Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
Published: 30th, July 2025 GMT
Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
Shugabannin manyan hukumomin watsa labarai na ƙasa Hukumar Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) – sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, bisa rasuwar mijinta, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Daraktan Kula da Yankin Arewa maso Yamma na Rediyon Najeriya, Mallam Buhari Auwalu, shi ne ya gabatar da tawagar, inda ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasar a matsayin babban rashi ga iyalinsa, Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
Yayin ziyarar, Daraktan Sashen Injiniya na Hedikwatar Rediyon Najeriya, Injiniya Sanda Askira, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin kuma ya saka masa da Aljannatul Firdaus.
A madadin dangin marigayin, Dujiman Adamawa, Alhaji Musa Yola, ya nuna godiya ga Daraktocin Janar da sauran tawagar bisa wannan ziyarar ta’aziyya.
Ya ce wannan alamar jajantawa da nuna ƙauna ya zama babban ƙarfafawa ga iyalan marigayin a wannan lokaci na jimami.
Tawagar ta kuma kai ziyarar ta’aziyya ga ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Alhaji Mamman Daura.
Daraktocin Janar sun bayyana cewa za a ci gaba da tuna tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa gaskiyarsa, ƙaunarsa ga ƙasa da kuma gudunmawarsa wajen cigaban siyasa da tattalin arzikin Najeriya.
Haka kuma, sun yi addu’ar Allah ya baiwa iyalansa haƙuri da ƙarfin zuciya, tare da roƙon ‘yan Najeriya da su ci gaba da rayuwa bisa ƙa’idoji da dabi’un da marigayin ya tsaya kai da fata a kansu.
A nasa bangaren, Alhaji Mamman Daura ya nuna matuƙar godiya bisa ziyarar, yana mai bayyana ta a matsayin abin ƙarfafawa da kuma nuna haɗin kan ƙasa.
Ya gode wa shugabannin hukumomin labarai bisa addu’o’insu da kalamai masu daɗi da goyon baya da suka nuna wa iyalan Buhari a wannan lokaci na juyayi.
Cov/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Lalbarai ziyarar ta aziyya ga Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA