Aminiya:
2025-04-30@19:41:27 GMT

An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal

Published: 29th, April 2025 GMT

An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai.

A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita.

Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu.

Wata sanarwa da hukumar samar da wutar lantarki a Spain ta Red Electrica ta fitar, ta ce da misalin ƙarfe 7 na safiya agogon ƙasar, an samu nasarar dawo da sama da kashi 99 na wutar lantarki a ƙasar.

Haka nan ita ma takwararta ta Portugal ta ce tun cikin daren jiya Litinin, aka dawo da wutar lantarkin da dukkanin tashoshin wutar ƙasar guda 89.

Bayan ɗauke wutar da aka samu a Spain, jami’an ba da agajin gaggawa sun sanar da nasarar kuɓutar da mutane dubu 35 da suka maƙale a jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.

Har yanzu dai hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka samu ɗaukewar wutar lantarkin ba, wanda shi ne karo na biyu da irin wannan mummunar katsewar wutar lantarki ta faru a Turai cikin watanni

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sifaniya Wutar Lantarki da wutar lantarki wutar lantarki a wutar lantarkin

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai

A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana.

An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida.

DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno

PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba.

Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0 a Emirates a cikin watan Oktoba.

Arsenal da Paris Saint-Germain da Inter Milan da Barcelona su ne kungiyoyin da 4 da suka kai matakin zagayen daf da karshe na gasar.

A wannan Larabar ce kuma za a yi karon batta tsakanin Inter Milan da Barcelona, bayan kimanin shekara 15 da aka yi makamancin wannan karawar daf da karshe tsakanin ƙungiyoyin biyu a Gasar Zakarun Turai.

Inter Milan ce ta kai zagayen ƙarshe a 2010, sai dai wannan karon Barcelona na fatan lashe kofin bana da zarar ta fuskanci Arsenal ko Paris St Germain a watan gobe.

Sai dai, Barca da Inter sun fuskanci juna a gasar ta zakarun Turai a 2022/23, inda ta Italiya ta yi nasara 1-0 cikin Oktoban 2022 a wasa na biyu suka tashi 3-3 a Sifaniya.

Wannan shi ne karon farko da Barcelona ke fatan kai wa karawar ƙarshe a Champions League, tun bayan da ta lashe na biyar jimilla a 2015.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027
  • Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
  • Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato 
  • HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
  • Kano: Galadima biyu a masarauta ɗaya
  • Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal
  • Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku
  • Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
  • Tawagar ‘Yan Sama Jannati Na Shenzhou 19 Za Su Dawo Doron Kasa A Ranar Talata