Aminiya:
2025-12-03@11:01:54 GMT

Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio

Published: 3rd, December 2025 GMT

Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio

Daga Musa Kutama, Kalaba

Yusuf Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Yusuf Lazio, fitaccen jarumi ne a Masana’antar Finafinan Hausa, wato Kannywood. Jarumin ya yi shura a fim xin Na-Ladidi, inda ya ce, haxa waqa da fim a lokaci xaya, a wurinsa ba wani abu ba ne, hasali ma mawaqi ne shi kafin ya fara fitowa cikin fim.

Ga yadda hirar ta kasance:

Gabatar da kanka ?

Sunana Yusuf  Mohammad Abdullahi  ana kira na da  Yusuf Lazio.

Dama can kana da alaqa da Lazio ne ko kuwa kulob xin ne ake kiran ka da shi?

A’a sunan ya samo asali ne daga goya wa qungiyar wasan qwallon qafa ta Lazio baya da nake yi.

An lura a ‘yan kwanakin nan ka xauke qafa a harkar fim, ka fi karkata a kan waqa. Me za ka ce a nan?

Ba xauke qafa na yi ba, ina nan ina fitowa a wani fim mai suna Gidan Sarauta sannan kuma yanzu haka ina aiki ma a wani fim xin daban.

Ga alama ka fi mayar da hankali wajen yin waqa a kan fim, wane qarin bayani za kayi a nan?

Har yanzu ina yin waqa kuma ina yin fim, domin waqa ce ta fara fito da ni. Sannan kafin ma in fara fitowa a fim da ma ni waqa nake yi sannan na dawo yin fim.

Kana ganin za ka iya haxa taura biyu?

Eh,  ba za su yi wahala ba, tunda duk biyun suna da alaqa.

Tsakanin yin fim da kuma waqa wanne ya fi wani wahala?

Gaskiya wannan wata harka ce da zan ce ma kamar ado ne. Ita waqa ana yin ta daban, abu ne na basira. Sannan fim ma abu ne na sha’awa, don haka haxa biyun bai ba ni wahala ba kwatakwata.

Ka lura da irin sauyi da ci gaban da ake samu ta harkar fim da kayan aiki na zamani ya kawo?

Eh, to dama ai kasan duk mai sana’a duk wacce ta fi kawo maka riba ai ita za ka fi mayar da hankali a kai. Cikin ikon Allah mun samu sauyi mai yawa, mun samu nasara a kan haka, wanda a da qaramin jarumi ba zai iya yin fim nasa na kansa ba. Amma yanzu zai iya fitowa, ya yi fim nasa, ya bayar da umarni. Hakan ya sa na yi matuqar farin ciki da wannan ci gaba da aka samu.

Da ka ce an samu ci gaba ta wane vangare sai ka yi bayani?

Yanzu idan ka duba, zan iya yin fim ba darakta, ka ga zan iya yi, in sanya a Youtube, mutane su kalla. Ka ga wannan ba qaramin ci gaba ba ne aka samu a fannin yin fim. Sannan kuma yanzu ba sai ka naxi fim a kaset ko a wani CD ba, kana iya shiga Youtube ka sa, a kalla.

Ko kwalliya na biyan kuxin sabulu a sanya finafinanku ta kafar sada zumunta. Kuxaxen da kuka sanya aka yi aikin ko suna fitowa hala har ma a sa rai za a samun riba?

Qwarai ana samun nasara a kan haka, akwai riba.

Shin xora waqoqi ko fim a YouTube kana ganin zai magance satar fasahar waqa ko fim?

Ka san kowane mai sana’a yana yi don riba ce.  Alhamdulillahi, wannan sabuwar dabara nasara ce a cikin sana’armu, duk da yake ba za a rasa samun qananan abubuwa da za su riqa tasowa ba.

Ya alaqa take tsakaninku da Hukimar Tace Finafinai lura da cewa, yanzu ana sanya fim a YouTube mai yiwuwa ba tare da an kai mata, ta tantance fim xin ba?

Gaskiya ni ban tava karo da su ba, domin ni duk abin da nake yi ina tabbatar da cewa na kare abin da addinina yake so na kuma kiyaye abin da ba ya so. Ka ga ba zan shiga wani layi ba da na san abin zai kawo min zubar da mutuncina.

Bari mu koma kan waqa, ka ce ka haxa biyu fim da waqa wane vangare kake yi wa waqa ‘ya siyasa ko masu kuxi ko iya ta fim ka tsaya?

Gaskiya na fi mayar da hankali a waqoqin gambara, wato Hiphop na Hausa. Akwai albom da nake aiki a kansa na wasu sababbin waqoqin da na yi wanda na gambara ne gaba xaya.

Kuma kwalliya na biyan kuxin sabulu ?

Alhamdulillahi.

Wacce shawara kake xauke da ita ga masu tasowa don su mayar da hankali a kan abin da suka sa gaba?

Shawarata ita ce su mayar da hankali su tabbatar sun cim ma burinsu.

 

Tauraron Finanfinan Indiya na Bollywood, Dharmendra ya rasu yana da shekara 89

Dharmendra ya rasu ranar Litinin a wani asibiti a birnin Mumbai na Indiya bayan gajeruwar rashin lafiya.

Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi ya yi ta’aziyyar jarumin a cikin, yana mai cewa rasuwarsa “ta kawo babban givi a Masana’antar Fim ta Indiya”.

An haifi tsohon tauraron Bollywood a ranar 8 ga Disambar 1935 a qauyen Nasrali da ke Gundumar Ludhiana ta Punjab.

Mahaifinsa malamin makaranta ne, kuma shi ya sanya masa suna Dharam Singh Deol.

A lokacin rayuwarsa, Dharmendra ya bayyana kansa a matsayin “mutum mai sauqin kai”, wanda ya sami qauna da aminci daga miliyoyin magoya bayansa.

Ya taka rawar gani da dama, amma an fi sanin sa da Veeru, a cikin fim xin Sholay na 1975. Duk da haka, Dharmendra ya fito a finafinai sama da 300 da waqoqi da yawa,waxanda suka ja hankalin masu kallo tsawon shekaru da yawa.

A wani lokaci, jarumin, wanda aka tava yi masa laqabi da “Asalin Mutumin Bollywood” da “Garam  wato mai zafin nama”, ya shiga jerin “mazaje mafi kyau” a duniya a lokacin da ya kai qololuwar nasararsa; kuma akasarin magoya bayansa mata ne, inda ta kai har  suna kwana da hotunansa a qarqashin matashin kansu.

Ya bar mata biyu Prakash Kaur da Hema Malini da ‘ya’ya shida, Sunny Deol da Bobby Deol da Esha Deol da Ahana Deol da Vijeta da Ajeeta Deol da kuma jikoki goma sha uku.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: mayar da hankali Dharmendra ya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano

’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance.

Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32

Yayin kai harin, ’yan bindigar sun kuma sace aƙalla mutum uku.

Yankamaye, wani ƙaramin ƙauyen manoma ne, ’yan bindiga da ke tserewa daga maƙwabtan jihohin Kano ne suka fara kai musu hare-hare.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tura jami’ai domin bin diddigin maharan.

Mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun isa ne a kan babura inda suka ajiye su daga nesa, sannan suka shiga ƙauyen a ƙafa.

A yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar kwanan nan, Gwamna Abba Yusuf, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro.

Ya kuma ce hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da ɓarayi shanu a wasu yankunan Arewacin jihar, babban abin damuwa ne.

Gwamnan, ya ce suna aiki tare da hukumomin tsaro don magance barazanar da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Ya bayyana ƙananan hukumomin da abin ya shafa; Kunchi, Tsanyawa, Gwarzo, Kabo, Sumaila, Shanono, Tudun Wada, Doguwa, da Rogo.

Amma ya ce hukumomi na ci gaba da ayyuka domin toshe hanyoyin shigowar ’yan bindiga da kuma kare al’ummomin ƙauyuka.

“Duk da wasu ƙalubale da ake fuskanta a nan da can, jama’a su kwantar da hankalinsu, gwamnati tana aiki domin magance duk wata barazana ga zaman lafiya,” in ji Yusuf.

Gwamnan, ya kuma goyi bayan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ayyana dokar ta-ɓaci a harkar tsaro a faɗin ƙasar nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta
  • Majalisar Dokokin Akwa Ibom ta yi fatali da ƙudurin neman hana cin naman kare
  • An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164
  • Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano