Riza’i: Babu Hannun Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
Published: 30th, April 2025 GMT
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki.
Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.
A ranar Asabar da ta gabata ne dai wasu abubuwa su ka fashe a tashar ruwa ta Shahid Raja’i dake Bandar Abbas a kudancin Iran, wanda ya haddasa asarar rayuka da kuma jikkatar daruruwan mutane.
An bude kwamitin bincike domin gano hakikanin abinda ya faru a tashar da kuma haddas fashewar abubuwan masu karfi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ta Shahid Raja i
এছাড়াও পড়ুন:
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri
Ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka da safiyar ranar Laraba a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ya haddasa ambaliya.
Ruwan wanda ya fara sauka tun da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ya cika tituna da gidaje musamman a unguwannin Dala, Bulunkutu, titin Damboa, filin Polo, da Federal Low Cost.
Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasuAmbaliyar ta haifar da cikas a rayuwar jama’a, inda ruwa ya lalata dukiyoyi mutane masu tarin yawa.
Mutane da dama dun fice daga gidajensu domin neman mafaka, musamman waɗanda gidajensu ruwa ya mamaye.
Hakazalika, wasu tituna sun shafe sakamakon mamakon ruwan, lamarin da ya hana mutane fita ko komawa gidajensu da kuma yin ayyukansu na yau da kullum.
Wasu daga cikin mazauna garin sun ce ambaliyar ta tsananta ne saboda magudanan ruwa sun cika da shara irin su robobi, datti da tarkacen kayan gini.
Hakan ya hana ruwa tafiya yadda ya kamata.
Wani da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce mafi yawan magudanan ruwan Maiduguri ba sa aiki yadda ya kamata saboda sun toshe da shara.
Ya ƙara da cewa rashin kula da tsaftar muhalli ne ya haddasa irin wannan matsala.
A halin yanzu, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara sanya ido, ta tsaurara dokokin muhalli, da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsaftar gari.
Har ila yau, akwai buƙatar a gyara magudanan ruwa domin gujewa irin wannan ambaliya a nan gaba.
Masana sun gargaɗi jama’a cewa ana sa ran samum mamakon ruwan sama a makonni masu zuwa.
Amma an buƙaci jama’a su ɗauki matakan kariya da kuma haɗa kai da hukumomi domin shawo kan lamarin.