Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko
Published: 1st, May 2025 GMT
Masana Alkur’ani daga ƙasashe 20 ne za su shiga Gasar Karatun Alƙur’ani ta Duniya da za gudanar a karon farko a Najeriya.
Gasar wadda za ta gudana a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos na Jihar Filato, sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja
Tsohon Ɗan Majalissar Wakilai Mai wakiltar Mazaɓar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Filato, Honorabul Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shiryawa.
A lokacin gagarumin taron kaddamar da kwamitocin shirye-shiryen gasar ta duniya, wanda Gwanayen Alƙur’ani daga faɗin kasar nan suka halarta, Honourable Alkali ya ce tuni an sanar da cibiyar bunƙasa karatun addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo ta Sakkwato kuma ta goyi bayan ƙudirin.
Ya ce gasar na da nufin haɓaka harkokin addinin Musulunci da haɗin kan Musulmi, yana mai bayyana muhimmancin tattaunawar karanta Alƙur’ani Mai Girma wanda shi ne babban malamin da ke wanke zuciya da samar da shiriya ga al’ummar Musulmi.
Da yake alƙawarin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, Alkali ya bayar da misalin yadda wani bawan Allah ya yi ƙoƙarin shirya gasar karatun Alƙur’ani ta duniya amma ba a samu nasara ba saboda wasu ƙalubale da aka fuskanta.
A jawabinsa, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Gwani Sadiq Zamfara, ya yi bayanin irin ayyukan da kwamitin ya gudanar da nufin ganin an samu nasarar gudanar da gasar ba tare da matsala ba, sannan ya yi godiya ga wanda ya ɗauki nauyin shirya gasar.
Kasashen da ake tsammanin za su halarci gasar sun haɗa da Kamaru da Ghana da Chadi da Senegal da Kenya da Tanzania da Mauritania da Masar da Moroko da Libya da Algeria da Saudiya da Kuwait da Qatar da Malaysia da Ingila da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa da Amurka.
Ko wace ƙasa zata zo da mahalarta gasar maza da mata da kuma hukumomin su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Alkur ani ta Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran
Farashin Man Fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran, lamarin da ya tayar da hankalin masu zuba jari.
Ana fargabar cewa rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya.
An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8Wani muhimmin wurin da ake safarar man fetur na duniya, wato mashigar Hormuz da ke kusa da Iran na da matuƙar tasiri, domin kashi ɗaya cikin biyar na dukkanin man da ake fitarwa daga nan ne ake bi da shi.
Amma duk da haka, kasuwannin hannun jari sun fuskanci faɗuwar daraja saboda rashin tabbas da harin ya haifar.
Sai dai darajar wasu hajojin da ake ɗauka amintattu a lokutan rikicin irin su zinariya da kuɗin ƙasar Japan, Yen sun tashi sama, domin masu zuba jari na ƙoƙarin neman mafaka a cikinsu.