Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa
Published: 2nd, December 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Njgeria ta sanar da bai wa dan takarar shugabanncin kasar Guinea Bissau, Fernando Dias da Costa, ya kuma tsaya takara ne a tare da shugaban kasar Umar Sisoko Embalo da sojoji su ka kifar da gwamnatinsa kwanaki kadan bayan zabe.
A ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai Dias Da Costa ya sanar da cewa,shi ne wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, tare da zargin Embalo da cewa shi ne ya shirya juyin mulkin da ya kawo karshen zaben kasar, tun kafin a sanar da sakamakon zaben.
Haka nan kuma ya ce ya tsallake rijiya daga kokarin kama shi a ranar da aka yi jiyin Mulki, ya kuma boye, har sai da ya sami goyon bayan kasar Najeriya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, al-Kassim Abdulkadir ya ce; manufar bayar da mafaakr siyasar, shi ne kokarin hana dambaruwar siyasar a cikin kasar ta Guinea Bissau da rashin zaman lafiya a cikin yammacin Afirka.
Shi kuwa shugaban kasar da aka hambarar Embalo an tsare shi na wani lokaci, sai dai kuma an sake, shi sannan kuma ya nufi kasar Senegal domin samun mafakar siyasa. Sakin Embalo ya biyo yana tsoma bakin kungiyar tarayyar Afirka ne wacce ta yi Allawadai da juyin Mulki.
Kungiyar ta Ecowas ta aike da tawaga zuwa kasar ta Guine Bissau inda su ka gana da sojojin da su ka yi juyin Mulki. Ministan harkokin wajen Saliyo Thimothy Musa Kaba wanda ya jagoranci tawagar ya ce; Tattaunawar ta haifar da Da,mai ido. Sai dai kuma ta jadda kin amincea da juyin Mulki, tare da yin kira da a koma aiki da tsarin Mulki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu. December 2, 2025 Iran Bata Taba yin Watsi Da Diplomasiya Ba Amurka Ce Ke Kai Mutane Bango December 2, 2025 Shugaban Kungiyar ECOWAS Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau December 2, 2025 An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani
Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni.
Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace mulki a shekarar 2023, da kuma kamfanin Orano, mallakin kasar Faransa wacce ke da kashi 90% a arzikin urinum da ake fitawar shekarun baya.
A wani rahoto da gidan talabijin din kasar ta Nijar ya watsa da yammacin ranar Lahadi, an ambato shugaban kasar, Janar Abdourahamane Tiani, na tabbatar da “hakkin kasar na baje hajarta da albarkatunta da kuma sayar da su ga duk wanda ke son siyan su, bisa ga ka’idodin kasuwanci, cikin cikakken ‘yancin kai.”
Tun lokacin da sojoji suka kwace mulki a juyin mulkin 2023, Nijar ta juya baya ga faransa wacce ta yi mata mulkin mallaka, tana mai zarginta da tallafawa kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci