Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya
Published: 26th, April 2025 GMT
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba.
Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba a matsayin masu koyarwa a ayyukan aikin hajjin bana.
Ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin yada labarai domin yada ayyukan aikin hajjin tare da ba da kulawa ta musaman kan shawarwarin da aka bayar kan rahoton da kwamitin aiki hajjin ya gabatar.
Da yake gabatar da rahoton, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj, Alhaji Tukur, ya bayyana wasu muhimman batutuwa da ke bukatar kulawa.
Ya kuma bayyana bukatar tallafa wa hukumar kula jin dadin alhazai wurin tantance malamai. Yana mai cewa mafi yawancin shugabannin kananan hukumomi sun sanya malaman da ba su da kwarewar yadda za su koyar da mahajjatan.
Amirul Hajja ya nuna damuwarsa bisa yadda ake samu wadanda ba ‘yan Nijeriya ba a cikin mahajjatan jihar tare da ba da shawarar inganta hanyoyin da ake bi wurin tantance mahajjatan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya
Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan PDP guda biyu da ‘yan majalisar wakilai guda bakwai daga PDP.
Tun da aka rantsar da majalisar dattawa ta 10 a watan Yuni 2023, ‘yan majalisa da dama sun koma APC, wanda ya sa jam’yyar na ci gaba da samun gagarumar rinjaye.
Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba, mai wakiltar Sakkwato ta kudu na jam’iyyar PDP, ya koma APC a watan Maris 2024. Da farko, Sanata Ifeanyi Ubah ya canza sheka daga YPP zuwa APC a watan Oktoba 2023 kafin rasuwarsa.
A watan Fabrairu na 2025, Sanata Ned Munir Nwoko, mai wakiltar Delta ta arewa ya bar PDP ya koma APC, yana mai bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida a PDP na Delta ya sa ya sauya sheka.
Haka kuma, Sanata Ezenwa Onyewuchi, mai wakiltar Imo ta gabas, wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar LP, ya koma APC a watan Yulin 2024, yana mai cewa batutuwan cikin gida ne suka jawo hakan.
Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta kudu, wanda aka zabe a karkashin tutun jam’iyyar NNPP, ya sauya sheka zuwa APC a ranar 7 ga Mayu, 2025.
Bayan haka, sanatoci guda uku daga Kebbi da suka hada da Adamu Aliero, mai wakiltar Kebbi ta tsakiyar da Yahaya Abdullahi, mai wakiltar Kebbi ta arewa, da Garba Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta kudu, suka sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan taron da Shugaban kasa Bola Tinubu ya kira a fadar shugaban kasa.
Kazalika, tun lokacin da aka kaddamar da majalisar wakilai ta 10 a watan Yuni na shekarar 2023, wannan majalisa ya fuskanci lamarin sauya sheka ga wasu daga cikin ‘yan majalisa, wanda ya faru sakamakon sabani na ciki gida a jam’iyyu, matsin lamba na mazabu da kuma sabbin tsarin siyasa wanda hakan ya amfanar da APC.
Da farko, APC ta rike kujeru 175; PDP na da 118; LP na da 35; NNPP na da 19; APGA na da 5; ADC na da 2; SDP na da 2; YPP na da 1; yayin da kujeru uku babu kowa. Gaba daya dai, ‘yan adawar na rike da kujeru 182 fiye da APC. Amma yau, adadin kujerun ’yan adawar ya ragu zuwa 150.
An fara wannan salo ne a ranar 23 ga Yuli, 2024, lokacin da Hon. Idris Salman, mai wakiltar Kabba-Bunu/Ijumu a Jihar Kogi, ya canza sheka daga ADC zuwa APC, yana mai cewa akwai rikicin shugabanci da kuma matsi daga mazabarsa wanda ya sa ya koma jam’iyyar da ke mulki.
A watan Oktoba na 2024, Hon. Chris Nkwonta, mai wakiltar mazabar Ukwa ta yamma da Abiya ta yamma, ya bar PDP ya koma APC a ranar 2 ga Oktoba. Bayan haka a wannan watan, Hon. Sulaiman Abubakar, mai wakitar Gummi/Bukkuyum a Zamfara, shi ma ya fice daga PDP.
Jam’iyyar LP, wacce ta sami karfi a shekara ta 2023, ta fara fuskantar manyan tangarda a karshen shekarar.
A ranar 5 ga Disamba, 2024, ‘yan majalisar LP hudu cikin har da Hon. Chinedu Okere, mai wakiltar Owerri da kewaye da Hon. Mathew Donatus, mai wakiltar Kaura a Kaduna da Hon. Bassey Akiba, mai wakiltar Kalabar da kewaye /Odukpani a Kuros Ribas da Hon. Esosa Iyawe, mai wakiltar Oredo a Jijar Edo, sun koma APC, suna mai bayar da hujja kan rikice-rikicen cikin gida da suka kawo cikas ga kwazonsu.
Hon. Alfred Ajang, mai wakiltar Jos ta kudi / gabas a Filato, ya biyo bayansu a ranar 12 ga Disamba, yana jaddada dalilai masu kama da juna.
Sauyin ya ci gaba har zuwa 2025. A ranar 11 ga watan Fabrairu, Hon. Amos Magaji, mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba a Jihar Kaduna) ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yana mai cewa akwai rigima a cikin jam’iyyarsa ta asali.
Washagarin ranar, Hon. Garba Koko, wai wakiltar Kebbi shi ma ya shiga APC daga PDP.
A ranar 18 ga Maris, Hon. Jallo Hussaini Mohammed, mai wakiltar Igabi a Jihar Kaduna, da Hon. Adamu Tanko, mai wakiltar Gurara/Suleja/Tafa a Neja, sun sauya sheka zuwa APC daga PDP, su yi ikirarin cewa rashin jin dadin shugabancin PDP da kuma bayyana kwarin gwiwa a gwamnatin Tinubu su ne makasudin sauya shekarsu.
A ranar 27 ga Maris, Farfesa Chinwe Clara Nnabuife, mai wakiltar Orumba ta arewa/kudu, a Jihar Anambra) ta fice daga YPP zuwa APGA, tana zargin an tsame ta daga ayyukan jam’iyyar.
A watan Mayu na shekara ta 2025, ya zama lokacin da aka sami manyan sauye-sauye. A ranar 6 ga Mayu, ‘yan majalisar PDP guda shida daga Jihar Delta sun canza sheka zuwa APC bayan gwamnan jihar, Sheriff Oborebwori ya jagoranci wannan sauyin. ‘Yan majalisar dai su ne, Hon. Bictor Nwokolo, mai wakiltar Ika arewa, gabas/Ika ta kudu da Hon. Julius Pondi, mai wakiltar Burutu da Hon. Thomas Ereyitomi, mai wakiltar mazabar Warri da Hon. Nicholas Mutu, mai wakiltar Bomadi/Patani) da Hon. Ukodhiko Jonathan, mai wakiltar mazabar Isoko da Hon. Ezechi Nnamdi, mai wakiltar Ndokwa/Ukwuani).
A ranar 15 ga watan Mayu, ‘yan majalisa biyu daga jam’iyyar NNPP, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun shiga APC. A wannan ranar, dan majalisan PDP mai wakiltar Oriade/Obokun daga Jihar Osun, Oluwole Oke, shi ma ya koma APC.
A ranar 22 ga Mayu, Hon. Sunday Umeha, mai wakitar Udi/Ezeagu daga Jihar Inugu, wanda aka zaba a karkashin LP, ya koma APC, yana cewa har yanzu matsalolin cikin gida na ci gaba da raba kawunan ‘ya’yan jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp