2025-09-17@23:34:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 112
«zaɓen sabon Fafaroma»:
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba da fifiko kan hadin kai da karfafa jam’iyyar a fadin jihar. Ya ce, “Ina godiya ga daukacin shugabanni da ‘yan jam’iyyar NNPP na Jihar Kuros Riba, ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode muku da kuka karɓe mu, muna matukar farin ciki da shugabancin jam’iyyar a jihar, ina kara baku kwarin guiwa da ku yi aiki tukuru don ganin an samu...
“Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki. Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshikin shugabanci na dimokuraɗiyya. “Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan bukatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna. “...
Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar. Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar. Ya ce sun ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da shugabannin matasa, sannan an ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakokin jihar domin hana miyagu shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata mata mai tabin hankali da ba a iya gano danginta ba, ta haihu a bainar jama’a a cikin kasuwar garin Aarinoye a karamar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa matar ta haihu ne da misalin karfe 5:00;na yammacin ranar Laraba, kuma ta haifi jaririnta namiji lami lafiya ba tare da tallafin unguwar-zoma ba. ‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’ Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda Majiyar ta ce kafin matar ta haihu an saba ganinta daga safiya zuwa daren kowace rana dauke da juna biyu tana yawon tsintar dagwalon abinci da shan...
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaɓen ciyammomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar. Jam’iyyar PDP wadda ke mulki a jihar ta samu nasara a ƙananan hukumomi uku ne kacal, a zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar. Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu Shugaban hukumar, Dokta Michael Odey, ne ya bayyana sakamakon a cibiyar hukumar da ke kan titin Aba Fatakwal, da yammacin ranar Lahadi. Ƙarin bayani na tafe…
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar. A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor. Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata. Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya...
A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas. Hotuna: Bassey Willie
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro. Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra...
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar katin zaɓe ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya. Ya yabawa matakin kafa kwamitin tare da kira ga mambobinsa da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin su tafi su karɓi katin zaɓensu. Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba...
Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano. A ranar Asabar aka gudnar da zaben na cike gurbi a mazabun Majalisar Tarayya da akamaimaita a ranar Asabar a mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike gurbi na Bagwai/Shanono. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da karuwar adadin mutanen daga 288 a ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Kano. A cewarsa, zaben ya fuskanci barazana sakamakon “shigo da ’yan daba da dama daga cikin da wajen jihar” da suka yi yunkurin dagula tsarin zaben, amma an samu nasarar shawo kan lamarin ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro. ...
Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ɗan majalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari/Tsanyawa. Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wasu ’yan siyasa sun yi maguɗi. Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki APC ta lashe zaɓen cike gurbi a Zariya Shugaban jam’iyyar na jihar, Kwamared Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya shaida wa ’yan jarida cewa INEC ta “tauye wa jama’a haƙƙinsu” bayan ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Ya ce zaɓen ya kamata a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 10 da kotun ɗaukaka ƙara ta soke. NNPP ta ce INEC ta ƙwace sakamakon da aka...
An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna. Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba. Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasara A zaɓen da aka gudanar a Zariya, Isa Haruna Ihamo na jam’iyyar APC ne ya samu nasara da ƙuri’u 26,613. Nuhu Sada Abdullahi na jam’iyyar SDP ya zo na biyu da ƙuri’u 5,721, yayin da Mahmud Abdullahi Wappa na PDP ya samu ƙuri’u 5,331. Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a Kano Farfesa Balarabe Abdullahi, wanda ya bayyana sakamakon zaɓen, ya tabbatar da...
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar. Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa. Zaɓen cike gurbin na Babura-Garki ya fara ne da tsauraran matakan tsaro a fadin mazabar. Jami’an tsaro suka kasance a rumfunan zaɓe da wuraren da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya. A daidai ƙarfe 8:30 na safe, jami’an Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) sun isa rumfar Garki-Kofar Fada (003) inda suka fara shirye-shiryen zaɓe. Mr Ibrahim Shehu, jami’in zaɓe a rumfar, ya shaida wa...
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano. Da yake sanar da sakamakon da misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadin nan, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ya bayyana Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 31,472. Garba Gwarmai ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Yusuf Ali Maigado wanda ya samu ƙuri’u 27,931.
Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye. Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba. APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Wakilinmu ya zagaya rumfunan zaɓe, inda ya gane wa idonsa yadda aikin zaɓen ke tafiya a hankali saboda matsalar na’urar tantancewa. Malam Halliru Hamza, ya ce shi ma bai samu damar kaɗa ƙuri’a ba saboda na’urar taƙi ta tantance shi. Ya ƙara da cewa mutane da dama ba su fito ba saboda yadda siyasa ke tafiya ba tare da ci gaba ba, sai tsadar rayuwa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen. Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu. Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano. Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro suna aikin tabbatar da zaman lafiya domin a gudanar da zaɓen cikin lafiya. HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna “Dukkanin mutanen da muka gani suna kawo matsala an kama su, kuma zaɓen yana tafiya lafiya. “Na gamsu sosai da yadda komai ke tafiya. Kayan zaɓe sun isa a kan lokaci,...
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna. A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci. A wata sanarwa da kakaki rundunar,...
Ahmed Maiyaki da Sadiq Mamman Legas a madadin gwamnatin jihar Kaduna sun ce ofishin babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a zai yi nazari kan kalaman da kungiyar hadaka ta ADC ta yi tare da baiwa gwamnatin jihar shawara kan mataki na gaba. Tun da farko a wani taron manema labarai, jam’iyyar African Democratic Congress da hadin gwiwarta sun zargi gwamnatin jihar Kaduna da daukar hayar ‘yan baranda sama da 4000 tare da cire naira miliyan 30 daga asusun kowace karamar hukuma domin kawo cikas ga zaben da ke tafe.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut. A cewarsu, sun aika da koke...
Jam’iyyar ta naɗa Abdulrazaq Abubakar Isah Iko a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, da Adamu Aliyu a matsayin sakataren riƙon ƙwarya har sai an gudanar da sabon zaɓe. ADC ta gargaɗi shugabannin da aka dakatar kada su ci gaba da kiran kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar ko gudanar da harkokinta. Haka kuma ta soke tarukan siyasa da suka shirya, tana mai cewa hakan ya saɓa wa dokar zaɓe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba. “INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin ‘yan siyasa da su bi dokoki da ƙa’idojin zaɓe,” sanarwar ta shaida. Ya buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta matakan zaɓe tare da jiran jadawalin yadda zaɓen zai gudana a hukumance kafin su fara harkokin yaƙin neman zaɓe. Wannan gargaɗin dai na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yadda jama’a suke ayyana goyon bayan tazarcen Shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma...
Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar. A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya ce...
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ya ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Najeriya sun sauke APC daga kan mulki. “Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya zai lalace. “Ƙasar...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta Ya kuma ce sai a ranar 25 ga watan Agusta, 2025 za a fara rajistar ƙuri’a a zahiri. “Za a fara rajistar ƙuri’a ta Intanet a faɗin ƙasa daga ranar 18 ga watan Agusta,” in ji Farfesa Yakubu. “Rajistar ƙuri’ar a zahiri kuma za ta fara daga 25 ga watan Agusta, 2025,”...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC. Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya An bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano,...
A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai. A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam Hafiz Khalid, ya gabatar da cikakken jadawalin ayyukan zaɓen. Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gaskiya a kowane mataki, yana mai bayyana zaɓen a matsayin aikin gama gari da ke buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki. Mahalarta taron sun bayar da shawarwari masu amfani tare da gabatar da muhimman tambayoyi da suka shafi inganta sahihanci da nasarar zaɓen. Wasu daga...
Ya ce biyayyarsa ga doka da oda ya sa ya samu girmamawa daga abokan aikinsa da jama’a gaba ɗaya. Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwansa, abokansa da ma al’ummar masarautar Hardawa da ta Misau. Ya roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, ya kuma sanya shi a Aljanna. LEADERSHIP Hausa ta gano cewa aikin ƙarshe da Makama ya jagoranta a matsayin shugaban BASIEC shi ne zaɓen cike gurbi na shugaban ƙaramar hukumar Shira da mataimakinsa, a ranar 24 ga watan Mayu, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari. Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu bai cancanta ba, amma Buhari bai matsa lamba kan kotun ta sauya hukuncin ba. “A lokacin mutane sun shirya rantsar da ɗan takarar APC a Bayelsa, amma cikin ƙasa da awa guda, kotun ƙoli ta soke nasararsa. Duk da haka Buhari ya karɓi hukuncin,” in ji shi. Ya ce Buhari shugaba ne na gari, wanda duk da bambancin siyasa da ra’ayi, bai taɓa nuna bambanci...
Olumekun ya ƙara da cewa, katunan zaɓe na rijistar da ta gabata ma za su kasance a shirye don karɓa. Ya ce da saura kwanaki 105 zuwa zaɓe, INEC ta san lokaci ya matse, amma tana tabbatar da cewa sabbin masu rijista a jihar Anambra za su samu damar karɓar katunansu kafin zaɓen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100 da aka samu a bara. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati Sanarwar ta ce an yi bitar alkaluman mamatan a bana ne bisa la’akari adadin waɗanda suka kamu kuma ta yi ajalinsu a shekarar 2024. Hukumumar ta ce alkaluman mamatan ya kai kashi 18.9 cikin 100 na...
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya huɗu a Najeriya da aka zaɓa don wannan aikin na tsawon shekaru uku (tare da yiwuwar ƙarin shekaru biyu don sa ido). Sauran su ne Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (Owo) da Babban Asibitin Irrua da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin. Wannan shiri, wanda Gidauniyar Ƙasa da Ƙasa kan Cututtukan Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya (IFAIN) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar...
Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne, suka yanke hukuncin a ranar Alhamis. Sun yi watsi da ƙarar da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar, kan cewar hujjojin da ya gabatar ba su da inganci. Mai Shari’a Garba, ya ce Ighodalo da jam’iyyarsa PDP ba su kawo hujjoji masu ƙarfi da za...
“Mun yi watsi da ƙarar saboda babu ingantacciyar hujja a cikinta. Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke,” in ji Mai Shari’a Garba. Wannan hukunci ya tabbatar da cewa Sanata Okpebholo na jam’iyyar APC ne, halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Edo na shekarar 2024. PDP ta zargi cewa an yi maguɗi a zaɓen, inda ta nemi a soke sakamakon. Amma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi watsi da ƙorafinta, wanda ya sa suka kai ƙarar zuwa Kotun Ƙoli. Da wannan hukunci, an rufe duk wata shari’a da ta shafi zaɓen gwamnan Jihar Edo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015. Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba. Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe. Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da...
Duk da haka, an kashe ɗaya daga cikinsu, sannan sojojin suka lalata wasu gine-gine da ke sansanin. Abin farin ciki, babu wani soja da ya jikkata ko rasa ransa a wannan farmaki, wanda hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa a yaƙin da suke yi da ta’addanci. Sojojin sun ƙwato kayayyaki kamar bindiga AK-47 guda shida, alburusai 90 masu ɗango 7.62mm, da kuma tutar Boko Haram Wannan nasara na daga cikin ci gaban da gwamnatin Nijeriya ke samu wajen fatattakar ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce ba Shugaban Kasa Bola Tinubu kaɗi ne ya sa Muhammadu Buhari ya ci zabensa a shekarar 2015 ba. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Laraba, yayin kaddamar da littafin da mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa kan abubuwan da ya gani a zamanin mulkinsu. Buhari dai ya shugabanci Najeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023. ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II Daga cikin manyan bakin da suka halarci kaddamar da littafin akwai tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Yakubu Gowon da tsohon Mataimakan Shugaban Kasa, Atiku Abubakar...
Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus. Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba. David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Zaman ya gudana ne a harabar tsohon gidan gwamnatin jihar. Hon. Nanloong Daniel, wanda ke wakiltar mazaɓar Mikang wanda kuma tsohon jagoran masu rinjaye ne a majalisar ta tara, ya samu amincewar dukkanin ’yan majalisar 24 don jagorantar su. Daniel shi ɗan jam’iyyar APC ne. Zaɓen nasa ya biyo bayan wani zaman sirri da aka yi tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya. An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP. Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar. “Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun...
