Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Binciken Yawaitar Haɗurran Tankokin Man Fetur A Nijeriya
Published: 29th, April 2025 GMT
Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN).
Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamatin, Ministan Sufuri, Sanata Said Alkali, ya jaddada muhimmancin shawo kan kalubalen hadurran da ke ci gaba da barazana da haddasa munanan asarar rayuka da dukiyoyi.
Alkali wanda ya jaddada bukatar a gaggauta kawo karshen wannan mumunan lamari, ya bai wa kwamitin mako guda ya gabatar da rahotonsa, inda ya jaddada cewa, tsaro da inganci su ne kan gaba a cikin manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana.
Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.”
Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa.
Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp