Muhimman Dalilan Kirkiro Da Shirin Inganta Aikin Noma ‘SAPZ’
Published: 27th, April 2025 GMT
Kazalika, a cikin daukacin gwamnatin tarayya da kuma na jihohin kasar, an tsara yadda za su dakile kalubalen da fannin aikin noma da kuma yadda za a sama wa manoman kasar sauki, bunkasa rayuwar mazauna karkara da kuma habaka tattalin arzikin kasar.
Akasarin manufar aikin na SAPZ shi ne, domin inganta aikin noma a karkara, maimakon fitar da amfanin gona kamar irin su Rogo, Shinkafa, Tumatir da kuma Koko zuwa birane ko kuma kasar waje, za a tanadar da kayan aiki a yankunan da aka tsara za su amfana da shirin, domin manoman yankin su samu ribar da ta kamata.
Daya daga cikin manyan matsalolin da ake samu a Nijeriya ita ce, gibin da ake samu a bangaren aikin noma domin samun riba.
Amma a wadannan yankunan da za a gudanar da aikin, za a samar da masana’antun sarrafa amfanin gona, kayan adana amfanin gona, wutar lantarki mai dorewa, tituna da kuma cibiyoyin bayar da horo.
Nijeriya dai, ta shafe shekaru tana fama da karancin abinci, asarar da manoma ke tabkawa bayan sun yi girbi da kuma matsalar rashin aikin yi a tsanakin ‘yan kasar.
Har ila yau, aikin zai kuma samar da damar fitar da amfanin gona zuwa ketare, wanda hakan zai samar wa da Nijeriya biloyin Nairori.
Ta hanyar aikin na SAPZ, Nijeriya za ta iya samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, rage asarar da ake fuskanta duk shekara, bayan girbe amfanin gona da kudinsu ya kai kimanin Naira tiriliyan 3.5, samar da ingantacce wajen adana amfanin gona, samar da cibiyoyin bayar da horo ga manoma da kuma cike gibin da ake da shi a kasuwannin kasar.
Kashi na farko na aikin, an kaddamar da shi ne, a 2022, ta hanyar ware dala miliyan 538, wanda kuma za a wanzar da shi a cikin akalla sama da shekaru biyar.
Aikin na Bankin AfDB, zai samar da dala miliyan 210, inda kuma Bankin IsDB da IFAD, za su samar da dala miliyan 310, sai kuma gwamnatin tarayya da za ta samar da dala miliyan 18.05.
Jihohin Da Za Su Amfana Da Aikin:
Jihon da za su amfana da aikin su ne; Kaduna, Kano, Kwara, Kuros Riba, Imo, Ogun, Oyo, sai kuma Abuja.
A yanzu dai, Shugaban Bankin AfDB, Akinwunmi Adesina da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne, ke jagorantar aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: dala miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Dole Ne Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Samar Da Ayyukan Yi Da Rage Talauci — Bankin Duniya
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200.
Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki.
Ko da yake, ya nuna cewa kalubalen shi ne don karfafa kwanciyar hankali na tattalin arzikin kasa da habaka yanayin tattalin arziki ta hanyar zurfafa gyare-gyare mai fa’ida.
“Akwai bukatar tattalin arziki ya samar da karin ayyukan yi masu inganci da kuma rage talauci a tsakanin al’umma.”
Mukaddashin Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Taimur Samad ya ce, “Nijeriya ta samu ci gaba mai ban sha’awa don maido da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki, tare da ingantuwar yanayin kasafin kudi, yanzu Nijeriya na da damar inganta adadi da ingancin kashe kudade na ci gaba, kara saka hannun jari kan rayuwar Dan’adam, kariyar zamantakewa, da ababen more rayuwa.
“Rarraba dukiyar al’umma na iya fara kaucewa tsarin da ba a dawwama a baya, a maimakon haka wajen biyan manyan bukatu na ci gaban Nijeriya, ciki har da gwamnati ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da muhimman ayyukan gwamnati da kuma zama mai ba da damar ci gaban kamfanoni masu zaman kansu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp