PDD ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa
Published: 25th, August 2025 GMT
Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa.
Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Umar Iliya Damagum
এছাড়াও পড়ুন:
ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a BornoDa yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.
“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.
A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.