2025-12-01@20:58:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4946

«Francis»:

    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka...
    Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu. Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna. ’Yan sanda sun gano zinaren N23m...
    Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa....
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda...
    Daga Abdullahi Jalaluddeen  Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da  babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya...
    Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni. Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta....
    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma  ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi. Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki...
    Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi. Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da...
    A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a nan birnin tehran inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafin alakokin dake tsakani da kuma ci gaban yankin. Ganawar wani bangare ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.   Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga maniyyatan jihar na shekarar 2026, biyo bayan rage kudin kujerar aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar. Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya...
    A birnin Dublin na kasar Ireland an cire sunan tsohon sugaban “Isra’ila” Chaim Herzog,daga wata lambu na shakatawa a unguwar Ratgar, tare da maye gurbinsa da sunan Shahida Hind Rajab. Jaridar “Vadiot-Ahranot” ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa, hukumar birnin Dublin a Ireland ta amince da a sauya sunan shugaban “Isra’ila” ta shida Chaim...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.  Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana halin da Falasdinu ke ciki da rauni mafi muni da aka aikata kan bil adama a doron kasa. A yayin bikin Ranar Falasdinu ta Duniya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sake nanata goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bai wa Falasdinawa, tana mai bayyana halin da suke ciki...
    An yi gangami a fadin duniya domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu a daidai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Falasdinu a ranar 29 ga watan Nuwamba da MDD ta kebe. A faransa a gudanar da irin wannan gangamin, inda suka yi Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza...
    Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5. kwatankwacin tagomashi na kashi 1.53% idan aka kwatanta da bara warhaka. Bayanin da aka samu daga hukumar kwastam ta Iran ya ce: “A wannan lokacin, an fitar da tan 105,231,000...
    Wata fitacciyar sinima a Faransa, Cinematheque Francaise, ta rufe ɗakunan kallonta na tsawon wata guda saboda yaɗuwar kuɗin cizo da aka gano a cikinta Cibiyar wadda ke gabashin birnin Paris ta ce rufe sinimar zai ba ta damar tabbatar da cewa masu kallo sun samu “aminci da kwanciyar hankali” bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi na...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar hizbullah ta kasar Labanon ta yi kira ga shugaban cocin katolika na duniya pope leo na 14 da zai kai ziyara kasar labanon da yayi tir da hare hare da rashin adalcin da isra’ila ke yi kan kasar labanon duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a...
    Rahotanni sun bayyana cewa iran ta yi tir da sanarwar da shugaban Amurka ta fitar na rufe sararin samaniyar kasar venuzuwela kuma ta bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da kuma dokokin kula da zirga –zirgar jiragen sama. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baghae ne ya fitar da wannan sanarwa...
    A ranar nuna goyon baya ga alummar falasdinu shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari ya jinjinawa Alummar falasdinu game da juriya da tsayin Dakar da suka nuna, yace jarumtar da suka nuna ta bude sabon shafin tarihi, don haka gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka yana da muhimmanci sosai. Kasar Pakistan...
    Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake aike wa Majalisar Dattawa ƙarin sunayen mutum 32 domin tantance su a matsayin jakadu. Sunayen sun haɗa da manyan mutane kamar tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri. Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in...
    Babban kwamandan sojojin kasa na JMI Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su maida martani ko kuma kai hari kan makiya a duk lokacinda suka takali kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hatami  yana fadar haka a bikin kaddamar da jiragen ruwan yaki masu suna...
    Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a cikin watan Yunin da ya gabata. Daga ciki har da jiragen yaki samfurin Heron da Hermes -900 wadanda ke aiki da kayakin zamani. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran...
    Kamfanin kera jiragen sama na ‘Airbus’ ya bukaci duk wadanda suka sayi jiragen sama samfurin A320 ya dawo da shi saboda aiwatar da wata gyra a tsarin tuka jiragen. Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto kamfanin yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Wannan shine karon farko...
    An kammala gasar gina manhajan komfuta ta kasa da kasa farko a jami’ar Amir Kabir take nan Tehran . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an gudanar da gasar ne  tsakanin kasashe 30 daga yankuna daban daban na duniya, kuma an kammala gasar a jiya Jumma’a 28 ga watan Nuwamban da...
    Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen...
    Ofishin Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike bayan kisan gillar da sojojin Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a ranar Alhamis a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, bayan sun daga hannayensu suka mika wuya. “Mun firgita da kisan gillar da ‘yan...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ya jaddada cewa ayyukan Isra’ila, ciki har da kisan kai da ayyukan ta’addanci, ba komai ba ne illa wauta, domin “muna da dubban ƙwararrun nukiliya a Iran.” Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce a ranar Juma’a a wata hira da HUM News...
    Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, da nufin samar da sauki wajen samun kudade a cikin kasar. Hakan ya sanya Bankin, ya sayar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar. Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a...
    Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun...
    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan...
    Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe. An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti...
    Rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da shahadar  mayakanta biyu a yammacin kogin Jordan sanadiyyar harin da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai. Daya daga cikin shahidan shi ne Yusuf Ali Asa-Asa, dan shekaru 37, da kuma Mahmud Abdullah dan shekaru 26, sun kuma yi shahadar ne a jiya Alhamis.  Sanarwar...
    A bayanin da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar a yau, ta yi tir da harin da sojojin na “Isra’ila” su ka kai wa kauyen Beit-Jin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13. Bayanin ya kara da cewa; Harin, yana a matsayin keta hurumin shugabancin kasar Syrai da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya ce; Hadin kai a tsakanin al’umma yana a matsayin sakamako ne da Imani da aikin kwarai. Hujjatul-Islami Wal Muslimin Sayyid Muhammad Hassan Abu Turabi ya bayyana cewa; Aiki da hankali, da sani, da fahimtar siyasa tare da ruhi mai tsarki su ne ke haifar da hadin kai....
    Dubban mutane sun taru a Jihar Bauchi, don halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa. Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin ba jama’a damar halartar jana’izar malamin. Trump zai haramta wa ’yan...
    Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kai hari ne a garin beit Jin dake gefen birnin damaskas da ya kai ga mutuwar mutane 10 yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, wannan ya faru ne bayan rikici da ya barke tsakanin mazauna yankin da kuma sojojin Isra’ila da ya kai ga jikkata sojoji 6...
    Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman...
    Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen...
    Babban Sufeton ’yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce sun janye ’yan sanda 11,566 da ke rakiyar manyan mutane kamar yadda Shugaban Ƙasa ya ba da umarni a kwanakin baya. Ya kuma ce an sake tura waɗannan jami’an zuwa muhimman wuraren da aka fi buƙatars su don kare al’ummomi masu rauni a fadin ƙasa. NAJERIYA...
    Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa  karshen shekarar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta gano gawar wasu mata uku ’yan ƙasar Kamaru da ake zargin waɗanda suka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa sun kashe su. Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, Nonso Augustine Akpeh da Kingsley Akpeh, waɗanda ake...
    Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauka sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa jami’yyar haɗaka ta ADC. Komawar El-Rufai jam’iyyar ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane...
    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa....