Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20
Published: 2nd, December 2025 GMT
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita.
Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar a baya.
Bayan kauracewa taron shugabannin G20 da aka gudanar a Johannesburg a ranar 22-23 ga Nuwamba a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu, Trump ya maimaita ikirarinsa na cewa gwamnatin kasar mai rinjayen bakaken fata tana nuna wariya ga tsirarun fararen fata.
A jawabinsa, Ramaphosa ya kira zarge-zargen Trump na kisan kare dangi da kwace filaye daga fararen fata da cewa ba gaskiya ba ne, zargui ne maras hujja balantana makama, yana mai sake jaddada cewa “Afirka ta Kudu cikakkiyar memba ce da aka kafa G20 tare da ita.”
Rikicin da ke tsakanin Washington da Pretoria ya fara kamari ne a farkon 2025. A ranar 14 ga Maris, Amurka ta kori jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, bayan ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da abokansa da haɓaka ajandar duniya ta masu ra’ayin wariyar launin fata
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban venuzuwela Ya Gargadi Amurka Game Da Kokarin Da Take yi Na Karbe Ikon Kula Da Rijiyoyin Mai Na Kasar
Nicolas Maduro shugaban kasar Venzuwela yayi tir da barazanar da Washington ke ta nanatawa na yin amfani da karfin soji kan karakas, kuma yayi gargadi game da shirin Amurka na kwace ikon kila da rijiyoyin mai na kasar a hanyar amfani da karfin soji.
Maduro yayi wannan bayanin ne a cikin wata wasika da ya aikewa sakatare janar din hukumar kula da hakon manfetur ta duniya OPEC,
Kasar venuzuwela a hukumance ta bayyanawa hukumar cewa gwamnatin Amurka tana so kwace kula da rijiyoyin manta, mafi girma a duniya, ta hanyar yin amfani da karfin soja akanta da mutane da sauran humumomin kasar,
Haka zalika ya fadi a cikin wasikar cewa zai ci gaba da tsayawa kyam wajen kare arzikin makamashi da kasar ke da shi,kuma ba zai mika wuya ga duk wani bata suna ko barazana ba
Wannan wasika ta zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump yayi barazana a ranar Asabar cewa za’a rufe dukkan sararin samaniyar kasar venuzuwela.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala November 30, 2025 MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Turkiya November 30, 2025 An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu November 30, 2025 Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5 November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci