Arif: A Shirye Muke Mu Sabunta Sana’o’in Sudan
Published: 1st, May 2025 GMT
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta.
Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da ya gana da ministar masana’antu ta Sudan Mahasin Ali Yakub da ta kawo Ziyara Iran.
Muhammad Ridha Arif ya yi wa Sudan fatan alheri da son ganin zaman lafiya ya dawo, sannan kuma ya bayyana sake bude ofishin jakadancin Sudan a Tehran a shekarar da ta gabata a matsayin alamar kyautatuwar alaka a tsakanin kasashen biyu.
Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya zargi kasashen turai da kuma HKI da haddasa fitintinu da rarraba a cikin kasashen musulmi da kuma karkatsasu zuwa kananan kasashe. Sai dai ya bayyana cewa da yardar Allah kasashen na turai ba za su yi nasara ba.
A nata gefen, ministar masana’antu ta kasar Sudan din ta bayyana tausayawa ga gwamnati da kuma al’ummar Iran akan hatsarin da ya faru a tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’i dake kudancin Iran wacce daruruwan mutane su ka rasa rayukansu da kuma jikkata.
Ministar ta kasr Sudan ta bayyana Jamhuriyar musulunci ta Iran a matsayin babbar kasa wacce ta ci gaba, kuma Sudan tana da bukatuwa da ci gaban da ta yi a cikin fagage mabanbanta na kere-kere.
Ministar ta kasar Sudan Mahasin Ali Yakub, ta bayyana fatan ganin Iran ta taimaka wajen sake gina Sudan da ta fuskanci rushewar cibiyoyinta da dama saboda yaki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki.
Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada.
Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin hanya tilo ta samar da zaman lafiya a kasar Falasdinu. Ya kuma bayyana rashin amincewar shirin tilastawa Falasdinwa barin kasarsu.