Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya, kamar yadda ta yi a lokacin rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, ta yaya masana’antunta za su farfado bisa wannan tsarin?

 

Hakazalika, babu yadda za a yi Amurka ta sake zama cibiyar masana’antun duniya bayan da ta yi watsi da matsalolin da ake fuskanta a zahiri kamar sauyin yanayi, wanda ayyukan masana’antu ne suka haifar da shi tun farko.

Bari mu dauka cewa Trump zai iya cimma nasarar aiwatar da manyan gyare-gyare game da tsarin kasar lokaci guda, zuwa kyakkyawan tsarin siyasa da tattalin arzikin kasar duk da cewa akwai rashin jituwa tsakanin jam’iyyun kasar. Kana bari mu dauka cewa mutanen Amurka da ma duniya baki daya za su koma sayen yawancin kayayyakin da ake samarwa a Amurka. Har yanzu an bar mu da wata tambaya, shin za a samu isassun Amurkawa da za su yarda su yi aiki a masana’antunta, kuma za su yi hakan kan albashi mara tsoka idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, bayan da Trump ya kori kaso da dama na baki daga kasar ta Amurka? (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali

Ministan harkokin wajen kasar Brazil Mauro Vieira ne ya jagoranci wannan taro, inda bangarori daban daban suka tattaunawa kan yadda kasashen BRICS za su karfafa zaman lafiya da tsaron duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
  • Wang Yi: Neman Sulhu Da Ja Da Baya Riba Ne Ga Masu Son Cin Zali
  • Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata
  • Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara