Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
Published: 25th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya da fasaha don shiga zagaye na uku na shawarwarin da ba na kai tsaye ba da Amurka ta hanyar shiga tsakanin mahukuntan Oman.
Baqa’i ya bayyana cewa: Bangarorin biyu sun amince da gudanar da tarukan fasaha tare da halartar manyan jami’an shawarwari, yana mai bayanin cewa “bisa tsarin da Oman ta shirya da kuma hadin gwiwa tsakanin Iran da Amurka, za a gudanar da tarukan fasaha da shawarwari kai tsaye tsakanin ministan harkokin wajen Iran da wakilin shugaban Amurka na musamman a ranar Asabar.”
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaban da ake samu a shawarwarin yana bukatar daya bangare ya nuna kyakykyawar fahimta, da gaske, da kuma hakikanin gaskiya, yana mai jaddada cewa: Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi aiki ne bisa gogewar da ta gabata da kuma dabi’ar daya bangaren, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cimma halaltacciyar hakki da muradun al’ummar Iran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa, ambaliya da iska mai ƙarfi sun rushe da lalata gidaje 171 a yankunan jihar cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya haddasa asara da kuma mutuwar yara huɗu.
Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe, inda ya ce iftila’in ya shafi ƙananan hukumomin Dukku da Kwami da Gombe da Akko.
Harin Filato: Remi Tinubu ta ba da gudummawar Naira biliya 1 Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad“Mun samu rahoton rushewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe da kuma 27 a Akko, ciki har da wata coci da ambaliya ta lalata.
Haka kuma yara huɗu sun rasa rayukansu, mafi yawansu yara ne,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, rashin tsaftar muhalli da kuma yawan sare bishiyoyi na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen haddasa ibtila’in.
Ya yi kira ga al’umma da su daina zubar da shara a cikin magudanan ruwa, tare da amfani da wuraren zubar da shara da gwamnatin jihar ta gina.
“Akwai buƙatar kowa ya taka rawar gani wajen kare muhallinsa, musamman a lokacin damina.
Iyaye su kula da ‘ya’yansu, musamman ma yara ƙanana domin gudun afkuwar hatsarin faruwar hakan,” in ji Malam Abdullahi.
Sakataren SEMA ya kuma yi tir da yawan sare bishiyoyi domin yin gawayi na girki, yana mai cewa hakan yana ƙara haddasa fari da kuma rushewar muhalli.
Sai ya shawarci jama’a su ci gajiyar daminar da ake ciki wajen dasa bishiyoyi a gidajensu da unguwanninsu domin rage ƙarfi da haɗarin iska da kuma yaƙi da hamada.
Malam Abdullahi ya ƙara da cewa, Hukumar SEMA na shirin kai kayan tallafi ga waɗanda ibtila’in ya shafa a sassan jihar.