Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma Francis
Published: 27th, April 2025 GMT
Dubun dubatar mutane mabiya Addinin Kirista ne suka yi cikar ƙwari a jana’izar ƙarshe da ake yi wa jagoran ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis, a cikin yanayi na matakan tsaro.
Hukumomi a birnin Roma sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen St. Peter’s Square na Fadar Vatican, inda ake gudanar da jana’izar Fararoma Francis.
Tun da sanyin safiya dubun dubatar jama’a suka yi wa dandalin cikar ƙwari domin samun damar yi wa Fafaroma Francis ganin ƙarshen a jana’izar da ke zama guda a cikin mafi girma a duniya.
Mutum dubu 400 sun halarci jana’izarAƙalla mutum 400,000 ne suka halarci jana’izar Fafaroma Francis a dandalin St Peter’s da ke Vatican.
Haka kuma sun ga lokacin da aka ɗauki gawarsa zuwa wajen da aka binne shi a cocin Santa Maria, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gidan Italiya.
“Mun yi ƙiyasi cewa mutane 400,000 ne tsakanin waɗanda suka halarci dandalin St Peter’s da kuma waɗanda suka tsaya kan tituna suka kalli jana’izar,” in ji Matteo Piantedosi.
Shugabannin duniya da suka halarci jana’izarShugabannin manyan kasashen duniya ciki har da na Faransa da Amurka da wasu jagororin gwamnatoci ciki har da na Jamus da Burtaniya da fitattun sarakunan duniya irinsu na Jordan, duk sun halarci jana’izar.
Shugaba Putin bai samu halartar jana’izar ba, amma kuma takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ya halarta dandalin na St. Peter’s don yi wa Fafaroma Francis ganin karshe.
Daga cikin fitattu a dandalin St Peter da safiyar ranar Asabar akwai Yarima William na Birtaniya da shugaban Amurka Donald Trump da wanda ya gada, Joe Biden da Firaiministan Birtaniya, Sir Keir Starmer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Jana’izar na zuwa ne bayan kammala yi wa gawar Fafaroma ganin bankwana na tsawon kwanaki da wasu dubban mabiya ɗarikar ta Katolika suka yi a cikin yanayi na juyayi da alhini.
Fafaroma na farko da aka binne a wajen Vatican cikin shekaru 100Fadar Vatican ta tabbatar da cewa an binne Fafaroma Francis a cocin Santa Maria Maggiore.
“Fafaroma Francis shi ne mutum na farko cikin shekara 100 da aka binne a wajen Vatican, kuma an binne shi a asirce, inda makusantansa suka yi masa gaisuwar ban-girma,” a cewar sanarwar da fadar ta fitar.
Shi ne Fafaroma na farko tun bayan Leo XIII, wanda ya mutu a 1903 — da aka a binne a wajen Vatican.
Kowane lokaci idan ya koma birnin Rome daga balaguro, ya sha ziyartar Santa Maria Maggiore.
Cocin dai yana wajen Vatican da ke tsakiyar birnin Rome.
Mutumin farko daga Latin Amurka da ya zama FafaromaƊan ƙasar Argentina, wanda ya yi jagorancin majami’ar Katolika tsawon shekaru 12, ya mutu ne a ranar Litinin da ta gabata yana da shekaru 88, bayan fama da mutuwar ɓarin jiki da bugun zuciya.
Kiraye-kirayen zaman lafiyaFrancis ya sha yin kiraye-kirayen kawo ƙarshen rikice-rikicen duniya a zamanin jagorancinsa, kuma jana’izarsa ta bai wa shugaba Trump na Amurka, wanda yake koƙarin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine damar ganawa da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelenskiy a cikin majami’ar Saint Peter Basilica.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fadar Vatican Fafaroma Francis halarci jana izar Fafaroma Francis a wajen Vatican a jana izar
এছাড়াও পড়ুন:
Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP.
Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC.
Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15A ranar Juma’a, ‘yan majalisar Ribas guda 16, ciki har da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, da suka sauya sheƙa zuwa APC.
Amaewhule, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rarrabuwar kai da aka samu a PDP.
Hakazalika, kakakin ya ce yana son ya yi aiki tare da Shugaba Bola Tinubu, bayan ya gano yana da kyakkyawan tsari na ciyar da ƙasar nan gaba.
Da yake magana da manema labarai bayan duba wasu ayyuka a Abuja, Wike, ya ce ’yan majalisun ba su tuntuɓe shi game da batun sauya sheƙarsu ba, amma ya ce suna da ’yancin zaɓen abin da suke so.
Ya ƙara da cewa ba duka ’yan majalisar ne suka fice daga PDP ba.
Ya ce, “Ni har yanzu ina PDP. Ba dukkaninsu ne suka fice daga jam’iyyar PDP ba. Ina ganin 16 ko 17 ne suka fice daga cikin 27. Har yanzu muna da kusan mutum 10, kuma za mu ci gaba da aiki tare da su.”
Wike, ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, amma ya ce kowa na da ’yancin zaɓen abin da yake so.
Ya ɗora alhakin ficewarsu kan rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi, inda ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bai wa mutane damar barin jam’iyyar idan ta rabu gida biyu.
Ya ce tun da farko ya bai wa shugabancin PDP shawara su gyara jam’iyyar, tare da gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki ba jam’iyyar za ta ci gaba da yin asara.
Wike, ya ƙara da cewa suna ci gaba da ƙoƙari domin sauran mambobin PDP su haɗa kai don yaƙar jam’iyyun adawa.