Aminiya:
2025-06-14@22:01:58 GMT

Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasu

Published: 29th, April 2025 GMT

Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Muslunci a Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, rasuwa.

Babban Mufti na ƙasar Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan, ne ya sanar da rasuwar Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a kai a daren Litinin.

Sai dai bai bayar da cikakken bayani game da inda Sheikh Hadiyatullah ya rasu ko kuma lokacin da hakan ya faru ba.

Sheikh Molaasan ya bayyana cewa rasuwar marigayi Sheikh Hadiyatullah ta bar giɓi mai wuyar cikewa a shugabancin Musulunci na ƙasar.

Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya

“An haife shi a garin Iwo a Jihar Osun kuma an san shi da dabi’u  Musulunci. Sheikh Hadiyatullah ya kasance fitaccen malamin Musulunci kuma masanin shari’a, wanda an san shi da ƙoƙarinsa na neman a aiwatar da Shari’a Musulunci a tsarin mulkin Najeriya, tattaunawa tsakanin addinai, da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin Najeriya masu bambancin addini.

“Ya yi aiki a matsayin Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci na tsawon shekaru, inda ya jagorance ta a lokutan ƙalubalen zamantakewa da ci gaba.

“Sheikh Hadiyatullah ya fara karatun addinin Musulunci a wurin malaman gida kafin ya ci gaba da karatunsa a ƙasashen waje.

“Ya samu girmamawa a faɗin Najeriya da ma wajenta saboda zurfin ilminsa a fannin fiƙihun Musulunci da kuma salon shugabancinsa mai nutsuwa da tsayin daka kan akida,” kamar yadda Molaasan ya bayyana.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa Sheikh Hadiyatullah ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Shari ar Muslunci Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah Sheikh Hadiyatullah Sheikh Hadiyatullah ya

এছাড়াও পড়ুন:

Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Nada Sabbin Kwamandojin Soja Da Dakarun Kare Juyin Musulunci

Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka yi shahada.

Bayan shahadar kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci Shahid Hussain Salami, da kuma  babban hshahid Muhammad Hussain Bakiri, sai Shahid Gulam Ali Rashid wanda shi ne kwamandan Bakirin soja na “Khatamul-Anbiya, jagoran juyin ya sanar da sunayen wadanda su ka maye gurbinsu.

Birgediya Muhammad Pakphur shi ne wanda jagoran ya sanar a matsayin sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci, sai kuma  Manjo Janar Musawi a mastayin sabon kwamandan rundunar sojan kasar, yayin da aka nada janar Ali Shadmani a matsayin kwamandan Barikin soja na Khatamul-Anbiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Samu Babban Canji Kan Tsarin Ciniki A Tsakanin Sin Da Afirka
  • Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai
  • Masana Ilimin Nukiliyar Iran Sun Yi Shahada
  • Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Nada Sabbin Kwamandojin Soja Da Dakarun Kare Juyin Musulunci
  • Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki
  • Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya
  • Iran tana da hakkin mayar da martani ga Isra’ila : Sanarwar Ma’aikatar harkokin waje
  • Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025
  • Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya
  • Ya Kamata Ana Kammala Shari’ar Zaɓe Kafin Rantsuwa