Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro
Published: 3rd, December 2025 GMT
Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele.
Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan TsaroSanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar da wanda aka naɗa Ministan Tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a karanta wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da tantance wanda aka naɗa nan take.
Opeyemi ya bayyana cewa majalisar ba za ta iya jinkirta irin wannan buƙata ba a wannan lokaci mai muhimmanci, domin ta shafi muhimman abubuwan da suka shafi ƙasar.
A ranar Talat ace Tinubu ya aike da sunan Christopher gaban majalisar domin amincewa bayan murabus din tsohon Ministan, Muhammad Bdaru Abubakar.
Kafin nadin nasa dai, Christopher shi ne tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya da Tinubu ya sauke tare da ragowar manyan hafsoshi a kwanakin baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majlisar Dattawa Ministan Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu.
Rahotanni da suka fito daga Najeriya sun nuna cewa ministan tsaro Alh mohammadu Badaru Abubakar a ranar 1 ga watan Decemba ya mika takardar ajiye aiki a matsayinsa na ministan tsaron kasa, saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa,
Kamar yadda kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba tinubu ya amince da takardar neman ajiye aikin, kuma ya gudemasa game da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasarsa, tuni kuma aka fara lalubo wanda zai maye gurbinsa domin mika sunansa ga majalisa don a tantance shi.
Badaru Abubakar dan shekara 63 da haihuwa shi ne gwamnan jihar jigawa har na tsawon zango biyu wato daga shekara ta 2015 zuwa ta 2023 kuma shugaban kasa tunubu ya nada shi a mukamin minister a ranar 21 ga watan Agusta shekara ta 2023
Ya ajiye aikin ne adai dai lokacin da shugaba tunubu ya sanya dokar ta baci kan tsaro a fadin kasar,da zimma kawo karshen matsalar tsaro da kasar take fama da shi .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Bata Taba yin Watsi Da Diplomasiya Ba Amurka Ce Ke Kai Mutane Bango December 2, 2025 Shugaban Kungiyar ECOWAS Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau December 2, 2025 An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma December 2, 2025 Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci