Aminiya:
2025-12-01@16:15:15 GMT

MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar

Published: 1st, December 2025 GMT

Shugaban Ƙungiyar Iyaye na Jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’ar ta yanke wasu kuɗi masu yawa domin yaye ɗalibai.

A wata sanarwa da ya fitar tare da sakataren ƙungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya ce koken da aka kai wa PCACC da kuma rahotannin da aka wallafa ba su da tushe.

Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno

Ya bayyana zargin a matsayin yunƙurin ɓata wa jami’ar suna.

Ya ce MAAUN na daga cikin jami’o’in masu zaman kansu mafi sauƙin farashi a Kano, kuma tana ba da ingantaccen ilimi.

“MAAUN na ɗaya daga cikin jami’o’i masu zaman kansu masu sauƙin farashi a Kano, tana ba da ingantaccen ilimi tare da ƙayatattun gine-gine.

“Wasu jami’o’in a jihar suna cajin kuɗin makaranta ninki uku a kan na MAAUN, amma ba a jin kukan kowa game da su. Me ya sa sai MAAUN?

“Idan ɗalibi ya biya kuɗin makaranta na tsawon shekaru huɗu, me ya sa za a ga laifi idan aka nemi ya biya kuɗin yayewa a jami’a mai zaman kanta?

“Wannan ba wani sabon abu ba ne. Wannan batu gaba ɗaya na nuna wata maƙarƙashiya ce da ke nufin ɓata suna da barazana daga wanda ba a san ko waye ba da yake iƙirarin cewa yana kare muradun ɗalibai da iyaye,” in ji shi.

Ya kuma yi tambaya: “Me ya haɗa MAAUN da hukumar PCACC a kan wannan batu?”

A ƙarshe, ya shawarci wanda ya kafa jami’ar da ya ci gaba da jajircewa wajen samar da ilimi mai inganci.

A gefe guda kuma, ya yaba masa saboda ƙin ƙara kuɗin makaranta duk da halin matsin tattalin arziƙi da ya sa wasu jami’o’i ƙara ƙudinsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗalibai Kuɗin Yaye Dalibai MAAUN zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar.

Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni huɗu, domin bai wa gwamnatin Tarayya damar aiwatar da muhimman buƙatun da suka gabatar.

Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa

Ya ce an cimma matsayar ne bayan saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ta ƙunshi ci gaban da aka samu kan manyan buƙatu 19 na ƙungiyar, ciki har da biyan bashin albashi da alawus-alawus da sauran haƙƙoƙinsu.

Suleiman ya ce Majalisar Koli ta dakatar da yajin aikin ne a matsayin wata alama ta kyakkyawan fata, domin a ci gaba da sa ido kan yadda gwamnati za ta aiwatar da alƙawuran.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta yi amfani da wannan wa’adi na makonni huɗu domin ƙara faɗakar da ’yan Najeriya da kuma ci gaba da tattaunawa da gwamnati.

Yajin aikin ƙungiyar ya bar asibitoci 91 cikin mawuyacin hali, kasancewar likitoci 11,500 — waɗanda su ne manyan ginshiƙai da ke kula da marasa lafiya a ƙasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100%
  • N750,000 kuɗin bikin yaye ɗaliban Jami’ar MAAUN ya tayar da ƙura a Kano
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 163
  • Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
  • Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban
  • CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali