2025-07-03@05:16:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5191
«kwamitin da»:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kafin sanar da sabuwar ƙawance da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yi wa wannan haɗaka zagon ƙasa da kawo cikas ga tafiyar. Ɗaya daga cikin irin waɗannan zagon ƙasa da ake zargin wasu da yi wa wannan sabuwar haɗaka, ita ce na sanar da su rashin samun ɗakin taron da suka shirya gudanar da taron lokaci ƙalilan gabanin taron. NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan...
Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu. Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani Sadik, da sauransu suka kai wa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ziyarar goyon baya. Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba Wannan ya tunzura Alhikma kasancewar wasu daga cikin wadanda suka je mubayi’ar ‘ya’yan kungiyar YBN ne a baya, da kuma 13/13 ta ubangidansa, mawaki Rarara. A cikin wadanda Alhikima...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba a taron manema labaru da aka gudanar cewa, kayayyakin Sin sun shiga kasuwar duniya, inda suka kara baiwa masu sayayya na kasa da kasa damar samun zabi. Jami’ar ta yi tsokacin ne bisa yadda batun wasu kayan shayi na kasar Sin ya jawo hankalin sassan kasa da kasa, bayan shigarsu kasuwar hannun jari ta kasashen waje. Mao Ning ta bayyana cewa, kayayyakin Sin sun kara jawo hankulan masu sayayya na kasa da kasa ta hanyar fasahohi, da shaida al’adun gargajiya, da zane-zane da suke dauke da su, da kuma abubuwan dake hade Sin da kasashen waje. Daga kayayyaki kirar kasar Sin zuwa tambarin kayayyakin Sin, kasar Sin...
Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025. A jawabinsa wajen taron kaddamar da daliban, kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin sa na farko daga samun wannan mukami shi ne batun kafa hukumar Gudanarwar Kwalejin da sake fasalin Kwalejin, wanda hakan ya bada damar tantancewa da kuma samun amincewar Cibiyar kula da makarantun aikin Jinya ta Najeriya. Yana mai cewar, daukar wannan mataki ya bada damar kara yawan dalibai da Kwalejin take dauka daga 120 zuwa 240,...
Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su. Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta dakatar da duk wani tallafin makamai da take bai wa Ukraine din. Hamas ta karɓi tayin tsagaita wuta a Gaza Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada hare-harenta a kan kasar, yayin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza yaki tsakanin kasashen da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Hamas ta sanar da karɓar tayin tsagaita wuta a yaƙin Gaza kuma tuni ta soma nazarin sabuwar yarjejeniyar aka gabatar mata. Hamas wadda ta nuna alamun samun masalaha ta bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra’ila da janye dakarunta daga yankin. Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC Ƙungiyar ta ce tana tuntuɓar abokan shawararta, sannan ta jinjina wa ƙoƙarin masu shiga tsakanin. Shugaban Amurka ne ya gabatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60, wadda ya ce tuni gwamnatin Isra’ila ta amince da ita. To sai dai rahotonni na cewa da dama cikin ministoci masu ra’ayin riƙau ba...
Jakadan Pakistan a kasar Sin, Khalil Rahman Hashimi ya ce, “sabuwar dokar ta bayar da karin kariya har ma da wani sauki na musamman ga kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin. Akwai tanade-tanade da dama a kasar Sin wadanda suke bayar da kwarin gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu don su iya bunkasa harkokinsu da kuma ba da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin kasar Sin. Akwai samun moriya da dama da kuma goyon bayan gwamnati har ma da ba da kariya ta fuskar shari’a ga kamfanoni masu zaman kansu.” Shi ma jakadan Nepal a kasar Sin, Krishma Prasad Oli ya ce, “dokar ta sahale wa kamfanoni su gudanar da ayyukansu ba tare da wani matsi ba. Akwai babbar dama...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar Fasaha ta Zamani ta Arewa maso Yamma da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta gina a Kano, wadda matasa suka lalata a lokacin zanga-zangar ƙuncin rayuwa ta #EndBadGovernance a watan Agustan 2024. Ministan Harkokin Sadarwa Dr. Bosun Tijani, ne ya wakilci shugaban ƙasa a wajen bikin ƙaddamarwar. A jawabin sa, Minista Tijani ya bayyana cewa wannan katafaren aiki da gwamnatin Tinubu ta samar ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, zai iya zama babbar hanya ga matasa su tsira daga talauci idan har suka yi amfani da damar yadda ya kamata. Ya bayyana damuwarsa kan lalata cibiyar mako guda kafin a ƙaddamar da ita, duk da cewa an kammala aikin tun watan Janairu....

Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun kuduri aniyar kare kan iyakokin Iran da tsaron kasar da kuma al’ummarta Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce: “Suna goyon bayan zaman lafiya, kuma ba su amince da yaki ba, amma a lokaci guda kuma, suna tabbatar da aniyarsu ta kare kan iyakokin Iran da tsaron kasarta da kuma al’ummarta.” A yau, Laraba ne, Shugaban kasar Iran Pezeshkian ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sadarwa, inda ya jaddada babban kudirin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na kare kan iyakokin kasar da tsaro da al’ummar kasar. Yana mai jaddada cewa: “A tushen al’adu da wayewar Iran, suna da gogewa da yawa wajen rage wahalhalun da mutane ke fuskanta.” Shugaban ya kara da...
Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin. Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba,...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar ta Iran. Riyabkov ya shaidawa manema labarai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow cewa: “Za su karfafa hadin gwiwa a aikace tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa: Dole ne a karfafa karfin tsaron kasar Iran, saboda Rasha tana da gogewa mai kima a wannan fanni, kuma za ta ci gaba a kan hakan.” A ofishin jakadancin...
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a zirin Gaza tun da sanyin safiyar Laraba. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Akalla fararen hula 6 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai harin bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis. Sannan wasu Fararen hula 10 da suka hada da kananan yara suka...
Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare. ’Yan sanda sun kama wani mutum da jabun kuɗi a Gombe Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba A wajen babban taron da ta gudanar a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, Nwosu ya ce: “Mun sauka daga muƙamanmu domin mu bai wa David Mark dama ya jagoranci wannan tafiya zuwa fadar shugaban ƙasa.” Ya yaba wa Aregbesola, wanda ya taɓa kasancewa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum, mai shekaru 35 daga ƙauyen Kunji da ke Kwadon, bisa zargin mallakar jabun kuɗi. Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama Kawu ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025, a ofishin ’yan sanda na Lawanti, sannan aka kai shi ofishin Amada domin ci gaba da bincike. Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba Ya ce an samu dalar Amurka 1,000 da ake zargin na bogi ne (kimanin Naira miliyan 1.5), da kuma Naira 10,000 a cikin kayansa. A yayin bincike, Kawu ya amsa cewa kuɗin na wani mutum ne. ’Yan sanda sun ce suna ci...

Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5
Yau Laraba, Hukumar Kula da Fasaha ta Kasar Sin (MIIT) ta ba da rahoton yanayin tafiyar masana’antar manhajoji ta kasar daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2025 da muke ciki. A cewar rahoton, masana’antar manhaja da hidimar fasahar sadarwa ta Sin tana gudana yadda ya kamata. Da farko, yawan kudaden shiga da aka samu kan sana’ar manhaja ya karu karara. Daga Janairu zuwa Mayu, adadin ya kai kudin Sin yuan triliyan 5.5788, wato ya karu da kashi 11.2% idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara. Na biyu, ribar da aka samu a fannin kuma ta habaka da kashi 10% ko fiye. Daga Janairu zuwa Mayu, jimilar ribar da aka samu a bangaren sana’ar manhaja ta kai kudin Sin...
‘Yan tawagar jam’iyyar UDA ta kasar Kenya da suka kawo ziyara kasar Sin sun kwatanta jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da bishiyar kuka, suna cewa, “Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tamkar bishiyar kuka ce, wadda ke da ingantattun saiwoyi da ma babban karfi na warkar da kanta, tana ta fid da furanni da ‘ya’ya ba tare da tsayawa ba” “bishiyoyin kuka suna da tsawon rai na sama da shekaru dubu”. Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana cikin karfinta, kuma za ta ci gaba da kokartawa domin bauta wa jama’a, tare da dogara da jama’a don cimma karin nasarori. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jajanta wa mutanen da ambaliya da guguwa suka shafa a ƙananan hukumomin Damboa da Askira-Uba. A cikin kwanakin da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haifar da ambaliya a ƙauyukan Wovi da Gumsuri na Damboa. Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Wannan ambaliya ta yi sanadin mutuwar mata biyu, kuma ta lalata gidaje da raba mutane da muhallansu. A wani ɓangare kuma, guguwa mai ƙarfi ta afka wa garin Rumirgo da ke Askira-Uba, inda ta lalata gidaje da dukiyoyin jama’a. Dauda Iliya, mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar da...
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus. Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba. David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Zaman ya gudana ne a harabar tsohon gidan gwamnatin jihar. Hon. Nanloong Daniel, wanda ke wakiltar mazaɓar Mikang wanda kuma tsohon jagoran masu rinjaye ne a majalisar ta tara, ya samu amincewar dukkanin ’yan majalisar 24 don jagorantar su. Daniel shi ɗan jam’iyyar APC ne. Zaɓen nasa ya biyo bayan wani zaman sirri da aka yi tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang,...
Shugaban Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Jabaka, ya yi kira ga al’ummar yankin da su dauki matakan kariya domin dakile yaduwar cutar kwalara da sauran cututtukan da ke yaduwa cikin sauri a yankin. Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kan matakan da hukumar ta dauka domin dakile barkewar cutar ta amai da gudawa a wasu sassan karamar hukumar. Alhaji Jabaka ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli, musamman wajen tsaftace rijiyoyi da sauran hanyoyin samun ruwan sha, wuraren da ake dafa abinci, da kuma tsaftace muhalli gaba daya, tare da tsaftar jiki wanda ya ce shi ne mabuɗin hana yaduwar cutar ta kwalara. A cewarsa, kwalara cuta...
“Ba za su samu tayin da ya fi wannan ba abu zai ƙara muni idan suka ƙi.” Har yanzu babu martani daga jami’an Isra’ila kan iƙirarin Trump ba. Tattaunawar neman tsagaita wuta ta tsaya cak tun watanni da suka gabata saboda rashin jituwa kan matakin da za a ɗauka bayan an daina faɗa. Isra’ila tana son ta ci gaba da samun damar kai farmaki idan ta ga dama, amma Hamas tana so a daina faɗa gaba ɗaya. Ana sa ran Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai kai ziyara fadar White House a mako mai zuwa. Trump ya ce zai yi magana da Netanyahu domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin. A farkon shekarar nan, wani ƙoƙari na tsagaita wuta ya rushe a...
Babbar Kotun Jihar Filato da ke zamanta a Jos, ta yanke wa dalibin nan na makarantar GSTC Bukuru, Odey Emmanuel, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe malamin makarantarsu a kan abinci. Alkalin kotun, Mai Shari’a S.J. Bakfur, ya ce an sami Odey ne da laifin na kisan kai wanda kotun ta ce ya saba da tanade-tanaden sassa na 188 na 189 na kundin dokar manyan laifuffuka ta jihar Filato ta shekara ta 2017. Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu A cewar alkalin, masu shigar da kara sun gabatar da hujjojin da suka iya gamsar da kotun cewa wanda ake zargin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata . Ya kuma kara da cewa hare-haren sun yu watsi da hanyar zaman lafiya da kuma zaman lumana a yankin. Ya kuma yi sanadiyyar karin tashe tashen hankula a yankin. Ministan ya bukaci kasashen duniya gaba daya su yi tir da HKI da kuma Amurka wadanda suka keta hurumin kasa mamba a MDD ba tare da wani daloli nay an haka ba. Ya ce hare-haren da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga mutanen kasar da daukaka. Don haka gwamnati mutanen kasar ba zasu taba yarda a barshi ba. Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da tashar talabijin ta CBS news na kasar Amurka dangane da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar a cikin watan yuni da ya gabata. Hare-haren da aka kaiwa kasar a dai-dai lokacinda take tattaunawa da Amurka. A wani bangare a maganars Aragchi ya bayyana cewa baya ganin Iran zata farfado da tattaunawa da kasar Amurka nan kusa. Ya ce: Idan har zamu sake shiga tattaunawa da...
Firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia assudani ya bayyana cewa kasarsa ta shigar da karar HKI a gaban kwamitin tsaro na MDD saboda keta hurumin sararin samaniyar kasar don kaiwa kasar Iran hare-hare. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sudani yana fadar haka, ya kuma kara da cewa HKI ba tare da neman izinin gwamnatin kasar ba a cikin yakin kwanaki 12 da JMI ta shiga sararin samaniyar kasar daga nan kuma ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin da kuma cibiyoyin fararen hula daga kasar ta Iraki. Duk ba tare da amincewar kasar ba. Firai ministan ya yi allawadai da hare-haren ya kuma bukaci a huklunta HKI kan hakan. Y ace kasar Iraki bata da garkuwan sararin...
Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta. Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.
Ya ce kamar yadda mutane suka karanta a jarida, shi ma ya karanta, amma babu gaskiya cikin batun. Ya ce a yanzu, kowa ya san yana cikin PDP kuma yana da matsayi a jam’iyyar, bai bar ta ba kuma da yardar Allah zai ci gaba da zama a cikinta. Ya ce dalilin da ya sa wasu ke son ya koma APC shi ne domin jam’iyyar APC a Filato ba ta da shugabanni nagari, shi ya sa suke kallon shugabannin PDP da fatan su shiga jam’iyyar domin kawo gyara. Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin APC na ƙasa suna sha’awar abubuwan da PDP ta yi a Filato, kuma suna ganin irin waɗannan ayyuka na buƙatar shugabanni masu nagarta. Amma...
Aregbesola, wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Osun, ya ƙara da cewa jam’iyyar siyasa bai kamata ta zama hanyar neman mulki kawai ba ko wata dama ga wasu tsiraru ba. Ya ce jam’iyya ta gaskiya ita ce wadda ke da tsari da manufa, kuma wadda ke aiki don jama’ar da ta ke wakilta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai magana da yawun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce sam maigidan nasa bai yi wani abu don yi wa yunƙurin Bola Tinubu na zama Shugaban Najeriya a 2023 zagon ƙasa ba. Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata yayin wani taron manema labarai gabanin kaddamar da sabon littafin da ya rubuta a kan zamansa mai magana da yawun Buhari, wanda za a kaddamar ranar tara ga watan Yuli. ’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa An dai yi zargin cewa da gangan Buhari ya jinkirta cire tallafin man fetur har zuwa karshen mulkinsa a 2023 domin ya hada ’yan Najeriya fada da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare. A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali. NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa. Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025. Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina SP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari. Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a...
Cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; a Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Hassan Abdullahi, Daraktan Tsaro na Cikin Gida a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), wanda ya wakilci NSA. Wasu fitattun malamai na addinin Musulunci da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jiddah sun haɗu da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Modibbo, tare da Ambasada Mu’azzam Ibrahim Nayaya, da Manjo Janar Adamu Hassan,...

An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin
A yau Talata ne gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gudanar da bikin daga tuta, da bikin murnar cika shekaru 28 da dawowar yankin musamman na HK karkashin ikon kasar Sin. Da yake jawabi yayin taron, kantoman yankin Lee Ka Chiu John, ya ce tun bayan kama aikinsa, gwamnati mai ci a HK, ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don gina yanki mai tsaro da daidaito, tare da zage damtse wajen gina tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’ummarsa, kuma sannu a hankali matakan na haifar da mai ido. Lee ya ce, a nan gaba, zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da samun ci gaba mai inganci, da managarcin yanayin tsaro, kana zai gaggauta bunkasa yankin...
A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CBS, Araqchi ya yi tsokaci kan ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana iya komawa tattaunawa da Iran a cikin wannan mako: Araqchi yana mai mayar da martini da cewa: “Ba ya jin za a dawo da tattaunawar cikin gaggawa.” Ya kara da cewa: “Kafin yanke shawarar komawa kan tattaunawar, dole ne Iran ta fara tabbatar da...
Magajin garin birnin Tehran ya bayyana cewa: Karyar ‘yan sahayoniyya ya tonu na cewa ba su kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran ba Magajin garin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ali-Ridha Zakani ya tabbatar da cewa: Karairayi da ‘yan sahayoniyya suke yadawa dangane da rashin kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran a fili yake karara. Yana mai nuni da cewa akwai kwarararn dalilai da ake da su wadanda suke fallasa karyar wadannan ikirari. A cikin bayanansa, Zakani ya ce: Dalilai kan wadannan karairayi su ne kaburbura gawawwaki da suka hada da fili mai lamba ta 42 a makabartar Al-Jannar – Zahra da ke babban birnin Tehran. Ya...
Kotu a kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Ayatullah Baqir Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda Hukumar tsaron kasar Iraki ta sanar a ranar litinin cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aiwatar da zaluncin kisa kan Ayatullahi Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda. Ofishin yada labarai na hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan masu laifin Sa’adoun Sabri da Haitham Abdul Aziz, bayan da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen aiwatar da hukuncin kisa kan Shahadar Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa, Alawiyya Bint al-Huda a...
Mummunan kisan kiyashi kan ‘yan darikar Alawiyyan Siriya, kuma wadanda aka yi wa kisan gilla a kasar a watan Maris sun kai mutane 1,479 A cikin binciken da ya yi na baya-bayan nan, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cikakkun bayanai na kisan gillar da aka yi tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris din wannan shekara ta 2025, inda aka kai wa ‘yan darikar Alawiyya hare-hare a yankin gabar tekun Siriya. Binciken ya tabbatar da mutuwar Alawiyawa 1,479 da bacewar wasu da dama a wurare daban-daban guda 40, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen hankula da daukar fansa kan tsirarun mabiya mazhabobin Musulunci a kasar ta Siriya. Kamfanin dillancin labaran reuters ya wallafa binciken nasa ne bisa...
Tawagar likitocin kasar Sin ta 24 wadda ke jamhuriyar Nijer, ta ba da horon fasahar likitancin gargajiya ta Sin a babban asibitin Nijar dake birnin Yamai, wanda ya jawo hankulan mahalarta kusan 50, ciki har da manyan ma’aikatan kiwon lafiya na asibitin, da dalibai daga kwalejin likitanci ta jami’ar Yamai da kuma masu sha’awar likitancin gargajiya na Sin. Zheng Zhida, shugaban tawagar likitoci ta Sin, ya bayyana a bikin kaddamar da horon cewa, tun bayan kafa cibiyar likitancin gargajiya na Sin dake babban asibitin Nijar, duban-dubatar marasa lafiya sun amfana da ita. Ya ce horon na wannan karo ba darasi ne kawai dake bada fasahohin likitanci ba, wani aiki ne na mu’ammalar al’adu. A nasa bangare, farfesa Mamane Daou, daraktan...

Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta
Yau Talata ita ce ranar cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS. A cikin lokacin sanyi na shekarar 2012, jama’ar kasar Sin sun wayi gari da ganin motocin gwamnati kalilan ne ke kai-komo a kan tituna, kuma an daina amfani da kudin gwamnati wajen shirya liyafar cin abinci a gidajen cin abinci masu tsada, kana hatta kyautar da ake bayarwa ta kek, watau “Mooncake” lokacin bikin tsakiyar kaka an rage girmanta daga dan karamin akwati zuwa wani karamin kunshi. Wannan shi ne sauyin da aka samu bayan aiwatar da shahararrun “Ka’idoji Takwas” na jam’iyyar JKS. Matakin da aka dauka na dokoki ya zama tamkar wani magani mai karfi wanda ke warkad da “cututtukan” da suka...
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da ƙaddamar bincike a game da harin da dakarunta suka kai kan wata cibiyar intanet da ke yankin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbin fararen hula a jiya Litinin. Hukumar kare lafiyar fararen hula ta Falasɗinu, ta ce wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta harba a jiya Litinin sun faɗa kan kasuwar kwamfuta ta ‘Al-baqa’ da ke gaɓar teku da ke birnin Gaza, kuma a wannan cibiyar kaɗai mutane 24 ne suka rasa raukansu. Ɗaya daga cikin masu magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, tabbatas sun kai hare-hare kan wurare da dama da dakarun Hamas ke fakewa don gudanar da ayyukansu a Gaza, to...
Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba. Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na bayyana cikin tsananin firgici da damuwa, alamar cewa yana fuskantar tilas daga barayin daji da suka umurce shi da ya faɗi abin da suke so. Da yake martani kan bidiyon, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa wannan wata sabuwar dabara ce da ɓarayin suka bullo da ita don jawo hankali. Ya ce, “Idan aka kalli bidiyon da kyau,...
Hakazakika, an zakulo Mata dalibai daga wasu zababbun makarantun sakandare a jihar da kuma wasu daidaikun Mata a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna. Da yake kaddamar da Rabon Kayan, Shugaban Ma’aikatar Fadar Gwamnatin jihar Kaduna Malam Liman Sani Kila, ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu na tallafawa Mata Da Matasa a fadin kasar baki daya. Hakazakika, ya jinjinawa Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani bisa bubbasar da takeyi wajen tallafawa Mata Da dalibai Mata Da masa abin a Yaba ne Yana Mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta himmatu wajen ciyar da aikin Noma a jihar Kaduna. Kila ya kuma jinjinawa Hajiya Hafsat Uba wajen jajircewata wajen...

Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci
Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa ta bai daya, tare da raya tattalin arziki na teku mai inganci da dai sauransu. A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kafuwar babbar kasuwa ta bai daya a ciki kasar Sin ta dace da bukatunmu na bullo da sabon tsarin neman ci gaba da samun bunkasa mai inganci, don haka ya kamata a aiwatar da aikin bisa manufar kwamitin tsakiya, da daidaita ayyuka...
Bayanai daga makusantan fitaccen attajirin nan da ya riga mu gidan gaskiya, Alhaji Aminu Ɗantata sun nuna cewa an ɗage jana’izarsa da aka shirya gudanarwa bayan sallar La’asar a ranar Talata. Yanzu an mayar da jana’izar zuwa bayan Magariba a haramin birnin Madina. Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu A wata zantawa da ya yi da BBC, Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya bayyana cewa tuni gawar Alhaji Aminu ta isa birnin na Madina. “Alhamdu lilLah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya...
Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu. Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota. Hakazalika, ya bayyana cewa Danbokolo na amfani da wata ƙwaya mai suna ‘pentazocine’ domin ci gaba da aikata miyagun laifuka. Yanzu haka, sojojin Operation FASAN YAMA suna ci gaba da neman Bello Turji wanda ya ɓuya. Janar Kangye ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya tana da ƙwarin gwiwar samar da zaman lafiya a dukkanin sassan ƙasar nan. Ya kuma roƙi haɗin kan ‘yan Nijeriya don cimma wannan buri....
Kakakin gwamnatin JMI ta bayyana cewa a dai-dai lokacinda Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar , babu wata tattaunawa da Amurka nan kusa, duk tare da cewa Amurkawan sun bayyana cewa za’a ci gaba da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin gwamnatin kasar Iran Malama Fatimah Muhajirani tana fadar haka a jiya Talata, ta kuma kara da cewa, babu wata rana da aka sanya na tattaunawa da Amurka kuma mai yuwa babu wata tattaunawa da ita nan kusa. Fatima tana maida martani ne ga wata sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayara na, na cewa nan kusa zasu sake farfado da tattaunawa da JMI. Tehran dai ta bayyana cewa bata bukatar wani...
Malaman addinin musulunci daga mazahabar sunna kima 1300 sun tabbatar da cewa gwagwarmaya da HKI wajibi ne a addinin musulunci kuma wajibi ne a Sharia. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanin da malaman suka fitar bayan taron da suka gudanar na cewa tallafawa falasdinawa wadanda HKI take kashewa wajibi ne a sharia. Kuma suna kira ga dukkan malaman sunnan su gane haka su kuma bayyanawa sauran musulmi musamman ahlussa kan cewa jihadi a kan yahudawa sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasar Falasdinu wajibi ne ga wanda yake da ikon hakan. Bayanin ya kara da cewa abinda Falasdinwa suka yi a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023M da kuma fara yakin Tufanul Aksa yana dai...
Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Major General Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a taron addu’a da kuma girmma marigayi Manji Janar Muhammad Baqiri babban hafsan hafsoshin kasar wanda yayi shahada a ranar Jumma’a 13 ga watan Yunin da ya gabata. Ya kuma kara da cewa babban shaitan da kuma karamin shaitan duk zasu halaka sun kasa kaiwa ga bukatunsu a yankin kwanaki 12 da suka...
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 22 ga watan Yulin wannan shekara domin sauraron bukatar ba da belin da Tukur Mamu, da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci Mai shari’a Mohammed Umar ya tsayar da ranar ne biyo bayan dage shari’ar da lauyan Manu, Johnson Usman, SAN, ya nema, domin ba shi damar yin nazari tare da ba da amsa da ya dace kan karar da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya shigar a kansa. A cikin bukatar da Mamu ya gabatar a jiya Litinin 30 ga watan Mayu, ya nemi a bayar da belinsa dsaboda yanayin rashin lafiyarsa. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan...
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar. Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin farar hula, lauyoyi, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin addini. Sanarwar ta ce, “Wannan shiri ya biyo bayan kiran da gwamnatin jihar ta yi tun da farko na gayyatar al’ummomi da su gabatar da buƙatunsu na sabbin masarautun gargajiya. “Kwamitin yana da alhakin tantance waɗannan bukatun bisa ƙa’idar adalci, daidaito, shigar da kowa cikin harkokin siyasa da zamantakewa, da ɗorewar tattalin arziki.” Alhaji Hamza Koshe ne zai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin. Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ibtila’in ambaliyar. Domin sauke shirin, latsa nan
Masu fafutuka a kasar Togo sun sanar da cewa an kashe mutane 7 a yayin Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka yi a makon da ya shude, suna masu tuhumar jami’an tsaro da yin amfani da karfin da ya wuce haddi. Kamfanin dillancin labarun “Reuters” wanda ya nakalto ‘yan fafutukar na kasar Togo, suna cewa; Jami’an tsaro sun yi amfani da karfi mai ban tsoro akan masu Zanga-zangar.” Kungiyoyin fararen hula da na masu kare hakkokin dan’adam 12 ne su ka fitar da sanarwar, su ka kuma kara da cewa; jami’an tsaron kasar sun yi amfani da kulake wajen dukan masu Zanga-zangar, haka nan kuma igiyoyi da suke daure su, kamar kuma yadda su ka sace da lalata dukiyar...
Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya. Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta taba amfani da Kalmar ‘dakatar da fada ba” a mastayin zabi. Haka nan kuma ya ce; ‘Yan sahayoniya ba wadanda za a amince da su ba ne, balle gaskatawa, ba a cikin Iran ba, balle kuma a kowane wuri a duniya.” Shikarci ya kuma yi ishara da cewa; sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwan fiye da kowane lokaci a baya, don haka duk...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s). Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.s) shi ne wanda ya samar da gwarazan mazaje na musamman da shahidai da su ka fuskanci ‘yan mamaya. Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Matasan da su ka yi watsi da duniya su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu...
Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) ta sanar da cewa; Da akwai ‘yan kasar Sudan miliyan 4 da suke rayuwa a kasashen makwabta da suke fuskantar hatsarin yunwa. Sanarwar hukumar ta kunshi cewa mutanen sun fice daga kasarsu ne tun asali saboda neman abinci da kuma mafaka daga yakin da ya barke a cikin Sudan tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023. Bugu da kari sanarwar hukumar ta zo ne a matsayin gargadi saboda yadda ake samun koma bayan taimakon da ake amfani da shi wajen tafiyar da rayuwar ‘yan hijirar. Har ila yau sanarwar ta ce; da dama daga cikin iyalan da suke isa kasashen makwabta, suna cikin gajiya da kuma rashin abinci mai gina jiki, haka nan kuma...
Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin dala biliyan 51.26. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin. Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki watanni biyu bayan ibtila’in ambaliyar. Domin sauke shirin, latsa nan
Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida. Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su. Sai dai wani namiji daga cikin iyalan gidan yai taho mu gama da ɓarawon a cikin wata fafatawa mai zafi da ta jawo raunika a tsakaninsu duka biyu. Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari Kakakin...
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar yin aiki tukuru wajen aiwatar da cikakkun manufofi, na ingiza managarcin jagorancin jam’iyyar bisa kyawawan akidu. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin tsokacin da ya yi, lokacin da yake jagorantar taron nazari na jami’an hukumar siyasar na kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yi watsi da bangaren rahoton kwamitin SAGO, na masana kimiyya mai bayar da shawara game da asalin kwayar cutar da ta haddasa annobar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce a ranar 27 ga watan Yunin nan, kwamitin SAGO, ya wallafa wani rahoto game da tushen kwayar cutar SARS-CoV-2, wadda ta haddasa barkewar annobar COVID-19. Sanarwar ta ce, duk da yake bincike mai zaman kansa da kwamitin SAGO ya gudanar bai nuna wata sabuwar shaida game da asalin kwayar cutar ba, bai kuma bayyana wani abu da ya saba da sakamakon binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO na...
Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce gona da iri kan Iran, kuma har yanzu Amurka ba ta dauki wani mataki ba kan wannan batu. A wata hira da tashar BBC game da batun tattaunawar makamashin nukiliyar Iran da Amurka: Takht-e Ravanchi ya ce: “Sun ji daga Amurka cewa a shirye take ta ci gaba da tattaunawar, amma har yanzu ba a tsayar da ranar ba, kuma Iran ba ta amince da...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce; Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ta Kasar Kan Hukumar IAEA Dole Ne Aiki Da Ita
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar ta dakatar da hadin gwiwa da hukumar IAEA dole ne aiki da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana a wani taron manema labarai cewa: Dole ne hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yi aiki nesa da batun siyasa, yana mai nuni da cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, dole ne yin aiki da ita. Ya ce wannan doka ta tana nuna damuwa da fushin al’ummar Iran ne dangane da hare-haren wuce gona da iri da aka kaiwa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran da kuma kisan gillar da aka yi...
A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
Gabanin fara wasannin ƙasashen Afrika na ƙwallon ƙafa ta mata da hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta shirya a ƙasar Morocco da za a fara a ranar Asabar, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) za ta ƙaddamar da sabon kofin gasar a wani ɓangare na ƙoƙarin ɗaukaka wasan ƙwallon ƙafa na mata a nahiyar Afrika. A ranar Laraba, 02 ga watan Yuli na shekarar 2025 za a ƙaddamar da sabon kofin gasar cin kofin Afrika ta mata a ƙasar Morocco, ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta bana, sabon kofin wani ɓangaren ne na burin shugaban CAF Dr Patrice Motsepe na bunƙasa ƙwallon ƙafa na mata a Afrika. NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke...
Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da wasu larduna masu iyaka da shi da ke kudu maso yammacin kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama tun daga ranar 18 ga watan Yuni, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa, inda lamarin ya fi muni a yankin Rongjiang. Mahukuntan yankin sun raba yankin zuwa kashi bakwai a matsayin wadanda ambaliyar ta fi shafa tare da kwashe mazauna zuwa wasu manyan wurare masu...
Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon kwana guda a wasu sassan jihar. Wannan na zuwa ne bayan wani hargitsi tsakanin jami’an tsaro da wasu ɓata-gari a yankin Kakuri. Wuraren da dokar ta shafa sun haɗa da Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, da Kakuri GRA. Wata sanarwa da Gwamnatin Kaduna ta fitar ta buƙaci mazauna da su kiyaye umarnin wannan doka.
Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar na da mambobi sama da miliyan 100.27, karuwar kusan miliyan 1.09 kan na shekarar 2023. Zuwa karshen 2024 kuma, JKS na da sassa miliyan 5.25 a matakin farko, karuwar 74,000 idan aka kwatanta da shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Rahotanni na cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa. Gwamnatin Nijeriya ce ta sanar da hakan ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris yayin ganawa da da BBC. APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara Ministan ya ce an ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina. A cewarsa, “akwai ƙa’idoji da Gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar. “Saboda haka yanzu ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin Gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,” in ji Ministan. Mohammed Idris ya...
Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa. Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar. Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa. Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus...
Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar. Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin, wacce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe HOTUNA: Sabon shugaban rikon APC APC ya jagoranci taron Majalisar Gudanarwa A baya, Ma’aikatar Lafiya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 606, sannan mutane 5,332 da suka jikkata. Jahangir ya ce hare-haren Isra’ila kan gidan yari na Evin da ke Arewa maso Yammacin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel. “Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” in ji sanarwar. Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin do ya fuskanci shari’a. A wani labarin kuma,...
Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini. Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
Jami’an tsaro sun hana mambobin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar Adwa ta PDP gudanar da taron da suka tsara gudanarwa. A safiyar Litinin din nan ne jami’ai da yawa ne suka kutsa cikin zauren da aka tsara gudanar da taron inda suka bukaci wadanda suka hallara da su watse. Jami’an tsaro da aka jibge a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar. Har zuwa lokacin hada da wannan rahoto, wasu daga cikin ’yan kwamitin amintattun na PDP suna tattaunawa a kan halin da ake ciki. Mun samu rahotannin cewa jami’an sun umurci mambohin su bar ofishin jam’iyar domin ganin ba a gudanar da wani taro a ofishin jam’iyar ba.
Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.
Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da ministan tsaro na kasar Saudiya Yerima Khalid bin Salman, ya kuma kara da cewa HKI ba kasashe abin amincewa ba. Musawi ya ce sojojin JMI a shirye suka su dakile dukkan hare-haren da HKI zata kawo nan gaba. A wani bangare kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasa da kasa ta kuma MDD...
Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta Lebanon ya fadawa Jaridar da The National ta kasar Amurka kan cewa a makon da ya gabata an kama wani shugaban yan kungiyar yan ta’adda ta ISIS a cikin kasar, tare da zarginsa da shiri hare-hare masu yawa a kasar Lebanon. Kafin haka dai a cikin watan da ya gabata wani dan ta’ada ya tarwatsa kansa a cikin wani coci a birnin Damascus babban birnin...
JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI. Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan...
Sojojin HKI sun kai falasdinawa akalla 72 ga shahada a safiyar yau Litinin, daga cikinsu har da yara kanana da kuma wadanda suke jiraran a basu taimakon abinci a cibiyoyinsu a cikin Gazzar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau litinin a Gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa a wurare da dama a gaza. Labarin ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka ji ciwo zuwa asbitin Al-Ahli. Bayan haka yahudawan kai kai hare-hare a yankin Zaitun da kuma kasuwar zawiyya. Labarin ya kara da cewa baba gadaje a Asbitin don haka zaka ga wadanda suka ji ciwon kwance a kasa. Har’ila yau labaran sun bayyana cewa mafi yawan wadanda sojojin yahudawa suka kashe...
Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula. Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile yakin duniya na uku. A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taba dauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da karfin kokarinmu. A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban dan’Adam shi ma yana da tasiri a MDD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban karni, wanda kasashe...
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus. Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano. Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan. Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari. Ya ce, kafafen yada labarai sun...
A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94. Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano. Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina...
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙarshen mako. Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawaki tofa ne ya sanar da haka a safiyar Litinin. A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun amince da yin jana’iza da binne Alhaji Aminu, Ɗantata a Madina, kamar yadda ya bar wasiyya.
Rahotannin da suke fitowa daga Amurkan sun ce, wani mutum mai dauke da bindiga yankin Cotinai dake jihar Idaho ya bude wuta akan ma’aikatan kashe gobara a lokacin da suke kan aikinsu na kashe wutar da ta tashi a dajin Kootenai. Jami’an tafiyar da sha’anin Mulki a yankin ya bayyana cewa; har yanzu ba a yi nasarar kama maharin ba,kuma yana ci gaba da kai wa jami’an tsaro hari, saboda babbar bindiga yake amfani da ita. Bude wuta akan mai uwa da wani a kasar Amurka wata halayya ce wacce ta dade ana fama da ita saboda yaduwar makamai a hannun mutane. Kungiyar da take kare wadanda suka makamai a cikin Amurka tana da karfin tasiri a cikin harkokin siyasar...
Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu ne sannu a hankali zurfinsa yake bayyana. A jiya Lahadi ne matatar man fetur ta Haifa ta sanar da cewa; Wani karamin sashe nata ne zai fara aiki, saboda hare-haren makamai masu linzami na Iran. Matatar man fetur din wacce ake kira da sunan : “BAZAN” ta ce sai zuwa wata Oktoba ne ake sa ran cewa za ta koma aiki baki daya. A ranar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya. Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa. Shin ko me doka ta ce a kan daukar doka a hannu da wasu ‘yan Najeriya su’ke yi? NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don kawo karshen daukar doka a hannu a...
Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka. Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar. Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Sojojin Nijeriya sun kashe wani shugaban ‘yan ta’adda Mai Dada a yankin Maru na jihar Zamfara yayin wani farmaki na musamman. Babban hafsan Soja Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa an kama wasu waɗanda ake zargin suna kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki, tare da aika wasu masu basu bayanai a jihohin Borno, Kaduna da Edo. Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17 Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga A Borno, Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da ƙwato makamai da harsasai da dama, yayin da aka kama wanda ake zargin jigilar kayayyakin ga ‘yan ta’adda a Monguno. An kuma ƙwato bindigogi da harsasai a jihohin Kaduna da Filato,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar 28 ga watan Yuni, 2025, Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yanta, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan ya shafe shekaru 94 a duniya. Ya rasu a birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wanda rasuwarsa ta kasance wani babban giɓi a tarihin ci gaban Najeriya, musamman a fannin tattalin arziƙi da tallafa wa marasa ƙarfi. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Wannan rashi na Dantata babban al’amari ne da ya shafi Najeriya da ma Yammacin Afirka baki ɗaya. Aminu Dantata ya kasance mutum mai tasiri a fannonin kasuwanci, hidimar jama’a, addini da ayyukan jin-ƙai. A wannan zamani da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa...
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu. Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.” Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara...
Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Seyyed Abdurrahim Mousawi ya bayyana cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan kasar Iran ya zo ne duk da kamewa da kai zuciya nesa da Iran take yi, kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa ba na...
Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni. Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar. Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne...
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...