Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-02@03:38:03 GMT

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho

Published: 30th, April 2025 GMT

Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta.

A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.

Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai.

Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin biyan fansho.

Ya kara da cewa, wannan yunkuri ya yi daidai da kudirin jihar gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki, tare da bai wa ‘yan fansho dama su gyara duk wani bayanin da bai cika ba a takardunsu.

Shi ma da ya ke jawabi, Akanta Janar na Jihar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya jaddada cewa aikin tantancewar zai bai wa ‘yan fansho damar sabunta bayanansu da suka bace ko suka canza a takardunsu.

Saboda haka, ya bukaci dukkan ‘yan fansho daga ma’aikatun gwamnati, sassan hukumomi, kananan hukumomi da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi da su halarci tantancewar a ranar da aka tsara kamar yadda yake cikin jadawalin aikin.

A jawabinsa, Shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON ta Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman, ya tabbatar da cikakken goyon baya daga shugabannin kananan hukumomi 27 domin cimma burin aikin.

Shugaban na ALGON wanda shugaban karamar hukumar Malam Madori,  Alhaji Salisu Sani ya wakilta,  ya bukaci ‘yan fanshon da su ba da cikakken haɗin kai don samun nasarar shirin.

Shi ma Shugaban hukumar, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya bukaci ‘yan fansho daga sassa daban-daban da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya, tare da jaddada cewa su ziyarci sakatariyar kananan hukumominsu domin a tantance su.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, Alhaji Umar Sani Babura, ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta bada cikakken goyon baya domin nasarar wannan shiri.

Dukkan ‘yan fansho daga Ma’aikatun Gwamnati, Kananan Hukumomi, da Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi da ke cikin tsarin  fanshon, ya zama wajibi su halarci wannan tantancewa a ranakun da aka tsara a jadawalin aikin.

 

Usman Muhammad Zaria

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa yan fansho da Jihar Jigawa tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

An zabi Doro ne bayan naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Doro a matsayin ƙwararren masani da ke da fiye da shekaru 20 na ƙwarewa a fannoni da dama ciki har da aikin asibiti, gudanar da harkokin magunguna, da jagoranci a Nijeriya da Birtaniya.

An haifi Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a Kwall, ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau. Yana da digiri a fannin magunguna da shari’a, MBA a dabarun kasuwanci na IT, da kuma digiri na biyu a fannin aikin lafiya mai zurfi (Advanced Clinical Practice).

Da amincewar da aka yi masa a yau, ana sa ran Bernard Doro zai rantse a matsayin ɗan majalisar zartarwa (FEC) a zaman majalisar ministoci na gaba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15 October 30, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
  • Jihar Jigawa Ce Ta Fara Biyan Kudaden Kujerun Aikin Hajjin 2026- NAHCON
  • Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya