Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP.

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15

A ranar Juma’a, ‘yan majalisar Ribas guda 16, ciki har da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, da suka sauya sheƙa zuwa APC.

Amaewhule, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rarrabuwar kai da aka samu a PDP.

Hakazalika, kakakin ya ce yana son ya yi aiki tare da Shugaba Bola Tinubu, bayan ya gano yana da kyakkyawan tsari na ciyar da ƙasar nan gaba.

Da yake magana da manema labarai bayan duba wasu ayyuka a Abuja, Wike, ya ce ’yan majalisun ba su tuntuɓe shi game da batun sauya sheƙarsu ba, amma ya ce suna da  ’yancin zaɓen abin da suke so.

Ya ƙara da cewa ba duka ’yan majalisar ne suka fice daga PDP ba.

Ya ce, “Ni har yanzu ina PDP. Ba dukkaninsu ne suka fice daga jam’iyyar PDP ba. Ina ganin 16 ko 17 ne suka fice daga cikin 27. Har yanzu muna da kusan mutum 10, kuma za mu ci gaba da aiki tare da su.”

Wike, ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, amma ya ce kowa na da ’yancin zaɓen abin da yake so.

Ya ɗora alhakin ficewarsu kan rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi, inda ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bai wa mutane damar barin jam’iyyar idan ta rabu gida biyu.

Ya ce tun da farko ya bai wa shugabancin PDP shawara su gyara jam’iyyar, tare da gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki ba jam’iyyar za ta ci gaba da yin asara.

Wike, ya ƙara da cewa suna ci gaba da ƙoƙari domin sauran mambobin PDP su haɗa kai don yaƙar jam’iyyun adawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
  • Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
  • Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC
  • Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15
  •  Jiragen Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon
  • NAJERIYA A YAU: Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa