Jihohi Sun Samu Naira Tiriliyan 1 Na Kudaden Kananan Hukumomi A Zango Na Daya
Published: 26th, April 2025 GMT
A watan Janairu, kwamitin ya raba naira tiriliyan 1.703 tare ga gwamnatoin tarayya da jihohi da kananan hukumomi. A wannan kudade, gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 552.59, jihohi sun karbi naira biliyan 590.61, yayin da kuma kananan hukumomi sun karbi naira biliyan 434.57.
Rabon kudaden ya dogara ne kan kudaden shiga na naira biliyan 749.
Rabon watan Fabrairu ya kai naira biliyan 1.678, inda gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 569.66, jihohi sun karbi naira biliyan 562.20, sannan kuma kananan hukumomi sun sami naira biliyan 410.56.
Kudaden shiga sun hada da naira biliyan 827.63 na kudaden shiga na doka da naira biliyan 609.43 daga VAT da naira biliyan 35.17 daga EMTL da naira biliyan 28.22 daga ma’adanai da karin naira biliyan 178.
A watan Maris, kwamitin ya raba naira tiriliyan 1.578. Gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 528.70, jihohi sun karbi naira biliyan 530.45, sannan kuma kananan hukumomi sun karbi naira biliyan 387.
Kudaden shiga da aka rarraba sun hada da naira biliyan 931.33 a cikin kudaden shiga na doka da naira biliyan 593.75 daga harajin BAT da naira biliyan 24.97 daga EMTL, da naira biliyan 28.71 daga musayar kudade.
Kudaden shiga daga VAT a watan Janairun 2025 ya kai na naira biliyan 771.89, ya ragu zuwa naira biliyan 654.46 a watan Fabrairu da naira biliyan 637.62 a Maris. A halin yanzu, kudaden shiga na doka ya karu daga naira tiriliyan 1.848 a watan Janairu zuwa naira tiriliyan 1.653 a watan Fabrairu da naira tiriliyan 1.718 a watan Maris.
Duk da wadannan karin kudaden shiga, har yanzu kananan hukumomi ba su fara amsar kudadensu kai tsaye ba daga asusun tarayya, sabanin umarnin kotun koli da ta bayar a watan Yulin 2024.
Kotun koli ta ba da umarnin a biya kudaden kananan hukumomi daga asusun tarayya kai tsaye don tabbatar da ‘yancin cin gashin kansu na kudi da kuma kare su daga tsoma baki daga gwamnatocin jihohi.
Kungiyar kananan hukumomi ta Nijeriya (ALGON) ta zargi ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da kawo cikas ga aiwatar da ‘yancin cin gashin kai na kananan hukumomi, duk da cewa kotun koli ta yanke hukunci kan bayar da kudaden kai tsaye ga dukkan kananan hukumomi 774 da ke kasar nan.
ALGON ta kuma dauki matakin shari’a a kan babban lauyan gwamnatin tarayya da wasu cibiyoyin tarayya da dama a karar mai lamba ta FHC/ABJ/05/353/2025, suna nemanbai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin sarrafa kudadensu da kansu.
Karar ta kuma hada har ministan kudi, Wale Edun da ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Abubakar Bagudu da akanta janar na tarayya da CBN da NNPCL da kuma bankunan kasuwanci a matsayin wadanda ake tuhuma.
ALGON ta ce ta dauki wannan matsayin a kotu ne da nufin ba kawai tilasta ‘yancin gashin kai a takarda ba har ma da tabbatar da aiwatar da shi.
Shari’ar wacce da farko aka shirya yi a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, amma kotun ba ta samu zama ba. An dage shari’ar zuwa ranar 29 ga Mayu, 2025.
Da yake mayar da martani, Sakatare Janar na ALGON, Mohammed Abubakar, ya nuna takaicinsa kan ci gaba da jinkirin biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye duk da hukuncin kotun koli.
Abubakar ya ce lamarin ya zama mai rikitarwa kuma yawancin ‘yan Nijeriya sun yi takaicin faruwar hakan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: sun karbi naira biliyan naira tiriliyan 1 gwamnatin tarayya da naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.
Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 100 a duniya, yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani.
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniyaA cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.
Bayanai sun nuna fitaccen malamin yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alkur’anin.
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa shehin malamin rasuwa a Bauchi.
Yana daga cikin Halifofin Sheikh InyassSheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.
Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.
A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.
“To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.
“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.
“Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.
“An haife ni ne a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira, a ranar Laraba.”
‘Yadda na mayar da karatun Alkur’ani sana’ata’Ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.
“A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karatun Alkur’ani da karanta Salatul Fatihi da tasbihi da istigfari da salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori,” in ji shi.
Kwarewar Sheikh Dahiru BauchiDa aka tambaye shi kan fannonin ilimin da ya fi kwarewa, shehin malamin ya ce, “Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Alkur’ani kuma ta hannunsa ne na karbi Darikar Tijjaniya.
“Shi mahaifina ya karbi Darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba, daga baya sai mahaifina ya ba ni izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Alkur’ani mai girma.
“Bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkur’ani, daga nan kuma sai bangaren Tafsiri, a nan malaman Tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su.
“Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiran sa Tlimin Tarbiyya.
“A nan ma masu irin ilimin kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare.
“Sauran ilimomi kuma ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu, duk ina tattabawa,” inji shi.
‘Dalilin da nake buga misali kan duk tambayar da aka yi min’Da aka tambayarsa cewa jama’a na mamakin yadda idan aka yi masa tambaya sai ya ba da misali kafin ya bayar da gundarin amsar, sai ya ce, “Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane.
“Idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su.
“Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa.”
Shehin malamin ya zama masanin Tafsirin Alkur’ani Mai Girma wanda ya samu lambobin yabo a wannan bangaren.
Ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori daban-daban a Najeriya da ma kasashen waje.
Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi lambar yabo ta Digirin girmamawa, sannan Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR.
Nasarorin Sheikh Dahiru BauchiGa wasu daga cikin nasarorin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekarunsa:
Ya musuluntar da dubban mutane A duk lokaci bayan lokaci yakan karanta Alkur’ani kuma yana yin saukar Alkur’ani a kwana biyu Ya ba da lazumin Darikar Tijjaniyya wa dubban mutane da dama a fadin duniya Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1500 a Najeriya da sassan Afirka Sama da mutum 140,924 sun haddace Alkur’ani a makarantunsa a fadin Najeriya Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya Mutum ne mai kishin kasarsa Najeriya wanda aduk lokacin da ya bude baki zai yi addu’a sai ya roki Allah Ya ba kasar zaman lafiya da kwanciyar hankaliBugu da kari, malamin yana cikin wadanda suka fi kowa dadewa suna tafisirin Alkur’ani da watan azumin Ramadan.
Masallacin da yake tafsirin da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna, na daya daga cikin manyan masallatan da ke cikin garin, kuma za a iya cewa a tsawon shekaru, malamin yakan zauna a garin kusan fiye da a ko ina.
Wani bincike da wani wanda yayi Nazari kan rayuwar malamin ya kuma rubuta littafi a kansa mai suna Shehu Dahiru Bauchi Ginin Allah, shekaru uku da suka wuce, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, ya ce
Daya daga cikin almajiran shehin, Mallam Ahmad Tijjani Kolo, ya ce a yanzu an sami karin mahaddata a cikin zuri’arsa, inda yanzu suka doshi 300. Ya ce da wahala a sami mai irin wannan a tarihi.
Shugaban Kungiyar Daliban Sheikh Dahiru Bauchi, Mallam Ibrahim Imam Ismaila, ya ce a tarihi babu wanda ya taba samun irin baiwarsa.
‘Rayuwarsa gaba daya makaranta ce’Shi kuwa Daraktan Wakafi a Hukumar Shari’a na Jihar Bauchi, Mallam Ahmad Tijjani Sa’id, ya ce rayuwar shehun malamin gaba dayanta makaranta ce.
Ya kuma ce malamin ya yi tafiya daga Arewa har kasashen Kudu a kan jaki da doki don yada addinin.
Sannan ya yi tafiya a kan keke zuwa kauyuka da dama kamar Tafawa Balewa da yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma don yada addinin Musulunci.
‘Gidajensa 1,000 da ake zama kyauta’Malam Ahmad Tijjani Sa’id ya ci gaba da cewa babu abin mamaki cikin sha’anin malamin kamar yadda yake daukar nauyi ba tare da jin tsoron hidima ba.
“Yana da gidaje fiye da dubu daya a fadin kasar nan, amma ba inda ake haya, bayin Allah masu neman ilimi yake zubawa a ciki kyauta.
“Jama’ar da yake ciyarwa Allah kadai Ya san adadinsu. A kullum idan Shehi zai fito zai sallami baki fiye da 3,000 da suka zo ziyarar sa daga ciki da wajen Najeriya, kuma za ka samu dalibansa ya yi musu auren fari ya musu suna kuma bai gaji ba.
“Ya maka mace ta biyu ya dauki nauyinku. Ire-iren wadannan halaye na Shehi da wuya ka samu wanda zai iya yin haka.”