Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori
Published: 3rd, December 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya.
Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu, manyan sakatarorin biyar Abdulkarim Ibrahim, Dr John Ezeamama, Dr Abdul-Sule Garba, Dr Isiaku Mohammed da Dr Ukaire Chigbowu, sun dauki rantsuwar kama aiki, sannan suka sanya hannu a kundin rantsuwa.
An kuma rantsar da Dr Aminu Yusuf, wanda shugaban kasa ya nada a matsayin Shugaban NPC a ranar 9 ga Oktoba, da kwamishinoni biyu ciki har da Dr Tonga Betara daga Jihar.
NPC ita ce hukuma da ke da alhakin gudanar da kidayar jama’a a hukumance, yin rajistar haihuwa da mace-mace, da tattara bayanan kimiyyar jama’a domin tsare-tsare.
Majalisar ta yi shiru na minti guda domin tunawa da tsohuwar Ministar Harkokin Waje, Ambasada Joy Ogwu, wadda ta rasu a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025 tana da shekaru 79.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar.
Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin kallafaffen yaki na shekaru takwas tsakanin 1980-1988, dukkanin duniya ta kasance a bayan ‘yan Ba’asiyya da zummar kawo karshen jamhuriyar musulunci,amma goyon bayan da al’ummar Iran suke bai wa tsarin musulunci goyon baya, hakan ba ta faru ba.
Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; “Yan Sahayoniya da Amurka sun kawo wa Iran hari da yakin kwanaki 12 a karkashin wannan irin tunanin na kawo karshen tsarin musulunci a cikin kwakani kadan, su kuma ingiza al’ummar kasar zuwa kan tituna su yi wat sarin musulunci bore, said ai yadda al’ummar ta Iran ta yi tsayin daka ta kare kasa da tsarin dake tafiyar da kasar, ya rusa wannan makarmashiyar tashi.
Wani sashe na jawabin shugaban kasar ya kunshi cewa wajibi ne ga gwamnati ta kasance a tare da al’ummar kasa domin warware matsalolin da suke fuskanta da kuma kare mutuncin kasa da ‘yancinta.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa ( Ritaya) A Matsayin Ministan Tsaro December 2, 2025 Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa December 2, 2025 Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu. December 2, 2025 Iran Bata Taba yin Watsi Da Diplomasiya Ba Amurka Ce Ke Kai Mutane Bango December 2, 2025 Shugaban Kungiyar ECOWAS Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau December 2, 2025 An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Aljeriya: Taron Kasashen Afirka Don Amincewa Da Mulkin Mallaka A Matsayin Laifi December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci