Aminiya:
2025-11-03@08:04:17 GMT

AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon

Published: 1st, May 2025 GMT

Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar ta Tsakiyar Afirka saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023.

Wani taro da aka yi na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro kan sauyin siyasa a Gabon “ya yi nazari kan ayyukan tare da gano cewa sun yi nasara,” in ji shashen Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU a shafin X a ranar Laraba.

Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC

Sanarwar ta ce za a yi maraba da Gabon “ta dawo nan da nan, ta ci gaba da shiga ayyuka” a sakatariyar Tarayyar Afirka.

An dakatar da Gabon a lokacin da Janaral Brice Oligui Nguema ya ƙwace mulki bayan kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo, wanda iyalinsa suka yi mulki tsawon shekaru 55.

Nguema ya yi alkawarin miƙa mulkin ƙasar mai arzikin man fetur ga farar hula bayan shekaru biyu na riƙon ƙwarya, kuma an zaɓe shi a matsayin shugaban farar hula da kashi 94 na kuri’un da aka kaɗa.

Sabon kundin tsarin mulkin da aka samar ya tanadi cewa shugaban ƙasar zai yi mulkin ƙasar da faffaɗan iko.

Matakin da Tarayyar Afirka ta ɗauka ya biyo bayan taron da aka yi a makon da ya gabata tsakanin Nguema da shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara, inda Nguema ya nemi goyon baya ta hanyar janye masa takunkuman.

Kasar mai yawan mutane miliyan 2.3 tana fama da rashin ayyukan yi, da katsewar lantarki da rashin ruwan sha, da basussuka a suka yi wa gwamnati katutu duk da arzikin mai da take da shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tarayyar Afirka

এছাড়াও পড়ুন:

Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.

A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

Cikin wani saƙo da ya wallafa  a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.

Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.

“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar