2025-05-13@04:58:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 74
«Ƙanwa»:
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin Mashawarci kuma Mai Kula da Shirin Gyaran Noma da Kiwo na Shugaban Ƙasa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar da naɗin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. An kashe shugaban Lakurawa,...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a...
A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka haɗe a ƙarƙashin Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS. Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin ƙungiyar da ƙasashen AES, domin har yanzu ana...
Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe. Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi. Daga...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa. Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da...
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su...
Shirin Rumbun Saukin zai fi bayar da da muhimmanci ne kan ma’aikatan gwamnati da dattijai masu shekaru 60 zuwa sama, inda kayan abincin za su kasance a nau’ikan ma’aunai daban-daban domin a dai-daita da bukatun iyalai da samun masu cin gajiya wanda za su yi rijista ta yanar gizo ko kuma ta cibiyoyin da aka...
Mansa Mūsā, ko dai shi jikan ko kuma abokin wasan Sundiata wanda shi ne ya kirkiro Daular Mali yah au kan karagar mulkin ne a shekarar. A karni na 17 (1324),lokacin ne ya tafi aikin Hajjin wanda ya zama abinmagana saboda dalilai masu dama. Aikin Hajjin da ya tafi ne ya sa idon duniya ya...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...
Kocin Manchester United Ruben Amorim ya bayyan cewar Kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Everton David Moyes ba mutum ne wanda za a raina iyawarshi a harkar kwallon ƙafa ba, David Moyes ya na yin aiki mai kyau na farfado da Everton fiye da yadda na ke yi cikin ƙanƙanin lokaci a Old Trafford inji Amorim....
Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar,...
Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da...
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da Jam’iyyar APC ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar wasu hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da suka hada da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun raba kudi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 da ke Kano a gaban kotu....
“Hakkinmu ne mu tabbatar da cewa kuɗin jama’a ba su faɗa hannun jagorori marasa cancanta ba. Saboda haka, za mu ɗaukaka ƙara kuma mu ci gaba da fafutuka har sai an yi mana adalci,” in ji shi.
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu...
Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen farfado da darajar ilimi, ya kuma nuna damuwa bisa ganin yadda darajar ilimi take kara faduwa a kasar nan. Ya ce dole sai gwamnati tarayya da na jihohi sun hada kai wajen tafiyar da harkar karantawa a kasar nan ta yadda yaran masu karamin karfi...
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon...
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon...
ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A da akan kwashe kwanaki ana bukukuwan aure a ƙasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin biki da zaman ajo zuwa buɗar kai da sayen baki. Sai dai waɗannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin...
Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu. Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya...

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba. “Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan...
Ya gargaɗi kamfanonin da suka samu kwangilar da su tabbatar da ingantaccen aiki, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗan aikin. Sannan, ya buƙaci direbobin manyan motoci da su guji lodin da ya fi ƙarfin titin domin kare lafiyar matafiya da rage hatsari. Don haka, gwamnati za ta kafa...
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansir Hassan ba da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.