DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
Published: 3rd, December 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar.
Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban.
Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron yayin da yake shirin kama aiki a ma’aikatar tsaro bayan majalisa ta tabbatar da shi?
NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ma aikatar Tsaro matsalar tsaro Ministan tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus
Daga Bello Wakili
Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.
Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon.
Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har sau biyu daga 2015 zuwa 2023. An kuma naɗa shi minista ne a ranar 21 ga watan Agustan 2023.
Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaron ƙasa, kuma ana sa ran zai fayyace cikakkun matakan da za a ɗauka a nan gaba.