Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699

Matatar man Dangote ta sake rage farashin man fetur ɗin da take sayar da man, inda ta rage farashin man fetur ɗin daga Naira 828 zuwa Naira 699 kan kowace lita.

Bayanan farashin da aka wallafa a shafin  kasuwancin farashin man fetur a Petroleumprice.ng a ranar Juma’a sun nuna cewa matatar ta aiwatar da wani bita na baya-bayan nan, inda ta rage farashin man da N129 a kowace lita – ragin kashi 15.58 cikin 100.

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina

Wani jami’in matatar man da ya zanta da manema labarai bisa sharaɗin sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin tsokaci a bainar jama’a, shi ma ya tabbatar da yin ragin.

Ya ce, matatar man ta rage farashin man fetur zuwa N699 kowace lita.

Sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar 11 ga watan Disamba, 2025, wanda ya yi daidai da farashin man fetur karo na 20 da matatar man ta sanar a bana.

Ragi na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki biyar bayan shugaban matatar, Aliko Dangote ya jaddada ƙudirinsa na ganin an tabbatar da farashin man fetur a cikin gida cikin “madaidaicin farashi a kasuwanni” duk kuwa da taɓarɓarewar da ake samu a duniya da fasaƙwaurin da ake yi a kan iyakokin Najeriya.

Da yake bayani bayan ganawar sirri da shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ranar 6 ga watan Disamba, Dangote ya ce farashin zai ci gaba da faɗuwa yayin da matatar man ke ƙara yawan kayan da ake fitarwa da kuma yin gogayya kai tsaye da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bankin Ajiya na Jihar Jigawa Ya Karamar Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu
  • Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai
  • Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Kiyasta Naira Biliyan 3 Don Ayyukan Hajjin 2026
  • 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
  • Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare
  • Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan
  • Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria