Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan
Published: 1st, September 2025 GMT
Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622.
Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka jikkata a lamarin.
Sai dai hukumomi sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar yawan mutanen da suka mutu zai ƙaru, kasancewar yankin da abin ya shafa mai nisa ne, kuma ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa na fuskantar cikas wajen isa wurin.
Girgizar ƙasar ta auku ne da dare lokacin da mutane suke barci a gidajensu. Rahotanni sun nuna cewa daruruwan mutane na iya kasancewa sun maƙale ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe, lamarin da ke ƙara tsananta fargaba da damuwa a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Girgizar Kasa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas.
Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar.
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiA jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya.
“Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar Ribas domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa,” in ji Shugaban Ƙasa.
Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar, za su koma kan kujerunsu daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
Tun da farko, dokar ta-ɓacin ta dakatar da manyan jami’an gwamnati da masu madafun iko na jihar sakamakon rikici da aka daɗe ana yi a jihar.
“Da ban ayyana wannan dokar ta-ɓacin ba, da hakan ya zama babbar gazawa a wajena a matsayina na Shugaban Ƙasa.
“Amma yanzu da zaman lafiya da doka suka wanzu, al’ummar Jihar Ribas za su sake cin moriyar dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu.
Ya kuma yi kira ga gwamnoni da majalisun dokokin jihohi na faɗin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.
Har ila yau, ya jaddada cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tubalin kawo ci gaban dimokuraɗiyya ga al’umma.