara da cewa, “Tun bayan hukuncin kotu na ranar Juma’a, ɓangarorin biyu sun dinga gudanar da taruka domin tsara dabarunsu. Idan Anyanwu da nasa suka iso Wadata kuma Damagum da nasa NWC suka bayyana, ba mu san abin da zai faru ba. Ma’aikata na cikin fargaba sosai.”
Wata majiya ta kuma ce bangaren Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, na ƙoƙarin jawo wasu mambobin NWC zuwa gare su. “Suna neman rinjaye ne, idan suka fi yawan ɗayan bangaren, komai zai iya faruwa,” in ji ta.
Duk da wannan rikicin, majiyoyi sun ce Damagum da gwamnonin PDP sun dage cewa taron gangamin zaben shugabanni na ƙasa da aka shirya a gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo daga 15 zuwa 16 ga Nuwamba, zai ci gaba kamar yadda aka tsara.
Wani jigo ya ce, “Ko bayan hukuncin kotu, shugabancin jam’iyyar ya umarci mambobi su ci gaba da shirye-shirye. Idan hakan ta tabbata, ɓangaren Anyanwu ma na iya shirya nasu taron daban, domin sun daɗe suna shirin hakan.”
Yadda rikicin ya samo asaliA ranar Juma’a ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana PDP gudanar da taronta na Ibadan, har sai ta bi tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Mai shari’a James Omotosho ya yanke hukunci cewa jam’iyyar ta keta kundinta da dokokin zaɓe ta hanyar kasa gudanar da sahihin zaɓen shugabanni a jihohi 14 kafin sanar da taron.
Masu shigar da ƙarar su ne shugabannin jam’iyyar na jihohin Imo, Abia, da sakataren yankin Kudu maso Kudu — Austin Nwachukwu, Amah Abraham Nnanna, da Turnah Alabah George.
Bayan hukuncin, Damagum ya kira taron gaggawar NWC a ranar Asabar, inda aka dakatar da wasu mambobi huɗu da ke da alaka da ɓangaren Wike na tsawon wata ɗaya.
Wadanda aka dakatar sun haɗa da Samuel Anyanwu (Sakataren jam’iyya na ƙasa), Kamaldeen Ajibade (SAN) (Lauyan jam’iyya), Okechukwu Osuoha (Mataimakin lauya), da Umar Bature (Sakataren Tsare-tsare).
Kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan NWC ta zargi mambobin da rashin ladabi da karya doka.
Ya ce, “An dakatar da su na wata ɗaya kuma an miƙa batunsu ga kwamitin ladabtarwa domin karin mataki.”
Ya ƙara da cewa, Setonji Koshoedo, mataimakin sakatare na ƙasa, zai rike mukamin sakataren a wucin gadi, yayin da Jacob Otorkpa, darektan sashen shari’a, zai kula da harkokin Shari’a na jam’iyyar na ɗan lokaci.
Sai dai a martani, bangaren Anyanwu da ke goyon bayan Wike, su ma sun gudanar da taro inda suka dakatar da Damagum da wasu shugabanni shida.
Anyanwu ya ce an ɗauki matakin ne domin “ceto jam’iyyar daga rushewa” da kuma “maido da martabar shugabanci.”
Ya bayyana cewa Damagum an dakatar da shi ne saboda “rashin iya jagoranci, almundahana da karya umarnin kotu,” sannan ya sanar da cewa Mohammed Abdulrahman, mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Arewa ta Tsakiya, zai zama muƙaddashin shugaban ƙasa.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da Debo Ologunagba, Taofeek Arapaja (mataimakin shugaban kudu), Daniel Woyenguikoro (akwatin kudi), Sulaiman Kadaɗe (matasa), da Setonji Koshoedo.
“Kokarin murƙushe adawa dole a daƙile shi” — Olawepo-HashimTsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi gargaɗin cewa rikicin da PDP ke ciki na iya zama barazana ga dimokuradiyyar ƙasa.
Ya ce hukuncin kotun da ya dakatar da taron Ibadan wani yunkuri ne na “murƙushe jam’iyyun adawa” domin bai wa jam’iyya mai mulki damar kafa mulkin jam’iyya ɗaya.
Olawepo-Hashim, wanda ke sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce, “Abin da ya faru a kotu ba keɓantacce ba ne. Tsari ne da aka tsara don lalata tsarin jam’iyyu masu yawa.”
Ya kuma yi tir da rahoton da ke cewa tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, an hana shi sayen fom ɗin takarar shugaban jam’iyyar, yana mai cewa hakan “cin fuska ne ga dimokuradiyyar cikin gida.”
Ya zargi wasu “’yan biyar-biyar” a cikin jam’iyyar da yin aiki da jam’iyya mai mulki domin hana gyare-gyare, yana mai kira ga “’yan dimokuradiyya na gaske su tashi tsaye su kare ’yancin siyasa a Najeriya.”
“Damagum zai gamu da irin ƙaddarar Ayu” — FayoseA nasa ɓangaren, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce PDP ta shiga halin “sumewa” kuma babu alamar dawowa daga rikicin da ke damunta.
Yayin da yake magana da ’yan jarida a Ado-Ekiti, Fayose ya ce Damagum zai “bi sawun tsohon shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu,” idan aka ci gaba da tafiya a wannan hanya.
Ya ce, “PDP ta gaza saboda rashin shugabanci da rikice-rikicen cikin gida. Gwamnoni da jiga-jigai da dama sun bar jam’iyyar. Ka ga akwai wani fata na dawowa da karfi? A yanzu dai babu.”
Fayose ya roƙi sabon muƙaddashin shugaban, Mohammed Abdulrahman, da ya gyara jam’iyyar, ya tabbatar da gudanar da zaɓen shugabanni a jihohi kafin taron ƙasa na gaba.
Ya kuma zargi Damagum da “karɓe ikon jam’iyyar da makirci”, yana mai cewa, “Damagum bai kamata ya zama shugaban jam’iyya ba. Ya samo kansa ne saboda wasu muradu, kuma hakan ne ya haifar da wannan rikici. Waɗannan shugabanni na yanzu sun zo ne don binne jam’iyyar.”
Fayose ya yi gargaɗi cewa idan PDP ba ta koma kan turbar asali ba tare da yin sahihin gyara ba, jam’iyyar na iya rushewa gaba ɗaya kafin zaben 2027.