Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-12-01@22:47:11 GMT

Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Ajiye Aiki

Published: 2nd, December 2025 GMT

Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Ajiye Aiki

Daga Bello Wakili

Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon.

Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har sau biyu daga 2015 zuwa 2023. An kuma naɗa shi minista ne a ranar 21 ga watan Agustan 2023.

Murabus ɗinsa ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaron  ƙasa, kuma ana sa ran zai fayyace cikakkun matakan da za a ɗauka a nan gaba.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Badaru Badaru Abubakar

এছাড়াও পড়ুন:

DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon abokin takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaben 2023 tare da Peter Obi.

DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed ne a daren Juma’a bisa zargin ci gaba da bayyana ra’ayoyi da take ganin na iya tayar da hankali a Najeriya.

Wata majiyar tsaro ta ce DSS ta daɗe tana bibiyar kalaman Baba-Ahmed a kafafen yada labarai, musamman kan iƙirarin da ya yi na cewa akwai “rikicin kundin tsarin mulki” a Najeriya.

A cewar majiyar, “Kwanan nan Datti Baba-Ahmed ya bayyana a talabijin inda ya zargi kotuna da rundunar sojoji da rashin hana rantsar da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima. Har ma ya yi nuni da cewa rantsar da Tinubu ta bai wa sojoji damar cin mutuncin mutane.

Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika

Ta ƙara da cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da tashin hankali a ƙasar, musamman a irin wannan yanayin siyasa da ake ciki.

Ta ce, “Abin damuwa ne ganin yadda irin wannan magana ta janyo rikice-rikice a wasu ƙasashe kamar Guinea-Bissau. Hukumar tsaro tana ɗaukar wannan da muhimmanci, ba don siyasa ba, sai don kare zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.”

A cewar majiyar, DSS ta yi wannan gayyata ne bisa ƙa’ida, saboda kalaman Datti Baba-Ahmed da suka yi kama da raina ƙoƙarin gwamnati wajen inganta tsaro a matsayin “wasa” na iya tayar da hankalin jama’a da kuma rage amincewa da hukumomin ƙasa.

Ta ce, “Wannan gayyatar ba hukunci ba ne, amma matakin kariya ne domin fayyace niyya, da manufar kalamansa a muhallinsu, da kuma hana fitowar labarai da za su iya haifar da rikici ba tare da an yi niyya ba.”

Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwa ba, haka kuma Datti Baba-Ahmed bai ce komai a hukumance kan gayyatar ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Yi Murabus
  • Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3  A Kasar Lebanon
  • Najeriya Ta Kara Ƙaimi Wajen Kawar da Cutar HIV Nan da 2030
  • Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran
  • Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran.
  • Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki
  • Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku
  • Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32
  • DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali