2025-10-13@17:06:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10130

«Rundunar Sojoji»:

    Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda...
    Sanarwar ta ce, wadannan hare-haren sun sake tabbatar da aniyar NAF na kare jami’an tsaro da fararen hula, da kuma ci gaba da matsin lamba kan masu tada kayar baya.   Ya kara da cewa, duk hare-haren an kammala su cikin nasara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Yanzu haka dai akwai jami’o’i da kwalejoji da cibiyoyi da dama da ake koyar da harshen mandarin a kasashen Afirka. Yayin da dalibai masu koyon harshen Mandarin suke ta karuwa a kullum. Misali a kasar Uganda akwai cibiyar koyar da harshen Mandarin wadda ta fara da dalibai 30 a shekara goma da ta gabata, amma...
    Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu domin tsunduma yajin aiki muddin ta ci gaba da sakaci kan wasu buƙatu da take nema a biya. A sanarwar gargaɗi da ASUUn ta fitar yau Litinin, ta ce daga jiya Lahadi, 28 ga watan Satumba, za ta bai wa gwamnatin...
    Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wato PENGASSAN, ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya daga daren Litinin, 29 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan umarnin da shugabancin ƙungiyar ya bayar tun ranar Lahadi, inda aka umurci mambobi da su tsaida aiki a dukkan kamfanoni da cibiyoyi da hukumomin da...
    ’Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 165.4 a watan nan na Satumba a Jihar Kano. Daga ciki, jami’an rundunar sun kama kwayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 82.7 a unguwar Rimin Auzinawa, suka mika ga Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin kammala bincike da gurfanarwa...
    Shigowar Ganduje Da Sauya Mallaka A Asirce Sakamakon barazanar soke yarjejeniyar ya sa dole wanda ya kafa kamfanin, Ahmad Rabiu, ya nemi sabon abokin tarayya. A cikin wannan lokacin ne, a ranar 5 ga Maris, 2020, aka gudanar da wani taro na musamman na kamfanin Dala Inland Dry Port. A cikin wannan taron, an cire...
    Kwamitin harkokin waje da tsaron kasar Iran ya kammala dukkan shirye shirye na ficewar kasar daga yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman nukliya ko na kissan kare dangi. Isma’il Riza’e shugaban kwamitin ya fadawa ya fadawa tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran kan cewa, kwamitinsa ya kammala shiri na dukkan takardu da tsare-tsaren da...
    An kashe sojan HKI guda a safiyar ranar Lahadi bayan da wani ba falasdine mai tuka babbar mota ya Burma motarsa kan gungun sojojin HKI a wani yanki kusa da Qalqelia na yankin yamma da kogin jorda. Ya kara da cewa kafin haka sojojin HKI sun kashe Falasdinawa da dama a yankin yamma da kogin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa bukatun gwamnatin Amurka daga kasar Iran ba abar amincewa ba ne. Shugabany a bayyana haka ne a ranar Asabar kafin ya bar birnin Newyork zuwa Tehran bayan ya halarci taron babban zauren MDD na shekara shekara. Yace: Bamu daidaita da su kan snapback ba, sai Amurka tace...
    Mohammad Bakir Qalibof kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa abinda kasashen turai uku suka yi na amfani da Snapback baya bisa ka’ida kuma Iran ba zata kiyayesu ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa kasashen Rasha da China...
    Jami’an tsaron kasar Burtania sun kama George Gallaway da matar a birnin londan bayan sun shigo kasar daga kasar Rasha a ranar Asabar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa Gallawy da matarsa sun shahara da goyon bayan gwagwarmayan falasdinawa da kuma kiyayya ga HKI. Kafin haka gwamnatin kasar Burtania ta amince...
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi...
    Hukumar lura da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa daga ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa na fasinjoji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Wannan na zuwa ne bayan dakatar da tafiye-tafiye a watan Agusta sakamakon hatsarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin jiragen....
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta koma kan teburin gasar Laliga bayan doke Real Sociedad da ci 2-1 a wasan da suka buga ranar Lahadi. Joules Kounde da Robert Lewandowski ne suka zura ƙwallayen biyu da suka tabbatar da nasarar. Da wannan sakamako, Barcelona ta tattara maki 19 daga wasanni bakwai, tana da tazarar maki...
    Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa za a ci gaba da samun isasshen man fetur duk da barazanar shiga yajin aiki da ƙungiyar PENGASSAN ta yi kan taƙaddama da matatar man Dangote. Wannan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa matatar ta dakatar da tsarin siyar da ɗanyen mai da ake biya sa...
    Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi, ya sallami Kwamishinar Harkokin Mata da Ci-gaban Yara, Zainab Baban Tanko. Sanarwar da kakakin gwamnan, Mukhtar Giɗaɗo, ya fitar ta bayyana cewa sallamar ta fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa hakan ta faru ne a sakamakon sauye-sauye a majalisar zartarwa ta Jihar Bauchi. Ya bayyana godiyar...
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi...
