2025-08-01@01:20:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 213
«Bana mai ɗan wake»:
Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin....
Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external) Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external) Crystal Palace ta sanar...
Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya. Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai. Tinubu...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba. Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali...
Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA). Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau...
Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA). Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau...
Wasu yankuna a Jihar Legas, na iya fuskantar rashin wuta na tsawon kwanaki 25, yayin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), zai fara gyaran layin lantarkin Omotosho zuwa Ikeja ta Yamma mai ƙarfin 330kV. A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, aikin zai gudana kowace rana...
Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta bayar ta yanke wa fitaccen ɗan Tiktok, Al-Ameen G-Fresh da mawaƙi Hamisu Breaker, hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan yari bayan samun su da laifin wulaƙanta takardun Naira. Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukunci, inda ya yi musu ɗaurin wata biyar a gidan yari,...
Shahararren ɗan kokawa ɗan ƙasar Amurka mai ritaya Terry Gene Bollea wanda aka fi sani da Hulk Hogan ya rasu yana da shekara 71 a duniya. A cewar TMZ da sauran rahotanni, likitoci sun mayar da martani a gidansa na Clearwater, da ke Florida da sanyin safiyar Alhamis kan Hulk Hogan ya kamu da bugun...
An wajabta wa ɗaliban makarantun firamare da Ƙaramar Sakandare mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a Jihar Bauchi. Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko ta jihar (SUBEB) ce ta bayar da umarnin ta hannun shugabanta, Alhaji Adamu Mohammed Duguri. Ya bayyana cewa mallakar lambar NIN ta zama tilas lura da duk hukumomin...
Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna. Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu...
Sojoji sun kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ɗauke da tsabar kuɗi Naira miliyan 13 a kan hanyar Kaduna zuwa Jos a Jihar Kaduna. Dakarun Rundunar Operation Safe Haven sun kuma ƙwace bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da harsasai 30 a hannun ɗan ta’addan a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna. Kakakin rundunar, Manjo...
Sojoji sun kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ɗauke da tsabar kuɗi Naira miliyan 13 a kan hanyar Kaduna zuwa Jos a Jihar Kaduna. Dakarun Rundunar Operation Safe Haven sun kuma ƙwace bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da harsasai 30 a hannun ɗan ta’addan a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna. Kakakin rundunar, Manjo...
Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada...

Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta: Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyarwa A Makarantun Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ƙaddama da shirin na nuni da ƙwazon gwamnatinsa na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da dabaru daban-daban na ƙara yawan ɗalibai a makarantun jihar Zamfara. Ya ci gaba da cewa, “Alƙawarinmu na yin garambawul ya haɗa da tsare-tsare na yaƙi da...
Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada...
Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu...

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A CPC, Haruna Sa’eed Kajuru, Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kisan ‘Yan Zariya A Filato
Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan. Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin...
Ɗan wasan gaban Napoli, Victor Osimhen, ya amince da komawa Galatasaray na dindindin, wani ɗan jarida a Nijeriya kuma makusancin Osimhen, Buchi Laba ne ya bayyana hakan. Ya ce “Osimhen ya bayyana cewa yana son komawa Galatasaray daga Napoli, duk da cewar ƙungiyar ta ƙasar Italiya na fatan ci gaba da kasancewa da tsohon ɗan...
Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai...
Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ADC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Sabuwar haɗakar ta haɗa da fitattun ’yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci Majalisar Dattawa da ta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya. A watan Maris, Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio. Kotu ta ci tarar Natasha N5m saboda...
Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun...
Rahotanni na cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa. Gwamnatin Nijeriya ce ta sanar da hakan ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris yayin ganawa da da BBC. APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje An kashe ubangidan...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, sun roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su kai musu ɗauki kan barazanar da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ke musu. A farkon makon nan ne aka samu labarin cewa Bello Turji ya bai wa mazauna wasu yankuna a Isa wa’adin gina masa...
Mahaifin angon da ’yan uwan angon na jini da danginsa na daga cikin mutane 13 da aka yi wa kisan gilla a hanyar ɗaurin auren ango, inda aka ƙona gawarwarkin wasunsu a cikin motar da ta ɗauko su, a yankin Mangun da ke ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mahaifiyar angon, Malama Faji Sani da...
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ziyarci iyalan ’yan ɗaurin aure da aka kashe a Jihar Filato. Tun da farko, Hakimin Basawa, Haruna Abubakar ne, ya wakilci Sarkin lokacin da lamarin ya faru, saboda Sarkin ya yi tafiya. Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe Ganduje ya yi murabus...
Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno. Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar...
Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai. Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata. Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum...
Arsenal na fatan sayen ɗan ƙwallon Brentford, Christian Norgaard, da zai maye gurbin Thomas Partey. Wasu majiya na cewa farashin da Arsenal za ta ɗauki ɗan wasan na tawagar Denmark mai shekara 31, zai kai £10m da karin £5m idan ya taka rawar gani da karin tsarabe-tsarabe. Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da...
Leeds United ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan ƙungiyar Udinese na ƙasar Slovenia, Jaka Bijol mai shekaru 26 kan farashin fam miliyan 15. Wannan dai shi ne sabon ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta ɗauka bayan zuwan ɗan wasan gaban Jamus, Lukas Nmecha, kyauta. ‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta...
Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin...
Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da...
Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da...
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna baƙin cikinsa kan kisan wasu matafiya daga Jihar Kaduna da aka yi a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Matafiyan sun fito ne daga Zariya suna kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, yayin da wasu ɓata-gari suka farmake su. HOTUNA: Yadda aka...
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan matafiyan da aka kashe a garin Mangu na Jihar Filato, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure. A yayin isar da saƙon a ƙauyen DanBami da ke Anguwar Rimi, a Ƙaramar Hukumar Kudan, Gwamnan ya roƙi Allah Ya gafarta wa...
Mahaifin ango da ƙanin ango na daga cikin mutanen da aka kashe lokacin da wasu suka kai musu hari a Jihar Filato. Rahotanni sun nuna cewa mutum 31 ne ke cikin wata babbar mota mai ɗaukar fasinja 18 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), yayin da aka kai musu hari. Ɗan ƙunar baƙin wake ya...
An yi wa wasu matafiya ɗaurin aure 12 kisan gilla bayan wasu mutane sun kai musu hari a yankin Mangu ta Jihar Filato sun kai musu hari. Rahotanni sun bayyana cewa mutum 11 daga cikin matafiya suna samun kulawa a asibiti, bayan raunukan da suka samu a harin da aka kai musu a yankin Ƙaramar...
Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao,...
An samu rahoton cewa guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic), Idah a Jihar Kogi, inda ta ɓarnata kadarori da gine-gine da dama. Rahoton na cewa, wata mummunar guguwar ruwan sama da ta biyo bayan ruwan sama da aka kwashe tsawon sa’o’i ana yi a ranar Laraba...
Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki...
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum bakwai hukuncin ɗauri, bayan da suka ji wa wani ɗan sanda rauni yayin da ake ƙoƙarin cafke su. Al’ummar unguwannin Tudun Maliki da Sheka ne suka kai rahoton mutanen, inda suka zarge su da sayar da miyagun ƙwayoyi. ’Yan...
Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A. Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe. Rikicin...
Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin...
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen...
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen...
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen mutanen da ake yi a Jihar Benuwe, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunar masifa. Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya caccakin gwamnatin Nijeriya da cewa ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan lamarin. Tinubu ya...
Wani jami’in ɗan sanda, SP Mustapha Garba Gumau, ya yi gamo ajalinsa a wani hatsarin mota yayin da ya rage aƙalla sa’a ɗaya a ɗaura masa aure. Aminiya ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin jami’in ne a kan hanyar Gumau zuwa Magaman-Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda za a ɗaura...