‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan
Published: 26th, April 2025 GMT
‘Yan gudun hijira a Sudan sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su ceto yara da tsofaffi daga mummunan kangin da suka shiga
An gwabza kazamin fada a kusa da birnin El Fasher da ke arewacin Darfur tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka yi ruwan bama-bamai kan birnin da na manyan bindigogi, inda suka kashe fararen hula akalla 35.
Sojojin Sudan sun samu nasarar dakile wadansu daga cikin wadannan hare-hare, amma duk da haka sun janyo hasarar rayukan bil’adama da na dukiya. Sannan sojojin Sundan sun kuma kwace iko da birnin Bara da ke Arewacin Kordofan, kofar Nyala a Kudancin Darfur.
Dakarun kai daukin gaggawa sun yi wa birnin kawanya da nakiyoyi da ramuka da nufin yiwuwar harin farmakin sojojin Sudan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar ‘Yan Sama Jannati Na Shenzhou 19 Za Su Dawo Doron Kasa A Ranar Talata
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp