Na shiga fim ne don isar da saƙon Musulunci — Malam Inuwa Ilyasu
Published: 26th, April 2025 GMT
A wannan makon Aminiya ta samu tattaunawa da shahararren jarumi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannyood, Malam Inuwa Ilyasu, wanda ya shafe sama da shekara 40 yana harkar wasan kwaikwayo. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Gabatar da kanka?
To da farko dai sunana Inuwa Ilyasu.
Yaushe ka fara harkar fim?
Gaskiya dai kusan da ni aka fara yin fim kuma lokacin da muka fara yi, mun fara da yin tunanin ya za mu yi saboda kafin nan ai akwai wasan daɓe da muka fara yi.
A wancan lokaci muna faɗakarwa ta wasan kwaikwayo kusan tun wajejen 1970. Daga nan muka fara tunanin ta yaya za mu yi ƙoƙarin mu ma mu fara yin irin namu.
Yawancin fina-finanka kana fitowa ne a matsayin malami, kana faɗakarwa ko bayar da shawara a addinance. Wannan matsayin kai kake zaɓa ko kuwa masu shirya fim ne suke ba ka?
A’a ba ni na zaɓar wa kaina ba.
Idan na fahimce ka, an duba cancanta da kuma wanda aka gani zai iya bayar da abin da ake so ake ɗora ka a kai?
Yauwa, ana yin sa’a ce dai za ni ce ta tarar da mu je, domin ni daman dalilina na yin wasan kwaikwayo shi ne, saboda in samu in cusa aƙida ta addinin Musulunci da tarbiyartarwarsa da kuma cusa al’adarmu da ɗabi’unmu ga matasa masu tasowa. Misali, ai ka ga irin yadda wasu masu fim ɗin Indiya suke cin karensu babu babbaka.
Daga lokacin da ka fara wasan daɓe zuwa yadda ka juya zua yin fim, shin kana ga saƙonnin da kake son isar wa jama’a suna tasiri wajen faɗakarwa ?
Alhamdulillahi, ana samun nasara Insha Allahu, saboda mutane da yawa in na haɗu da su ko kuma ma wasu su ne za su neme ni, su yi yabo saboda Allah Ya sa sun ci karo da wata faɗakarwa da na yi a wani shirin da ta yi tasiri matuƙar gaske ga rayuwarsu.
Ka shafe sama da shekara 40 a sana’ar harkar fim, ko kai ma ka fara tunanin kafa wani kamfani da idan ka yi fim za ka riƙa ɗorawa a manhajar Youtube kamar yadda wasunku ke yi halin yanzu?
To ni irin wannan ba ya cikin tunanina. Kamar yadda na gaya maka a baya, mun fara yi ne da manufa, kuma muna yi ne domin faɗakarwa ga jama’a a ƙarƙashin ƙungiya da na faɗa mai suna “Dabo”. Haka kuma mun samu nasara, domin wasu daga cikin waɗanda suke a Kannywood ɗin cewa suke yi daga kallon fim ɗin da muke yi, suka koya. Wasu kuma daga irin faɗakarwar da ake yi a fim ta ba su sha’awa har su ma suka shigo matsayin masu yin fim. Wani kuma zai ce shi fim ya kalla, ya sa masa soyayyar abin a zuciyarsa, Alhamdulillahi an samu ci gaba sosai da nasara.
Kamar ta wace gaɓa nasarorin da aka samu?
Gaɓoɓin da dama, saboda za ka samu wasannin da muka yi, wasu suka kalla za su ɗauki darasin rayuwa, sannan muna harkar arziki da jama’a, ana ta nuna mana soyayya ba wata matsala. Sannan idan ma suna muke so mu samu, mun samu. Kai wasu ma na raɓe da mu, sun samu sannan akwai da dama da suke son su samu dama kamar yadda muka samu, amma ba su samu ba.
Wato dai fim ɗin duk da ka fito rawar da kake takawa da aka ba ka ana amfana da ita a kan duk abin da ka faɗakar ko ka a addinance ko a al’adance?
Eh, an samu ci-gaba sosai kuma Alhamdulillahi.
Ya kake kallon ƙalubalen da ake samu a tsakanin masu harkar fim?
Ban fahimce ka ba.
Irin ’yan matsaloli da ka taso tsakanin mawaƙa ko masu yin fim na baya-bayan nan da ake zargin su da wuce gona da iri?
Irin waɗannan abubuwan gaskiya muna ta yaƙin su a matsayinmu na dattawa. Amma ka san ɗan-adam sai da hikima.
Wace shawara kake da ita ga Masana’antar Kannywood da kuma masu nufin nan gaba su shigo ta, lura da cewa yanzu ka zama uba a cikinta tun daga kan hukuma da kuma jarumai?
Eh to akwai buƙatar sake duba inda hukuma za ta shigo ta gyara a cikin harkar, domin muna magana ne a kan addini da tarbiyya, musamman ta Musulmi. Ya kamata a ce gwamnati da ta kafa wannan hukuma ta tallafi to kuma ta duba hanyar da za ta tallafa wa wannan harkar saboda harkar fim tana bayar da dama ga matasa ta samun sana’a. Haka kuma tana hana zaman kashe wando. Sannan kuma ana amfani da fim wajen kawar da wasu miyagun abubuwa da suke faruwa a cikin al’umma, ta yadda ba sai an fito, ana kokawa ko kama mutane ba don yin gyaran. Saboda mu ƙalubale gare mu, mu tabbatar masu kallo za su gamsu da abin da muke yi kuma su faɗaka.
Ban sani ba ko akwai wani saƙo da kake son ka isar?
Saƙona shi ne, kowa lallai yana da buƙatar ya sanya hannu wajen tallafa wa wannan harka ta fim, saboda ta shafe shi a abin da ya shafi addininsa da al’adarsa. Don haka ya kamata kowa ya duba ta ina zai taimaka yadda za ta inganta, ta dace da waɗannan muhimman abubuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kannywood kwaikwayo
এছাড়াও পড়ুন:
An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal
An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai.
A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita.
Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a ChibokKafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu.
Wata sanarwa da hukumar samar da wutar lantarki a Spain ta Red Electrica ta fitar, ta ce da misalin ƙarfe 7 na safiya agogon ƙasar, an samu nasarar dawo da sama da kashi 99 na wutar lantarki a ƙasar.
Haka nan ita ma takwararta ta Portugal ta ce tun cikin daren jiya Litinin, aka dawo da wutar lantarkin da dukkanin tashoshin wutar ƙasar guda 89.
Bayan ɗauke wutar da aka samu a Spain, jami’an ba da agajin gaggawa sun sanar da nasarar kuɓutar da mutane dubu 35 da suka maƙale a jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.
Har yanzu dai hukumomi ba su bayyana dalilin da ya sa aka samu ɗaukewar wutar lantarkin ba, wanda shi ne karo na biyu da irin wannan mummunar katsewar wutar lantarki ta faru a Turai cikin watanni