    A ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, jirgin ƙasan da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja zuwa Kaduna zai dawo aiki. Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta ce jirgin farko a ranar zai baro tashar Idu da ke Abuja da ƙarfe 8.45 na safe, ya iso Kubwa 9.05 sannan ya sauka a tashar...
    Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na...
      LEADERSHIP ta labaro cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya rantsar da Hajiya Zainab Baban Takko a matsayin Kwamishina ne a ranar 9 ga watan Satumban 2024 tare da wasu sabbin kwamishinoni biyu.   Kafin ta hau kan wannan kujerar, ta zama shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Bauchi wanda gwamnan jihar Bauchi Bala...
    A jiya Lahadi ne masu tafiyar da ayarin jiragen ruwan dake son keta killace Gaza ” Sumud” su ka sanar da cewa, tsakaninsu da yankin Gaza bai wuce kilo mita 825 Ba. Ayarin jiragen ruwan dai yana kunshe da kananan jiragen da sun kai 50, sun fuskanci hare-hare da jiragen sama marasa matuki na HKI...
     A wani taron da jakadun kasashen Fransa, Jamus da Ingila su ka yi, sun yi wa Rasha gargadin cewa, za su rika kai wa jiragenta na yaki hari, idan su ka keta hurumin samaniyar daya daga cikin kasashen mambobi na Nato.  Kamfanin dillancin labarun “Blumberg” ya watsa wani rahoto da a ciki ya bayyana cewa;...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 30 domin biyan buƙatun ’ya’yanta, ko kuma ta fuskanci yajin aiki. Wa’adin  na ƙunshe ne a sanarwar Bayan taron ƙungiyar, ɗauke da sa hannun shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman; Sakatare Janar, Dakta Shuaibu Ibrahim; da Sakataren Yaɗa Labarai, Dakta Abdulmajid...
    Kwanaki kadan bayan da aka gudanar da zaben raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar, mahkuntan sojan kasar sun ayyana ranar yin zaben shugaban kasa da zai zama na farko a cikin shekaru 4 na mulkin soja. Sanarwar tsayar da ranar yin zaben shugaban kasar dai, an yi ta ne ta hanyar dokar soja a...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi barazanar rufe Mahautar Akwanga saboda matsalar rashin tsafta. Kwamishinar Muhalli da Albarkatu ta jihar, Magret Elayo, ce ta bayyana hakan a yayin ziyar da ta kai mahautar, bisa wakilcin Babban Sakataren  ma’aikatar, Husseini Babayayi. Elayo ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da ayyuka a mahautar cikin rashin tsafta, lamarin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Ɗangote don a sasanta a yau. Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan ƙwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Ɗangote ta salami ma’aikata fiye...
    Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na...
    Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36. Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas...
    Al’ummar unguwar Kuntau da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano, sun shiga  jimami bayan rasuwar wani matashin limami, Salim Usman, wanda ake zargin ya rasu a hannun ’yan sanda. An kama Salim mai shekara 24 a gidansa a ranar 22 ga watan Satumba, jim kaɗan bayan jagorantar sallar Magariba. 2027: APC za ta ƙwace...
    Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro. Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro. Limami ya rasu a hannun ’yan sanda a Kano...
    Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Amurka ta kawo cikas ga yarjejeniya tsakanin Iran da Turai game da batun yin watsi da dawo da takunkumi kan Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: An cimma yarjejeniya da kasashen turai dangane da yadda za’a yi watsi da batun sake dawo da takunkumi kan Iran,...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu...
    Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne...
    Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York....
    A yau Lahadi ne aka gudanar da biki mai taken “Bude sabon babi a sabon zamani: Bikin zurfafa hadin gwiwa tsakanin CMG da bangarori daban daban na Macao” a yankin Macao na kasar Sin. Shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG Shen Haixiong, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi....
     Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Ba dole ba ne Iran ta bi hukunce-hukuncen da ba bisa ka’ida ba Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya tabbatar a cikin jawabinsa yayin zaman majalisar a yau Lahadi cewa: Iran ba ta daukar kanta a matsayin wajibcin aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya. A yayin taron UNGA, Shettima ya samu...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.   Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya...
    Jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Seyi Olorunsola, ya ce jam’iyyar za ta iya samun nasara a jihar a zaɓen 2027 ba tare da taimakon Rabiu Musa Kwankwaso ba. A baya-bayan nan an yi ta raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai fice daga NNPP tare da komawa jam’iyyar APC. Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram...
    Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno. Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom. PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki...
    Jami’an tsaro a Jihar Kogi sun ceto mutane takwas daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su har 12 a hanyar Okene–Auchi. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta jihar, William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a Lokoja ranar Asabar. Ya bayyana cewa fasinjojin suna tafiya ne a cikin motar haya ta...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas. Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa...
    An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama. Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta...
    Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.   Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki...
    Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa...
    Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan fashin teku ne sun yi awon gaba mutum 17 a wani kwale-kwale da ke kan iyakar teku a jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba. Lamarin ya faru ne a lokacin da fasinjojin suka taso daga wani ƙauye a kan iyakar jihohin biyu, inda ‘yan fashin suka afka wa...