Damfarar CBEX: Mutum 8 da EFCC ke nema ruwa a jallo
Published: 26th, April 2025 GMT
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC, ta ayyana neman wasu jami’an CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ’yan kasar miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta ranar Juma’a.
An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji A soma laluben watan Zhul Qi’da — Sarkin MusulmiSanarwar ta ambato EFCCn tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama’a su zuba kuɗi don samun riba – daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu.
Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da Adefowora Abiodun Olaonipekun.
Sauran sun waɗanda ta ce ’yan ƙasashen waje ne sun haɗa da Johnson Otieno da Israel Mbaluka da Joseph Kabera da kuma Serah Michiro.
“Muna son sanar da al’umma cewa muna neman waɗannan mutane ruwa a-jallo saboda zargin damfarar mutane a wani tsarin zuba kuɗi na intanet wanda ake kira CBEX,” in ji EFCC.
Hakan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa jami’an EFCC ɗin damar kame da kuma tsare mutanen da aka samu da hannu wajen yaɗa tsarin na CBEX.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Damfara
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
Dakarun Sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano.
Wannan zuwa ne bayan mazauna Yankamaye Cikin Gari suka sanar da jami’an tsaro cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyensu a daren ranar Juma’a.
’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar AfrikaWannan na cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce sojin ƙasa tare da haɗin guiwar sojin sama da ’yan sanda sun garzaya wajen, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, sannan suka ceto mutanen da abin ya shafa.
Sai dai Zubairu, ya ce ’yan bindigar sun riga sun kashe wata mata mai shekaru 60 kafin sojoji su isa yankin.
Ya ƙara da cewa bayan harin farko da suka kai, sojojin sun bi sahun ’yan bindigar zuwa yankin Rimaye, inda suka yi musu luguden wuta, wanda hakan ya tilasta musu barin mutanen da suka sace.
Sai dai har yanzu ba a gano inda mutane huɗu da suka sace suke ba.
Bayanai sun nuna cewar bayan ’yan bindigar sun tsere, sun nufi Ƙaramar Hukumar Kankia da ke Jihar Katsina, kuma jami’an tsaro na ci gaba da bibiyarsu.
Kwamandan rundunar, ya yaba da jarumtar sojojin, ya roƙi jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihin bayanai a kan lokaci domin kawar da ’yan bindiga a jihar.