Yadda Sakamakon Jawo Jarin Waje A Rubu’in Farko Na Bana Ya Ba Da Sha’awa A Kasar Sin
Published: 26th, April 2025 GMT
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka.
Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25.
Rahmatollah Akrami, ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI, da kuma Hazem Majid Naji Al-Khalidi mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara sun jaddada muhimmancin kammala layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma kasuwar ba kudaden fito tsakanin kasashen biyu. Da kuma fatan zasu yi kokarin amfanar juna gwagwadon abinda zasu iya.