An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
Published: 2nd, December 2025 GMT
Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu.
Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka tafi gona domin yin roron wake lokacin da aka afka musu.
NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a JigawaYa ce: “An fara kai hari ne ga mutane 15, wasu sun tsere, wasu kuma aka sake su ba tare da sharaɗi ba. Amma har yanzu mutum 11 suna hannun ’yan bindiga, kuma sun buƙaci a biya su kuɗin fansa na naira miliyan biyar,” in ji shi.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Talata, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazavar Jama’a/Sanga, Hon. Daniel Amos, ya bayyana satar mutanen a matsayin mugunta da rashin tausayi, tare da yin Allah-wadai da kai hari kan talakawa masu aikin halaliya.
“Muna buƙatar kara tsaurara tsaro, yin amfani da dabarun bayanan sirri, da ɗaukar matakan gaggawa da haɗin gwiwa domin kwantar da hankalin jama’a da kuma ceto waxa0nda aka sace,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Kasashen Larabawa Sun Yi Allah wadai da kutsen sojojin Isra’ila a Kudancin Siriya
Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara.
A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila.
Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon.
A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.”
Ita ma Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya, ta “yi Allah wadai da harin ” da sojojin Isra’ila ke yi, wadanda ke kokarin “wargaza tsaro da zaman lafiyar Siriya da mutanenta.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Kuwait ta kuma yi Allah wadai da harin: “Waɗannan hare-haren laifuka ci gaba ne na dabarun wargaza zaman lafiya, wanda ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankalin yankin.
” Akalla ‘yan Siriya 13, ne suka mutu, yayin da wasu sama da 20 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai a Beit Jinn, wani yanki na birnin Damascus.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa November 29, 2025 Lebanon ta shigar da kara ga Kwamitin Tsaro bayan Isra’ila ta Gina katanga a Yankinta November 29, 2025 AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji November 29, 2025 Najeriya : An yi jana’izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi November 29, 2025 Larijani: Da’awar lalata karfin nukiliyar Iran wauta ce November 29, 2025 Babban banki Najeriya Ya Tura Dala Miliyan 50 Don Ƙarfafa Kasuwar Musayar Kudade November 29, 2025 Iran Da Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Hare-Haren Isra’ila A Kan Kasar Siriya November 29, 2025 Ziyarar Da Larijani Ya Kai Pakistan Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kara Dankon Zumunci November 29, 2025 Shaikh Niam Qasem: Hizbullah ce Za ta Mayar Da Martani Lokacin Da Ya Dace Kan Kisan Kwamandanta November 29, 2025 Iran Za ta Kauracewa taron fasalta kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026 November 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci