2025-04-30@20:10:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 822

«a fara biyansu»:

    Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar.   Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba su da rajista, musamman magungunan inganta jima’i, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan abubuwa na da matukar barazana ga kiwon lafiyar jama’a.   Ya yi gargadin cewa, yin amfani da wadannan magungunan ba tare da kulawar likitoci ba zai iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, ciki har da haɗarin cututtukan zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    ’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF). Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne...
    Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu. Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa, da akwai batutuwa da dama da su ka raba kawunan manyan malaman addinin na Roman Katolika da  su ka batun auren jinsi, da rawar da mata za su taka a karkashin inuwar cocin. Sai dai kuma wani mai sharhi akan abubuwan da su ka shafi cocin, Reese ya bayyana cewa, masu zaben za su mayar da hankali ne akan wanda zai kare ayyukan da mamacin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa. Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa. Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana. A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar. Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar. Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu. Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin...
    Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta. A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025. Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai. Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...
    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama. A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar...
    Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno. Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu. Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa. “Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke...
    Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar. Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.” Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar. Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar. Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar  nauyi ne da ya rataya a wuyan  hukumar. “Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.” “Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.   “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.   “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.   “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
    A cewarsa, kasar Sin ba ta neman kakaba akidunta kan sauran kasashe. Abun da take nema shi ne, aminci da tuntubar juna. Kuma a ganinsa, wannan shi ne ya kamata ya kasance ruhin hadin gwiwa.   Bugu da kari, ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar game da tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya da ci gaban duniya da hadin gwiwa ta fuskar al’adu, sun dace da muradun MDD na wanzar da zaman lafiya da gudanar da ayyukan agaji da tabbatar da tsaro a duniya, yana mai cewa, akwai babbar dama ta kara hadin gwiwa a cikinsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    An fara gudanar da zaman taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin  Iran da kasashen nahiyar Afirka karo na uku A safiyar yau Lahadi ne aka bude zaman taron karo na uku kan harkokin tattalin arziki tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Afirka a birnin Tehran, tare da halartar shugaban kasar Iran da mataimakinsa na farko da wasu tawagar jami’ai da ‘yan kasuwa daga nahiyar Afirka. Kasar Iran tana gudanar da wannan biki ne tare da jami’an kungiyar Tarayyar Afirka, da manyan jami’ai, ministocin tattalin arziki da cinikayya, da shugabannin kungiyoyin kasuwanci, ‘yan kasuwa, masu fafutukar tattalin arziki, shugabannin bankuna, kamfanonin inshora, da na’urorin samar da kayayyaki, da daraktocin manyan kamfanoni da na kasa da kasa daga kasashen Afirka. Taron...
    A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba! Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta. Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.” Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”
    Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki.   Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da shakatawa da wuraren raya al’adu da filayen jiragen sama da otel-otel da tashoshin tafiye-tafiye. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane. Haka kuma, rundunar ta gano bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da kuma bindigogi ƙirar AK-49 guda uku da alburusai guda arba’in da biyar a hannun waɗanda aka cafke. Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa Ƙungiyoyin da suka yi shuhura a Firimiyar Ingila Kakakin rundunar ’yan sandan, ASP James Lashen ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Jalingo. Ya bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Shehu Ibrahim da Abdullahi Haruna da kuma Yusuf Bello. Sauran kuma sun haɗa da Sulaiman Muhammed da Tijjani Bello da Muhammed Umar. Kazalika, akwai kuma Adamu Ibrahim...
    A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’.   Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu...
    A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saka, saboda tashin gwauron zabon da kayan a kasar. Galibin wadannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa kasashen a duniya. Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kudin shiga kimanin dala biliyan 2.7. Yawan bukatar kayan a kasuwannin duniya ya kawo hauhawar farashin kayan abinci na yau da kullum da amfanin gona na kasuwanci. An kuma yi hasashen cewa farashin zai ci gaba...
    Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria: Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a yi kina kara girma kina komawa jeji, ai a lokacin da ki ka dade da namiji a lokacin ne ya kamata ki kara wanka akan wanda ki ke dan maida hankalinsa kacokam a kanki, tsabta naki kwalliya naki jan hankali naki. Na daya zai fara hangen na waje, na biyu zai dinga nisanta dake, ko da ko ba mai ra’ayin kwalliya sosai bane, ba zai...
    Mayakan Boko Haram sun halaka mutum goma sha biyu da jikkata karin biyu bayan wani hari da suka kai kan kauyen Bokko Ghide a Karamar Hukumar Goza ta Jihar Borno. Wakilinmu ya ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai ’yan sa-kai biyu da wasu mutum 10 da suka fita debo itacen girki. Sulhu da ’yan bindigar Katsina: Gaba aka ci ko baya? Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma Francis Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayakan sun yi wa ’yan sa-kan kwanton bauna a kan hanyar Kirawa da ke gudunmar Pulka. “Sun fita neman itace ne a jeji a ranar Asabar, yayin da yaran [mayakan Boko Haram] suka yi musu kwanton...
    “Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau. “Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in ji Sarkin. Ya yi addu’a Allah ya jiƙan mamatan ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya. Sarkin ya yaba wa gwamnati da sojoji bisa ƙoƙarinsu amma ya buƙaci a ƙara amfani da sabbin fasahohin zamani da kayan yaki masu ƙarfi domin yaƙar ‘yan ta’addan. Ya yi gargaɗin cewa waɗannan hare-hare na iya tsoratar da manoma wajen komawa gonakinsu yayin da lokacin shuka ke gabatowa....
    Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro. Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka. Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira idan aka ga wani abu da ba a gamsu da shi ba; 08034805544, 07032490813 da kuma 09053872244 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin. Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida. Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci,...
      Kazalika, ya ce, kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa tare da IMF wato asusun ba da lamuni na duniya, da kuma ba shi goyon baya wajen taka muhimmiyar rawa a kan kiyaye tafiyar da tattalin arziki da hada-hadar kudin duniya cikin kwanciyar hankali.   Bugu da kari, Pan ya jaddada bukatar gaggauta zurfafa sauye-sauyen asusun na IMF a bangaren kaso, yana mai bayyana gyare-gyaren da suka kamata a yi a bangaren rabon kason a matsayin wani muhimmin bangare na sake fasalin tsarin shugabancin IMF. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    A jiya Juma’a, an gudanar da taron dandalin tattaunawar kirkire-kirkire na kafofin watsa labaru na duniya karo na 4, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice da gwamnatin lardin Shandong dake gabashin kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa a birnin Qufu na lardin.   Taron dandalin mai taken “Musanya da yin koyi da juna da ma amfani da kimiyya da fasaha na kasancewa karfin wayewar kai a yayin da ake neman sauye-sauye da ci gaba”, ya samu halartar wakilai kusan 300 daga kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin watsa labarai na kasashe da yankuna 95, da cibiyoyin masana na kasar Sin da na kasashen waje, da ma kamfanonin ketare da dai sauransu ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan kasuwar kayan abinci sun bayyana yadda suke tafka asara  bayan sun saye wasu kaya sun ajiye suna jiran samun tuna mai tsoka idan kayan sun yi tashin gwauron zabo. A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saƙa, saboda tashin gwauron zabon da kayan a ƙasar. Galibin waɗannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa ƙasashen a duniya. Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kuɗin shiga kimanin dala biliyan 2.7....
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa game da sake haduwa da ƙara ƙarfin mayakan Boko Haram a yankunan Tumbus na Tafkin Chadi da kuma tsaunukan Mandara a cikin dajin Sambisa. Yayin da yake jawabi ga Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, da manyan hafsoshin soji a Maiduguri, Gwamna Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojojin Najeriya wajen yaƙi da ta’addancin Boko Haram a Borno da ma yankin Arewa maso Gabas, amma ya nuna wani abin damuwa da ya faru kwanan nan a ayyukansu. Ya bayyana cewa bayan an yi ayyukan soja an gama, sai sojojin su janye, sai kuma ’yan Boko Haram da ISWAP su sake dawowa su karɓe waɗannan yankunan da aka ƙwato a baya. Babban abin da...
    Kasar Rasha ta fara tura iskar gasa zuwa kasar Iran ta kasar Azarbaijan, wanda daga karshe zai shiga kasuwan ga kasar ta rasah. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar ta na fadar haka a yau Asabar. Labarin ya kara da cewa tun taron kwamin hadin guiwa na kasuwanci da tattalin arziki na kasashen biyu ya gudanar da taronsa na hadin guiwa karo na 18 a birnin Mosco, Rasha ta bada sanarwan fara tura iskar gas zuwa kasar ta Iran ta kasar Azirbajan, wanda kuma hakan zai zama kasuwa ga kasar Rasha amma a kasar Iran.. Kasashen biyu dai sun dade suna kokarin karfafa dangantaka a tsakaninsu, musamman bayan da kasashen yamma suka dora masu takunkuman...
    Wannan dai, wani bangare ne na shirin kara habaka hada-hadar kawance tsakanin kasar da China.   Kazalika, hakan na daga cikin yunkurin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, na jawo masu zuba jari da yawansa ya kai kimanin dala biliyan daya a fannin habaka samar da Sikari a kasar.   Bisa tsarin wannan yarjejeniya, kamfanin zai kafa masana’antar Sikari da kuma gonar Rake da za su fara samar da tan 100,000 na Sikari a duk shekara.   Kazalika, Hukumar NSDC ita kuma, za ta taimaka wajen samar da duk takardu da kuma sahalewar gwamnati da ake bukata, domin fara aikin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    A wannan makon Aminiya ta samu tattaunawa da shahararren jarumi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannyood, Malam Inuwa Ilyasu, wanda ya shafe sama da shekara 40 yana harkar wasan kwaikwayo. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Gabatar da kanka? To da farko dai sunana Inuwa Ilyasu. Yaushe ka fara harkar fim? Gaskiya dai kusan da ni aka fara yin fim kuma lokacin da muka fara yi, mun fara da yin tunanin ya za mu yi saboda kafin nan ai akwai wasan daɓe da muka fara yi. A wancan lokaci muna faɗakarwa ta wasan kwaikwayo kusan tun wajejen 1970. Daga nan muka fara tunanin ta yaya za mu yi ƙoƙarin mu ma mu fara yin irin namu. Yawancin fina-finanka kana fitowa...
    Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa.   “Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi.   ”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya.   Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai.   “Kafin Buhari ya zama shugaban...
    A watan Janairu kawai, marigayi shugaban ‘yan fashin daji, Isuhu Yellow, ya sanya harajin naira miliyan 172.7 a kauyuka 25, ciki har da bukatar amfanin gona.   A misali, an kakaba wa kauyen Gijinzama harajin naira miliyan 8.5, Dakolo naira miliyan 5 da buhunan wake 20, da Kibari, Kunchin Kalgo naira miliyan 20, Sungawa naira miliyan 15, da Yalwa naira miliyan 2.7, da dai sauransu.   Ba da jimawa ba, wani shugaban ‘yan fashin dajin nan, Dogo Gide, ya bukaci a biya naira miliyan 100 daga wasu al’ummomi 23 da ke karamar hukumar Tsafe, lamarin da ya sa jama’a suka kauracewa gidajensu.   Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Kunchin-Kalgo da aka nemi naira miliyan 20 daga wajensu,...
    An sako limamin cocin Katolika, Rabaran Fada Ibrahim Amos wanda ’yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da rana a Kurmin Risga da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Fada Amos, wanda ke aiki a Cocin St. Gerald Ƙuasi Parish ya dawo gida lafiya lau ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare, kwana ɗaya bayan sace shi. An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe Bayani kan sakin nasa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Cocin Diocese na Kafanchan, Rabaran Fada, Dakta Jacob Shanet ya fitar, inda ya gode wa Allah tare da nuna godiya ga...
    Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci ya jagoranci sacewa da kashe ɗansa mai shekara shida domin yin tsafin kuɗi. Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere, a yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa. Tuni ’yan sanda suka cafke mutane takwas bisa zargin wannan aika-aika a unguwar Bura-Bunga da ke ƙaramar hukumar. Kakakin ’yan sanda a Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya sanar cewa waɗanda suka shiga hannu sun amsa cewa sun kashe yaron ne bisa umarnin bokaye da suka nemi sassan jikin ɗan Adam don yin tsafin kuɗi. An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi...
    “Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba.   “Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.”   Kazalika, wani ma’aikacin gidan man, ya tabbatar da cewa suna ‘yan wasu gyare-gyare ne amma za su sake budewa. Ya kuma ce, gidan man zai fara sayar da man fetur ga jama’a a ranar Talata kan kudi naira 910 a kowace lita.   Rahotonni sun tabbatar da cewa sauran abokan huldar matatar man Dangote, kamar su AP, Ardoba, da Optima, sun yi ta sayar wa...
    Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe. Shirin da shugaban kasar Donal Trump ya bayyana shi ne karshe dai, ya bukaci gwamnatin shugaba Volodimir Zelesky ta amince da yankin Cremea da kuma sauran yankunan hudu wadanda Rasha ta mamaye da karfi shekaru uku da suka gabata su zama mallakin kasar Rasha har’ abada. Sannan ta amince a daukewa kasar Rasha takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata tun bayan fara yakin. Sannan daga karshe ta amince ba zata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba. Shawara bata yi maganar wani abu banada wadannan hudu ba, duk da cewa Ukraine tana da wasu bukatu a yarjeniyar tsagaita...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa duk waɗanda ke son barin jam’iyyar PDP su tafi yanzu, domin a bai wa masu kishin jam’iyyar damar sake gina ta. Saraki ya fitar da wannan bayanin ne a martani ga yawan sauye-sauyen jam’iyya da ake yi a PDP, ciki har da ficewar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma jam’iyyar APC. Saraki ya bayyana cewa ya samu kiran waya daga mambobin jam’iyyar da dama da kuma matasa masu goyon bayan dimokuraɗiyya, suna nuna damuwarsu game da barin jam’iyyar PDP, musamman ma a sashin jihar Delta. A cikin sanarwar, Saraki ya jaddada cewa yana da muhimmanci jam’iyyar ta kasance da mambobi masu cikakken kishin gaskiya fiye da yawan mambobin da...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta. ///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka...
    Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC. Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC. Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani babban tagomashi ga jam’iyyar APC musamman a Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba.   A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na...
    A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar  mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani. Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan. Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a...
    Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a kan wasu kasashe na kwanaki 90. Kuma kashegari sai aka ji ya yi barazanar cewa, in dai ba a kai ga cimma daidaito a shawarwari ba, to, Amurka za ta maido da harajin. Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi gyara ta ba-zata a kan dokokinta na haraji, inda ta cire harajin ramuwar gayya a kan kayayyakin lataroni da suka hada da wayar salula...
    Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila. Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza. Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda...
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa NBC sun shirya taron yini biyu ga masu fafutukar siyasa da masu sharhi kan harkokin yada labarai.       Taron na da nufin tsaftace harkar siyasa da inganta fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar.   An zabo mahalarta taron ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban da gidajen rediyo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.   A nasa jawabin, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa, a karshen taron, mahalarta taron za su fahimci ladubban da suka shafi harkokin siyasa.   Ya yi Allah wadai da karuwar kararrakin batanci da sunan...
    “Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi.   Ya kara da cewa, ya kamata shugaban kasa ya yi tunani a kan nagartattun abubuwan da yake son bari bayanshi da kuma yadda tarihi zai tuna da shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Amurka ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Yaman, a daidai lokacin da kasar Larabawar ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza. Gwamnonin Sana’a da Sa’ada su ne wuraren da Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare a safiyar Alhamis. A birnin San’a, jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare 6 a yankin Barash da ke gabashin Dutsen Nuqum. Har ila yau Amurka ta kai hari a unguwar Al-Jarf da ke gabashin gundumar Sha’ub ta lardin Sana’a. A arewa maso yammacin kasar, an kai wasu hare-hare 6 ta jiragen yakin Amurka a yankin Sahlin da ke gundumar Al Salem a gundumar Sa’ada. Har ila yau, Amurka ta kai wasu jerin hare-hare ta sama kan lardin Al-Hudaidah, inda...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya.   Yayin ganawarsa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana da muradin yin hadin gwiwa tare da kasar Azabaijan wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa dokokin da aka amince da su a duniya, da yin tsayuwar daka wajen kare halastattun hakkoki da muradu, da kare daidaito da adalci...
    Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7. Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe. A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60. Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu...
    Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kudancin Amurka (Conmebol) ta gabatar da buƙata a hukumance ta ƙara yawan ƙasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64. Haɗakar ƙasashen Sifaniya da Morocco da Portugal ne za su karɓi baƙuncin gasar, bayan buɗe ta a ƙasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay. Matar da aka haifa ‘babu mahaifa’ ta haihu Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan mutuwar Fafaroma Francis Gasar Kofin Duniya ta 2026 ce ta farko da ƙasashe 48 za su halarta, to amma Conmebol na son a faɗaɗa gasar ta 2030 domin murna cika shekara 100 da fara gasar. “Hakan zai bai wa ƙasashen duniya damar kallon gasar, don haka ba wanda za a bari a...
    ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila. Mustapha Yahi, sakatare-janar na National Democratic Rally (RND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Al-Alam: inda yake cewa “Mun sake yin Allah wadai da ci gaba da ta’addancin isra’ila. Abdelaali Hassani Cherif, shugaban kungiyar Movement of Society for Peace (MSP),...
    A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.”   A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu kansu biyo bayan maida martani da China tayi na ramuwar gayya. Domin kuwa sai da gwamnatin America ta kashe kimanin dala biliyan 30 wajen tallafawa manoman kasar kan asarar da suka tafka, biyo bayan harajin da China ta kakabawa wasu daga cikin amfanin gonar America da ake shigar da su China.   Sabo da haka a nan za mu iya bugun gaba mu ce “Kwalliya...
    Haka kuma, ya soki jam’iyyar Galadima wato NNPP, yana mai cewa tana cike da rikice-rikice, saɓanin APC a ƙarƙashin shugabancin Ganduje wadda ke tafiya cikin daidaito. Okpala ya kammala da cewa Ganduje ya mayar da hankali wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba, kuma ba zai tsaya sauraren “maganganun marasa tasiri” kamar na Galadima ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin. Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar. Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa an dakatar da basaraken ne har sai abin da hali ya yi, saboda yawan samun kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a masarautarsa a baya-bayan nan. Ya ce tuni jami’an tsaro suka tsare sakataren basaraken, Cif Peter Omiogbemhi, sakamakon wani sabon hari a da ya yi ajalin wani bafade, Cif John Ikhamate. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 An...
    A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa. “Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin. Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun fara komawa harkokinsu na yau da kullum. “Muna gode wa sojojin bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa,” inji shi. Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a Buni Yadi ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a game da buƙatar ƙarin tsaro a yankin. Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta tura ƙarin sojoji don hana faruwar irin...
    Ya kara da cewa, kowace kasa za ta yi asara idan an gudanar da cinikin duniya bisa ka’idar fin karfi. Sin na fatan kara hadin gwiwa da sauran kasashe don tinkarar kalubale tare da yaki da babakere, ta yadda za su kare muradunsu bisa adalci da daidaito.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar.   Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan, rahe kasafin kudi na ma’aikatar harkokin wajen kasar da kasha 50%, saboda haka kuma ya rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasar da kananan ofisoshin jakadancin kasar fiye da 30 a yankuna daban daban a duniya amma mafi yawansu a nahiyar Afirka. Dangane da wannan matakin da gwamnatin kasar Amurka masana daga ciki ga wajen kasar ta Amurka masu yawa...
    A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
    Nahiyar dake da yawan mutane fiye da biliyan 1.4 na da babbar kasuwa. Matakin Donald Trump ka iya samar wa kasashen nahiyar damar karfafa hadin gwiwarsu da inganta tsarin masana’antu. Ban da wannan kuma, kasashen Afirka suna iya samun mafita ta hanyar kara hadin gwiwa da kasashe masu tasowa musamman ma kasar Sin.   Cikin shekaru 16 a jere ne Sin take kan matsayin abokiyar ciniki mafi girma ga Afirka. A maimakon matakin da Amurka ke dauka wato kara dora wa kasashen Afirka haraji, Sin tana dukufa kan taka rawar gani cikin tsarin hadin gwiwar mabambantan bangarori da gaggauta hadin gwiwar kasashe masu tasowa da cin moriya tare, matakin da zai samar da yanayi mai dorewa ga bunkasarsu baki daya....
    Sai dai Bukarti wanda ya shafe shekaru da dama yana gudanar da bincike kan kungiyar ta ‘yan ta’adda, ya kara nuna fargabar cewa, a halin yanzu ‘yan tada kayar bayan na yaɗa aƙidarsu a shafukan sada zumunta ta hanyar ɗora naɗaɗɗen faifan bidiyo da kuma gabatarwa kai tsaye.   Ya ce, “Yanzu idan ka shiga TikTok, za ka ga shafukan ‘yan Boko Haram, suna gudanar da shirye-shirye kai-tsaye ko kuma su ɗora naɗaɗɗen bidiyo, inda suke yada akidar Boko Haram, suna kafa hujjar kashe-kashen da suke yi da harshen Hausa, suna amsa tambayoyi daga masu sauraro, suna amsa tsokaci da aka rubuta.   “Ko a wannan makon ma, an samu wani dan Boko Haram da ya saka wani bidiyo na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara. To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro? Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya? NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi DAGA LARABA:...
    Wata gobara ta ƙone gidajen wuccin gadi sama da 100 ma ’yan gudun hijira a  sansanin ’yan gudun hijira na hukumar ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno. Shaidu sun ce ba a samu asarar rai ba a gobarar da ta tashi da misalin karfe 10.40 na safe na ranar Alhamis da ta gabata, kuma cikin sauri ta bazu a unguwar, inda ta ƙona kayan abinci, da sauran kadarori masu ɗimbin yawa. Majiyar da ke sansanin ta bayyana cewar an tura jami’an agaji zuwa wurin domin kula da jama’a da kuma hana sace-sacen kayayyakin jama’a da suka rage, yayin da jami’an kashe gobara tare da mazauna sansanin suka yi bakin ƙoƙarinsu wajen kashe wutar. Tashin gobarar dai ba...
    Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
    Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Uba Builder, ya sake jaddada kudirinsa na kyakkyawan shugabanci wajen gudanar da harkokin karamar hukumar. Ya bada  wannan tabbaci ne yayin rabon Naira dubu hamsin hamsin ga mutane 70 da suka amfana da shirin noman alkama da karamar hukumar ta kirkiro. A cewarsa, mutane 165 ne aka saka cikin shirin, inda matasa 70 daga ciki ‘yan siyasa ne, wadanda a ke da bukatar canza rayuwarsu zuwa hanyoyin neman na kai, duba da cewa siyasa ba sana’a ba ce, illa tsarin shugabanci ne. Alhaji Muhammad Uba Builder ya ce an samar wa mahalarta shirin da filin noma, tare da gyaran filin, da samar da irin alkama da sauran abubuwan bukata, yayin da suke lura...
    Ya kuma ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko yakin kasuwanci. Kuma wannan ba wai don kare muradu da martabar kasar Sin ba ce kawai, har ma da kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci.   A cewarsa, “Idan har wata kasa ta dage kan kakaba mana yakin haraji ko kuma yakin kasuwanci, to tabbas za mu yi gaba-da-gaba da ita ba tare da tsoro ba, kuma tabbas za mu dauki kwararan matakan mayar da martani.”(Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
      A shekaru 70 da suka wuce, kasashen yamma sun yi wa taron Bandung kallon taro na kasashe matalauta, amma kuma ga irin yadda ya haifar da kyakkyawan sakamako ga mikewar kasashen. A zamanin yau, lokacin da kasar Amurka ke ta kara kakaba harajin kwastam a kan sauran kasashen duniya, muna farin cikin ganin yadda kasashe masu tasowa ke hada kansu, da rike tsaronsu da ci gabansu a hannunsu, suna kuma rungumar akidun zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa don tinkarar yadda kasashe masu karfi ke neman cin zalin kasashe masu karamin karfi da ma rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Yau da muke waiwayen taron Bandung, za mu gano cewa, ko-ba-dade-ko-ba-jima za mu ga bayan nuna...
    Kididdigar da hukumar kula da harkokin makamashi ta kasar Sin ta fitar a yau Lahadi ta yi nuni da cewa, zuwa karshen watan Maris din shekarar da muke ciki, yawan wutar lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ya kai kilowatt biliyan 3.43, adadin da ya karu da kaso 14.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.   Daga cikin wutar lantarkin da ake samarwa, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa bisa makamashin hasken rana ya kai kilowatt miliyan 950, adadin da ya karu da kaso 43.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kazalika, a sa’i daya kuma, yawan wutar lantarki da kasar ke iya samarwa bisa karfin iska ya kai...
      Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce, banza ba ta kai zomo kasuwa. Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su. ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da ƙwacen waya da fyaɗe kai har ma da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a tsakanin matasa. NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Ko yaya wannan dabara take aiki?...
    To mun san ki a matsayin marubuciyar littafan Hausa. Shin ta ya kika tsinci kanki a duniyar rubutu? Hukuncin Ubangiji, na yi karance-karance da dama a baya, tun ina karamar secondary na fara rubuta labari a paper a shekarar 2016, idan na rubuta sai na ajiye. Lokacin da muka yi hutu da aka dawo aji na Hudu (a kasar Nijar shekara 4 muke yi a karamar secondary) a karamar secondary a lokacin na fara karantawa kawayena, idan an yi break, to bayan na gama karama secondry na ci gaba da rubutun a paper, a shekara ta 2019 na fara rubutu a yanar gizo har na fara yadawa. A 2016 mene sunan littafin da kika fara rubutawa? Gaskiya ba zan iya...
    Bada shawara kan abinda ko abubuwan da su daliban suke bukatar zama da babban burin ko wane daga cikinsu,da yadda za su cimma burin abinda suke son zama a gaba. Bada taimakon lokacin da ake fuskantar matsalolin rayuwa da kuma karatu. Yin kwatance da Malamin makarnta wajen koyi da abubuwan da aka ga yana yi,irin hakan na karawa dalibai kwarin gwiwa, wajen daukar mataki kan irin abinda ya dace su yi,na taimaka masu daukar mataki daukar mataki na irin burin da suke bukatar cimmawa akan ilimi. Samar da hanyar tafiya tare da kowa Samar da hanyar da kowane dalibi zai gane tafiyar tare da shi ake yin ta,wannan ma wani abu ne da yake nuna babu wani bambanci kan yadda...
    Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9. Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya.   A cewar sanarwar, ba tare...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter.   Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter.   Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa.   Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa  ...
        Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya. Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen ci gaban kasa. Alhaji Ibrahim Haruna ya ce, masarautun ba wai kawai suna zama uba ga al’umma ba ne, kawai har ila yau suna bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Ya bayyana cewa goyon baya da gudunmawar da Alhaji Aliyu Dauda ke bayarwa ga masarautun gargajiya, musamman a Arewacin Najeriya, ne ya sa aka zabesa domin karbar wannan gagarumar...
    Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya. Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1. Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta...
    Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace mazabar Sanata, a halin da ake ciki a Makarantar Firamare ta Bare ba ta san da hakan ba. Wannan makaranta tana nuna sakaci da gazawar masu mulki. An kafa makarantar ce a shekarar 2005 karkashin shirin Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB). Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a taba samun gyara ko ci-gaba ba. Maimakon zama alamar ci-gaba, makarantar ta...
    Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su iya bin tafarkin zamanantarwa da ya sabawa na yammacin duniya.   A nasa bangare kuwa, daraktan hukumar lura da harkokin waje na kasar Masar Ezzat Saad, cewa ya yi shawarar da Sin ta gabatar ta aiwatar da manufofin zamanantar da duniya, ta samar da karin sassan hadin gwiwarta da kasashen Afirka, tare da yayata kusancin sassan biyu ta fuskar amincewa da juna da hadin gwiwarsu....
    Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.   Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.   “Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.” Idris ya kuma...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa sojojin kasar ta yemen sun cilla makami mai linzami samfurin Zulfikar kan wani sansanin sojojin HKI a kusa da tashar jiragen sama na Bengerion dake birnin Yafa (telaviv. Saree ya kara da cewa sojojin, har’ila yau sun kai wasu hare-hare kan jiragen yaki masu daukar jiragen saman yaki na Amurka Harry Truman da kuma USS...
    Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba ta da wani kyakkyawan tsari da za ta iya kayar da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027. Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai kai tsaye a Abuja ranar Juma’a. Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno Daily Trust ta ruwaito cewa, shugabannin adawa a faɗin ƙasar nan na ƙara zage damtse wajen ganin sun ƙulla alaƙa da nufin kawar da Jam’iyyar APC. Sai dai kuma, mabambantan buƙatu tsakanin manyan masu ruwa da tsaki na ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattaunawar ƙawancen da...
    Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), LEADERSHIP ta Lahadi ta gano cewa har yanzu Gwamntin Jihar bata fara biyan mafi karancin albashin ba. An samu tsaikon yin hakan ne saboda niyyar ita gwamnatin ta dauki su Malaman makaranta matsyin kwararru ta cire daga tsarin albashi na ma’aikatan gwamnati,inda za ta fara biyansu da tsarin albashi na Malaman makaranta(TSS). Kamar yadda Shugaban kungiyar kwadago na Jihar NLC,Okoro...
    Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo sauyi da kuma zamanantar da kafafen yada labarai na Najeriya da watsa shirye-shirye ta hanyar hadin gwiwa da inganta fasaha.   Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai na 2025 da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta kasa da ke Abuja ranar Alhamis.   Da yake jawabi bayan dawowar sa daga taron kungiyar masu yada labarai na duniya (NAB) a birnin Las Vegas na kasar Amurka, ministan ya ce taron mai taken “Fasahar, The Trend, The Future,” ya samar da wani dandali na yin cudanya da masu ruwa da tsaki a duniya kan sabbin abubuwa da suka...
    Masarautar Gumel ta ce za ta bayar da dukkan goyon baya da hadin kai da ake bukata domin ci gaban yankin kasuwancin da ba shida shinge na Maigatari a jihar Jigawa.   Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Mohammad Sani ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin Jiha mai kula da shiyyar fitar da kaya ko kasuwanci maras shinge na Maigatari a fadar sa.   Ya ce, nan ba da dadewa ba majalisar masarautar za ta shirya taro da hakiman Gundumomi da Unguwanni da Kauyuka domin fadakar da al’ummarsu kan gudunmawar da suke bukata domin samun nasarar wannan yankin.   Sarkin wanda ya samu wakilcin Dallatun Gumel, Alhaji Musa Ayuba ya ce aikin noman rani da...
    Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Aminu Kano a Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta shirya taron shekara-shekara karo na 23 don tunawa da cika shekaru 42 da rasuwar Malam Aminu Kano.     A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya jaddada muhimmancin taron shekara-shekara wajen kiyaye manufofin da Malam Aminu Kano ya tsaya a kai.   Farfesa Haruna Musa wanda mataimakin shugaban jami’ar kula da harkokin ilimi ya wakilta, ya bayyana cewa jerin laccoci an yi niyya ne don ba da damar fahimtar juna dangane da yanayin tarihi.   “A ci gaba da kokarin da jami’ar mu ke yi na karfafa al’adun dimokuradiyyar Najeriya, muna gayyatar manyan mutane duk shekara don gabatar da laccoci a gidan Mambayya kan...
    Hakazalika, kamfanoni 43 da aka bayyana sun ba da shawarar raba jimillar Naira tiriliyan 1.678 ga masu hannun jarinsu, tare da yaba wa abokan huldarsu. A cikin 2024, bangarori na kasuwancin Nijeriya ya gamu da kalubale masu yawa na tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa wadanda suka yi matukar tasiri ga ayyukansa. Masana’antun sun fuskanci matsin lamba daga hauhawar farashin kayayyaki, faduwar darajar Naira, hauhawar kudin ruwa, karin kudin wutar lantarki, karancin tallace-tallace, yawan haraji da kuma tabarbarewar tsaro. A cikin wannan babbana al’amari, kamfanoni a manyan sassan tattalin arziki sun ba da rahoton sakamako mai karfi na kamfanoni da kuma bayar da lada ga masu hannun jari. Idan za a kimanta halin da ake ciki, babban jami’in...
    Mata da ’yan mata da suka tsira daga tashin hankalin ‘yan Boko Haram a Arewa Maso Gabashin Nijeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, ciki har da shiga tsananin damuwa da fuskantar nuna wariya da rashin samun dama na neman kuɗi da kuma uwa-uba rashin samun kulawar gwamnati da na al’umma. A lokacin tashin hankali da yaƙe-yaƙe mata da yara ne suka fi shan wahala sosai daga munanan hare-haren da ke shafar lafiyar jikinsu da ta ƙwaƙwalwarsu, sannan sun fi kowa faɗawa matsalar tattalin arziƙi da shiga cikin ɗimuwa. Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista Tun farkon fara rikicin Boko Haram a watan Yulin 2009, mata da...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Cibiyar Hind Rajab Foundation da ta mayar da hankali kan neman gurfanar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki, ta mika bukatar kama Gideon Sa’ar a birnin Landan na Birtaniya. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun jiyo ofishin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila na cewa babu wata niyyar takaita ziyarar Sa’ar...