Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Published: 28th, April 2025 GMT
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza
Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza.
A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba amma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri.
Ta bayyana cewa kin bari a shigar da kayayyakin jin kai na yankunan Falasdinawa tun daga ranar 2 ga watan Maris ya kara ta’azzara wahalhalun jin kai a Gaza, tana mai bayanin cewa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na kokarin samar da muhimman abubuwan da ake bukata domin ci gaba da rayuwar al’ummar Falasdinu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya yankunan Falasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
A yau ne aka bude taron tattaunawa game da wayewar kai takanin Sin da kasashen Larabawa karo na 11, wanda sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin da sakatariyar kawancen kasashen Larabawa suka dauki nauyin shiryawa a Beijing.
A gun taron, shugabanni na jam’iyyu da kungiyoyin siyasa, ‘yan majalisa, jami’an gwamnati, da wakilan masana da kafofin watsa labarai daga Sin da kasashen Larabawa guda 22 sun hallara don inganta ilmantarwa da fahimtar juna kan wayewar kai da kuma zurfafa hadin gwiwar abokantaka.
A wannan taron kuma, Sin da kasashen Larabawa za su mayar da hankali kan batutuwa kamar “Musayar darussan mulkin kasa da binciken hanyoyin zamanantarwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa”, da “Shawarwarin wayewar kan duniya da hadin gwiwar al’adu na Sin da kasashen Larabawa”, da kuma “Shawarar ziri daya da hanya daya da hadin kan jama’a tsakanin Sin da kasashen Larabawa”, kana za su shiga tattaunawa da musayar ra’ayoyi masu zurfi.(Safiyah Ma)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA