Falasdinawa 39 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’o’I 24
Published: 27th, April 2025 GMT
A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 39 sanadiyyar hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamaya su ka kai a sassa mabanbanta na zirin Gaza.
A birnin Khan-Yunsu Falasdinawa 3 sun yi shahada, daga cikinsu da akwai karamin yaro, yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Majiyar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta ambaci cewa, wani masunci ya yi shahada saboda harin da ‘yan sahayoniya su ka kai masa a gabar ruwan garin Khan-Yunus.
A wani labarin daga yankin na Gaza, sojojin HKI suna ci gaba da rusa gidajen fararen hula a arewacin birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza.
Tun da HKI ta sake komawa yaki gadan-gadan akan al’ummar Falasdinu a ranar 18 ga watan Maris, Falasdinawa 2,111 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 5,483 su ka jikkata.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza da ta fitar da wannan kididdigar ta kuma bayyana cewa; tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu jumillar Falasdinawan da su ka yi shahada, sun kai 51,495 wadanda kuma su ka jikkata sun kai 117,524.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama.
A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar da kisan kare dangi kai tsaye a tauraron dan Adam a Zirin Gaza.
Ta kara da cewa, “Sun ga kasashe kamar babu abin da zasu iya saboda da rauni” tare da nuna cewa “gwamnatin mamayar Isra’ila na kashe dubban Falasdinawa maza da mata, ta hanyar kisan kiyashi kan dukkanin iyalai da suka hada da kananan yara, da lalata gidaje, rusa cibiyoyin tsare rayuka, rusa asibitoci da cibiyoyin ilimi.