Sin Ta Yi Kira Ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya Da Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Sudan
Published: 28th, January 2025 GMT
Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang ya ce, ya kamata kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sudan, inda kuma ya bukaci gamayyar kasa da kasa da ta kara taka rawar gani wajen sasanta rikici a kasar.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya, yayin wani taro da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira don tantance rahoton da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta gabatar dangane da batun Darfur na kasar Sudan.
A cewar Geng, yayin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke gudanar da bincike a kasar Sudan, ya kamata ta yi mu’ammala sosai da gwamnatin kasar Sudan, kafin daukar wani mataki, ta yadda za a tabbatar da daidaita matsalar kasar, da magance tsanantar rikicin da ake samu. Kana ya kamata a aiwatar da dokokin kasa da kasa cikin daidaito, ba tare da siyasantar da harkokin shari’a, da bambanta ma’auni bisa wurin da ake ciki ba. (Bello Wang)
কীওয়ার্ড: kasar Sudan
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan
Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari.
Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka zarce ‘yan ciranin gargajiya na wasu kasashe kamar ‘yan Siriya da Falasdinawa.