Dickson ya goyi bayan buƙatar gudanar da bincike kan jinkirin aiwatar da kasafin yana mai jaddada cewa matsalar ba ta shafi rashin kudi ba tare da kira ga majalisar ta umarci kwamitocin kasafin kudi su gudanar da bincike cikin mako guda su kuma kawo rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa. Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game da sauya sheka. Ya ba da shawarar cewa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje su dunga kada kuri’a a zaben shugaban kasa, kuma ya yi kira a tsaurara dokoki kan kudaden kamfen ciki har samar da hukumar da za ta sa ido kan aiwatar da hukunci. Jega ya yi nadama da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Nijeriya take fuskanta shi ne,...
A nasu ɓangaren, ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi, MURIC, ta gargaɗi APC da Shugaba Tinubu da kada su sauya Shettima a matsayin mataimaki a 2027. Shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce duk wani yunkuri na cire Shettima zai zama matakin da bai dace ba kuma ya kamata a nemi shawara daga manyan masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar kowanne mataki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula. Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a Najeriya. NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato Hakan dai na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani game da zaɓen. Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiya mai rajin kishin APC a Kano mai suna APC Patriotic Volunteers, ta ce shekaru biyun da jam’iyyar NNPP ta shafe tana mulkin jihar nakasu ne da ke nuna tsantsar rashin ƙwarewarta a gwamnatance. A taron da ta gudanar da manema labarai a Kano, ƙungiyar bisa jagorancin shugabanta Alhaji Usman Alhaji (Wazirin Gaya) ta ce nazarin da ta yi wa salon mulkin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar mata da gazawarsa wajen haɓaka ɓangarori masu muhimmanci duk da makudan kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke bata, da kuma kudaden shiga na cikin gida da take samu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya...
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su daina gaggawar shige-da-fice wajen neman tazarce a Zaɓen 2027. ACF ta ce zai fi dacewa gwamnatin Tiinubun ta mayar da hankali wajen ganin ta kyautata rayuwar ’yan Nijeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓensa a 2027, lamarin da ƙungiyar cewa hakan ya yi wuri. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba Ɓarawon waya ya kashe babban jami’in soja da wuƙa a Kaduna Wannan kira dai na kunshe cikin wata sanarwar yi wa musulmi barka da Sallah Babba da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar. Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...
Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta. Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun mutanen da suke kwance a cikinta. Maƙabartar Kuka Bulkiya ta yi iyaka da unguwannin Dala da Madabo da Yalwa da Kwanar Taya da kuma Gwammaja, sa’annan akan kawo gawarwaki hatta daga unguwanni irin su Gwauron Dutse da Ƙulƙul da Dogon Nama da Madigawa da Sanka da Makafin Dala da dai sauran su. Asali dai an sanya mata sunan Bulukiya ne saboda wata bishiyar kuka mai...
Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutane 366 a sakamakon zazzaɓin Lassa da cutar sanƙarau a ƙasar, lamarin da aka bayyana da ƙalubalen kiwon lafiyar ga al’umma sanadin waɗannan cututtuka. Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 18 ga Mayu, 2025, NCDC ta tabbatar da ɓullar cutar zazzaɓin Lassa guda 733 daga mutane 5,118 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin jihohi 18 da ƙananan hukumomi 95. Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa A cikin wannan lokacin, ƙasar ta sami rahoton mutuwar mutane 141 masu nasaba da zazzaɓin Lassa, wanda ke nuna adadin waɗanda suka mutu ya...
Sai dai kwanaki uku kafin zaben mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya ya rushe shugabancin hukumar zaɓen tare da dakatar da su wajen shirya zaɓen. Sai dai duk da hukuncin da kotun ta bayar, hukumar zaɓen ta shirya zaɓe a ranar 26 ga watan Oktoba na shekarar 2024. Sai dai tun a wancan lokacin jam’iyyar APC ta yi fatali da zaɓen, inda ta bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba sakamakon saɓawa hukuncin kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa. “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da ma’aikatan hukumar suka halarta a sassa daban-daban na duniya a kan AI inda ƙasashen Afirka da dama suka tattauna domin rungumar sabuwar basirar ta hanyar yin amfani da ita a inda ya dace da kuma maganin yin amfani da ita wajen kawo cikas a zaɓe musamman yaɗa labarun ƙarya a lokutan zaɓe da sauransu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zaɓin ya haɗa har da na yin zaɓe ko ƙaurace masa? Mene ne matsayin tsarin dimokuraɗiyya idan aka wajabta wa al’umma kaɗa ƙuri’a? NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba. Domin sauke shirin latsa nan
Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan. Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar. Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Shin ko hakan zai kawo ƙarshen matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan faɗuwa zaɓen 2023? Daga cikin matsalolin da suka kunno kai a cikin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP tun bayan faduwarta zaɓe a 2023 shi ne yin baram-baram a kan yadda za ta dinke barakar da aka samu a lokacin zaben fidda-gwani da rikicin shugabanci a matakai daban-daban da kuma kasa tsayawa da kafarta domin samar...
Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar Babangida a littafinsa mai suna “A Journey in Service” ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe Zaɓen 12 ga watan Yunin 1993. Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’ Alhaji Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu. Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar. Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar. Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi. Gwamnan ya yi addu’ar...
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis. Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya. Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane Robert Prevost zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV). Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.
Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar mai mambobi 630. Kafin zama shugaban gwamnati ana buƙatar kuri’u 316 kuma jam’iyyar CDU/CSU da kuma jam’iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake buƙata. Merz zai maye gurbin Olaf Scholz wanda ya faɗi zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu Upon announcing the second vote, the head of the Union bloc in parliament, Jens Spahn, said, “The whole of...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zazzaɓin cizon sauro, wato maleriya, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma haɗari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya. Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta maleriya kan sake kamuwa da ita bayan ya warke. Ko me ya sa magungunan zazzaɓin cizon sauro suka daina aiki a jikin mutane? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa Wannan batu shirin Najeriya A Yau zai duba yayin da ake bikin Ranar Malaria ta Duniya. Domin sauke shirin,...
A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi. Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu...
Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
Da alama tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana nema karbe kambun ɗaukaka da ’yan siyasa a baya suka riƙa bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar nan biyu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obansanjo, wajen neman tabarrakinsu musamman a lokacin da zabe ya karato a kasar nan. Buharin wanda ya mulki kasar nan a tafarkin soja da kuma na farin hula daga bayabayan nan, a yanzu haka tauraronsa na haskawa, kuma yana ƙamshin turaren Ɗan goma, inda jiga-jigan ’yan siyasa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da SDP da kuma jam’iyyarsa mai mulki ta APC, suke nikar gari takanas zuwa gidansa da ke birnin Kaduna, tare da nuna irin kyakkyawan kusancinsa da su. Hakan dai na zuwa ne...
Jam’iyyar adawa ta SDP buƙaci Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin siyasa a Najeriya su dai shagala da batun zaɓen 2027, su mayar da hankalinsu wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara mayar da ƙasar tamkar filin kisa. SDP ta bayyana cewa kashe-kashe ɗaruruwan mutane da ke faruwa a faɗin ƙasar nan – Arewa da Kudu – musamman a makonnin da suka gabata, na da matuƙar tayar da hankali. Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na SDP, Araba Rufus Aiyenigba, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a, cewa abubuwan takaicin sun hada da da kisan mafarautan Jihar Kano a jihar Delta, baya ga ayyukan ’yan ta’adda da hare-haren da a ka yi wa mutane sama da 100...
Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...
Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990. Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin a ranar Talata, yana mai cewa babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da an bayyana wa jama’a ba. ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar A watan Yunin 2023 ce wani Ba’Amurke, Aaron Greenspan, a ƙarƙashin dokar ’yancin fitar da bayanai (FOAI) ya miƙa buƙatar a ofishin zartarwa...
Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027. Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe. Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ne ke yaɗa wannan jita-jitar don tayar da ƙura. “Wannan jita-jita ce kawai marar tushe. Maganganu ne da bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa, “Ko da a ce akwai wani dalili da zai sa shugaban ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan...
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe mulki daga hannun jam’iyya mai ci. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati Da yake jawabi ga manema labarai tare da wasu ’yan adawa a zauren taro na ‘Yar’adua Center da ke Abuja a ranar Alhamis, Atiku ya ce an yi taron ne don sake samar da wasu ‘yan adawa kafin babban...
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Taron ya gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, sai dai ba a bayyana manufar taron ba. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi. Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed sun tattauna wasu batutuwa da suka shafi babban zaɓen 2027 da kuma makomar siyasarsu. Wannan ganawa ta wakana ne a daidai lokacin da ’yan siyasa...
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, na ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi. Taron na gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, amma ba a bayyana manufarsa ba tukuna. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Obi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi. Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed za su yi magana da ’yan jarida bayan kammala ganawar tasu. Wannan ganawa na faruwa ne a daidai lokacin da ’yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027....
Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’. Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Ya ce Janar Abacha ne, ya ke da alhakin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga wata Yunin 1993. “Duk wani yunƙuri na ɗora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaɓen, wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin...
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Neja ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi. Shugaban Hukumar Zaɓen, Mohammed Jibrin Iman ne ya bayyana haka a lokacin da yake ƙaddamar da jadawalin ayyukan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025 a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin jihar. Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata Imam ya ce an fara shirye-shiryen zaɓen ne daga ranar 6 ga watan Maris, 2025, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ne tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Maris, 2025, yayin da za a tattara fom da kuma jerin...
Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe. Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari. An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa Ya yi nuni da juyin mulkin baya-bayan nan da aka yi a Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar, a matsayin alamu karara...
Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin. Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.
Jam’iyyar PDP mai ci a Jihar Osun ta lashe zaɓen dukkan kujerun ƙananan hukumomi jihar guda 30 da na kansiloli 332 da aka gudanar yau Asabar. Shugaban hukumar zaɓen jihar OSSIEC, Hashim Abioye ne ya sanar da sakamakon a wani taron ganawa da manema labarai da ya yi a jihar. Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Da yake jawabi a yammacin wannan Asabar ɗin a birnin Osogbo, Hashim Abioye ya ce an samu nasarar gudanar da zaɓen bisa duk wasu tsare-tsare da dokoki suka tanadar. Ya bayyana cewa jam’iyyu 18 ne suka shiga zaɓen domin cike giɓin da ake da shi a madafan iko na ƙananan hukumomin...
Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba. Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun Da yake jawabi...
Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu. A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci. Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa “Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima. “A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai...
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara. Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin yin sabon zaɓen ƙananan hukumomi. Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Ministan ya ce kotu ta dawo da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa a ƙarƙashin tsohon Gwamna Gboyega Oyetola, amma ta tsige su ta hanyar umarnin zartarwa da gwamnan...
Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993. Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban. Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram Babangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’. Yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ke nazarin littafin, Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar...
Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin zaɓe da ya binciki Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC dangane da jinkirin da take yi na gudanar da zaɓen cike giɓin wasu kujerun ’yan majalisar tarayya da na jihohi. Majalisar a wannan Talatar ta kuma bayyana cewa jazaman ne kwamitin ya gayyaci Hukumar INEC domin ta bayar da dalilai kan tsaikon da aka samu da kuma yadda take ƙoƙarin yi wa tufkar hanci. Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Da wahala City ta yi nasara a gidan Madrid — Guardiola Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta buƙaci kwamitin ya sauke wannan nauyi tare da miƙa mata rahoton bincikensa nan da makonni huɗu. Wannan dai na zuwa ne bayan ƙorafin da wani...
Ƙungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa ta Ƙasa (IPAC), reshen Jihar Katsina, ta bayyana amincewarta da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Laminu Lawal Boyi, ya bayyana cewa IPAC ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da bai wa dukkanin jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen. Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan sanda a Ondo NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya “Baya ga shugabancina a IPAC, ni kuma shugaban jam’iyyar Accord ne, wacce ta shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 34 da kujerun kansiloli 361 a faɗin jihar. “A matsayina na ɗan takara kuma mai ruwa da tsaki, na...