Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
Published: 2nd, December 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.
A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.
Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025.
An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da matsakaitan Sojoji (NDA) duk dai a wannan shekarar, inda ya samu digiri na daya a fannin kimiyya a 1991.
An daga Janar Musa zuwa matsayin babban Laftanar (Second Lieutenant) a 1991, kuma tun daga lokacin ya yi aiki a manyan mukamai iri-iri. Daga cikin mukamansa akwai: Babban Jami’in Ma’aikata a bangaren Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81;
Kwamandan Bataliya ta 73;
Mataimakin Darakta, Kayayyakin Aiki, Sashen Tsare-tsaren Rundunar Soja;
Wakilin Sojin Kasa a Kwamitin Horaswa na Hedikwatar Soji ta Najeriya.
A 2019, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Jami’in Ma’aikata na Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Cibiyar Sojin Kasa;
Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Lafiya Dole; da kuma Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Tafkin Chadi (Multinational Joint Task Force).
A 2021, an nada shi Kwamandan Operation Hadin Kai, inda daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya nada shi Shugaban Hafsoshin Tsaro a 2023.
A cikin wasikar da ya aikewa Majalisar Dattawa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken kwarin gwiwa kan ƙwarewar Janar Musa wajen jagorantar Ma’aikatar Tsaro tare da ƙara inganta tsarin tsaron Najeriya.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ministan Tsaro Shugaba Tinubu ya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Halayen Da Ambasadoji Ya Kamata Su Mallaka Kafin Tura Su Wasu Kasashe
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.
Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sunayen jakadu da yake sa ran majalisar kasa ta tantance ne dai batun ke ta shan suka daga manazarta kan sunayen da ya fitar.
Ko wadanne irin halaye ya kamata jakada ya mallaka a yayin da za a tura shi a matsayin wakili a wata kasa?
NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan