Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria:

Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a yi kina kara girma kina komawa jeji, ai a lokacin da ki ka dade da namiji a lokacin ne ya kamata ki kara wanka akan wanda ki ke dan maida hankalinsa kacokam a kanki, tsabta naki kwalliya naki jan hankali naki.

Na daya zai fara hangen na waje, na biyu zai dinga nisanta dake, ko da ko ba mai ra’ayin kwalliya sosai bane, ba zai so ace kin daina kwata-kwata ba, ajinki zai ragu a gareshi, hangen sabon aure zai daka tsalle ya shige zuciyar shi da sauransu. Kar mace ta kuskura tayi aure ya janye daga mijinta ta fannin kwalliya saboda shi ne ake kira da jagoran da namiji shi ke janye hankalin namiji sosai, dan ba namijin da baya son kwalliya ke kanki in kina kwalliya kin fi jin dadin kanki ko a cikin mata ‘yan uwanki bare a gaban miji, mace mai kwalliya ita ce ta nunawa a idon duniya, ta gaban mota, cikekkiyar mai iko da kasaita, gangariya tauraruwa a cikin mata, duk wacce take da wannan niyyar wai dan kin auri namiji me ya saura? to, wallahi akwai gwarama ki gyara dan gwagwarmayar gidan auren ya fi na waje, ai nanne ma za ki zage ki kara burge shi ya ji ya matsu kullum ya zo ya ga kwalliyar ki, mai sanyaya masa zuciya mai dauke da linkin sonki da kaunarki, mata a daure a dinga kwalliya.

 

Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To magana ta gaskiya rashin ilimin zaman aure ne ke jawo haka, domin yin tsafta ko kwalliya ga matar aure yana matukar kara kauna da soyayya a tsakaninta da mijin ta, kuma zai taimaka wajen ta mallake shi gabadaya ya daina hangen wata mace sai ita kadai. To farko dai hakan yana jawo ake samun sabani tsakanin macen da mijin ta a lokuta da dama wanda hakan ka’iya kawo tabarbarewar dangantaka a zamansu na aure, kuma hakan yana iya zama silar mijin nata ya karo mata abokiyar zama ko kishiya koda kuwa ba shi da niyyar kara aure domin haka ne kadai zai zama mafita a gare shi. To shawara a nan ita ce ya kamata dai mata su sani tsafta daya ce daga cikin dabaru na mallake miji ba wai sai an hada da guru ko laya ba, kuma tsafta tana kara dankon soyayya da kauna a tsakanin ma’aurata, kuma uwa uba tsafta wani yanki ne na Imani wanda take taimakawa wajen samun cikakken addini.

 

Sunana Aisha T. Bello Jihar Kaduna:

Gaskiya ina jin haushin irin wanan matan gaskiya, na taba yi wa wata magana kan haka sai ta ce mani ai ni kwalliya ta yara ce wai ta barwa yara kuma ita da kanta ta fada mun mijinta na son kwalliya. Matsalar shi ne kawai zai kara aure kuma gun karan auren sai ki ga mai kwalliya. Shawara ta a nan ga masu irin wanan hali shi ne; kwalliya ba a tsufa da kwalliya yana bada girma sosai za ki ga ana kai ki inda baki kai ba kuma yana bada Personality.

 

Sunana Sadi Dauda Baturiya Jihar Jigawa:

Hakika wannan al’ada tana faruwa da ma’auratan wannan zamani na mu, kuma yin hakan yana da alaka da kiwa wato (ganda). Babu shakka yawaitar mutuwar aure a wannan zamanin yana da kazanta da sauran matsaloli makamantansu. Gaskiyar magana shawara ta ga matan wannan zamanin musamman sabbin aure su cire irin wannan tunanin na kazanta bayan tsafta domin kuwa rashin yin tsafta yana daga cikin abin da yake rage karfin soyayya tsakanin ma’aura

Allah ya kawo mana karshen matsalolin mutuwar aure a cikin al’ummar mu amin.

 

Sunana Fatima Nura Kila Jihar Jigawa:

Wasu laifin mazan ne wasu kuma na matan, wasu mazan daga an yi aure an dau wasu watanni ba zai iya siyan kayan kwalliyar da za ta yi ya ganta tsaf ba, wani kuma ko kudin sabulu bai badawa a nan kuma hankalin mace zai karkata a nan ta ga ita ba ta kwalliyar take ba, domin kudin abun kwalliyar da za ta siya ma babu. Yana haifar da matsaloli masu tarin yawa, a wannnan lokacin wani a nan yake ganin wata matar a waje ta birge shi tunda matar sa ba ta yin kwalliyar, sannnan ya kan rage shakuwa a tsakanin ma’aurata. Ya kamata mu mata mu dage koda mazajen mu basu yi mana ba mu, mu yi da kudin mu domin hakan ba karamar kima yake karawa ba a idon miji, domin kwalliya wata aba ce da ta ke karawa mata kyau, wadanda suke yi kuma su daina su rika yin kwalliya hakan zai kara masu shakuwa a tsakaninsu.

 

Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:

Wato idan muka kalli yadda ake rayuwa kafin aure da kuma bayan aure za mu fahimci cewa su matan suna mayar da kansu haka ne a dalilin ganin cewa an riga da an zama abu daya, ko da kwalliya ko babu hakan ba zai sa mijin ya kosa ba, tun da su mazajen ne kusan basa yabawa matan idan suka yi kwalliya, ko ado, sabanin kafin aure kusan kullum a cikin samun yabon namiji ta ke. Batun matsaloli kuwa akwai su; ta bangaren mace hakan yana mayar da ita koma-baya ta fuskar matsayinta a wurin miji, da kuma jawo mata kaskanci, da rashin wadata ta da kayan kwalliya, tunda miji ya ga ta daina yi. Ta bangaren miji kuma rashin yin kwalliyan yana sakawa ya ringa hange, ko gane-ganen wasu matan a waje, da suke cancara kwalliya abinsu. Ko da ba shi da niyyar kara aure hakan zai iya jan hankalinsa. Ina jan hankalin mata tare da basu shawara da su cigaba da yin ado da kwalliya ga mazajensu, ba sai idan za a fita ba, misali: kai tsaye kin san lokacin da mijinki yake dawowa gida ko da kuwa dare ne, ki saka kayanki masu kyau, ki chaba kwalliya, ki fesa turarenki mai kamshi, mijin na shigowa gida ya ganki a haka wallahi sai ya ji dadi a ransa, kuma za a cimma abubuwa da yawa daga hakan. Ina fatan a samu wata bayan karanta wannan bayani nawa ta gwada wannan siddabarun za ta sha mamaki.

 

Sunana Naja’atu Baffa Jihar Kaduna:

Wataran abin da yake janyo hakan ba komai bane face yawan aikace-aikace na gida na iya hana mace yin kwalliya da sauransu, kuma jigon wannan aikace-aikacen yara ne, saboda an mikawa ita wannan matar dafa musu abincin da za su ci, idan kananun yara ne yi musu wanka da shirya su, gyara ko’ina na gidan da dai sauransu, idan ta yi wankan ba lallai ta tsaya yin ado ba. Wataran kuma al’ada ce ke canja ra’ayin mace ko bada son ranta ba kamar hana mace kwalliyya da shiga mai kyau yayin da ta kai wadansu ‘yan shekaru. Matsalolin da hakan ya ke haifarwa su ne; hakan zai bi daga ‘ya’yayensu har zuwa ga jikokinsu a matsayin abin da ya dace, rashin girmamawa da kaskanci a wajen mazajensu da ma wadanda su ke mu’amala tare da su. Shawarar da zan bawa mata masu irin wannan tunanin ita ce; su zauna da mijinsu su tattauna wajen shawo kan matsalar idan aiki ne yayi mata yawa da sauransu, sannan akwai shirye-shiryen da ake yi na yanar gizo-gizo da dama na wayar da kan mata su ma su rinka sauraren shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yin kwalliya Jihar Jigawa da kwalliya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.

A wani gagarumin mataki na karfafa yaki da rashin tsaro, gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Gusau, da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma kaddamar da sabbin dabarun yaki da ayyukan ta’addanci da masu aikata laifuka.

 

Taron wanda aka gudanar a Sakatariyar JB Yakubu wanda ofishin sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya shirya, ya hada manyan hafsoshin tsaro, manyan jami’an gwamnati, da wakilan hukumomin tarayya domin duba halin tsaro da jihar ke ciki.

 

A cewar wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga SSG, Suleman Ahmad Tudu, ya yi, an kira taron ne domin zurfafa hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki domin kara inganta ayyukan da ake gudanarwa a fadin jihar.

 

Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Nakwada, wanda ya jagoranci taron, daga bisani mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya jadadda kudirin gwamnatin jihar na siyasa na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

 

A cewar sanarwar, yayin taron, mahalarta taron sun tsunduma cikin wani muhimmin nazari kan kalubalen tsaro da ake fama da su tare da daukar sabbin shawarwari guda goma da gwamnatin jihar ta bullo da su.

 

Ta ce an tsara matakan ne don karfafa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan da kuma kara kaimi wajen yaki da ‘yan fashi.

 

Da yake jawabi, Malam Nakwada ya yabawa jajircewa da sadaukarwar jami’an tsaro da ke aiki a fadin jihar Zamfara.

 

“Gwamnatin Jiha ta yaba da irin sadaukarwar da ku da manyan jami’an ku suka yi wajen kare lafiyar al’ummarmu, a madadin Mai Girma Gwamna Dauda Lawal, ina mika godiyarmu ga sadaukarwar da kuke yi ba tare da gajiyawa ba.” Inji shi.

 

SSG ya jaddada bukatar daidaitawa da dabarun hadin gwiwa wajen tinkarar barazanar da ke tasowa, inda ya bayyana cewa, hazaka, kirkire-kirkire, da hadin kai na ci gaba da zama muhimmi wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

 

Ya kara da cewa, “domin tunkarar kalubalen tsaro masu sarkakiya yadda ya kamata, dole ne mu ci gaba da daidaitawa, yin sabbin abubuwa, da kuma yin aiki tare ba tare da wata matsala ba fiye da kowane lokaci.

 

Malam Nakwada ya kuma bayyana bakin cikinsa kan yawaitar hare-hare a sassan jihar, inda ya mika sakon ta’aziyyar gwamnati ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa.

 

“A madadin gwamnatin jihar Zamfara, ina jajantawa duk wadanda hare-haren baya-bayan nan ya rutsa da su, ina kuma tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an samar da cikakken zaman lafiya a tsakanin kowace al’umma,” inji shi.

 

Ya kuma kara nanata kudirin Gwamna Dauda Lawal na samar wa jami’an tsaro kayan aiki, da tallafin da ake bukata domin fatattakar masu aikata miyagun laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara.

 

A nasa jawabin rufe taron mataimakin gwamna Mani Malam Mummuni ya yaba da gudunmawar da masu ruwa da tsaki suka bayar tare da yin kira da a kara himma da hadin kai.

 

“Muna matukar godiya da kokarin da aka yi ya zuwa yanzu, amma dole ne mu kara himma. Bari mu tabbatar da kowane inci na jihar mu da muke so mu maido da fata ga jama’armu,” in ji shi.

 

Taron dai wani mataki ne mai jajircewa da gwamnatin Dauda Lawal ta dauka na magance matsalolin tsaro a gaba, yayin da gwamnatin ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.

 

REL/AMINU DALHATU

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”
  • NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe
  • Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — Tinubu
  • Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da  Falasdinu a matsayin Mamba
  • Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu
  • Manoma A Kaduna Sun Yabawa Irin Masara Na TELA Saboda Juriyarshi Ga Kwari
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Maida Gidan Marayu Zuwa Cibiyar Gyaran Mata Masu Shaye
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco