Lebanon: An Gudanar Da Taron Musulunci da Kiristanci a Beirut tare da halartar Paparoma
Published: 2nd, December 2025 GMT
Paparoma Leo XIV ya halarci taron Musulunci da Kiristanci da tattaunawa tsakanin addinai a dandalin Shahidai da ke Beirut.
Bayan isowarsa, Paparoma ya samu tarba daga shugaban Mabiya addinin kirista na Lebanon Bechara Boutros al-Rahi, da shugaban Mabiya darikar Katolika na Syria Ignatius Joseph III Younan, da kuma Babban Mufti na Lebanon Sheikh Abdul Latif Derian, da Mataimakin Shugaban Majalisar koli ta Mabiya mazhabar Shi’a a Lebanon Sheikh Ali al-Khatib.
A lokacin taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Shi’a a Lebanon ya yi maraba da Paparoma, yana mai cewa: “Muna farin ciki da zuwnku a Lebanon a madadin Majalisar da kuma daukacin mabiya mazhabar shi’a na Lebanon, Muna maraba da kuma godiya da ziyararku zuwa kasarmu a wannan mawuyacin lokaci da kasarmu ke ciki.”
Ya ƙara da cewa: “Muna fatan ziyararku za ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa wadda ke fama da raunukan da hare-haren Isra’ila ke ci gaba da haifarwa na zalunci.”
Ya ci gaba da cewa: “Ba ma son ɗaukar makamai, kuma muna sanya alkiblar Lebanon ta zama a hannu na gari, muna fatan duniya za ta taimaka wa ƙasarmu ta sami zaman lafiya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chuck Schumer: Trump Ba Shi da Ikon Kaddamar da Yaki Kan Venezuela December 2, 2025 Najeriya: Matatar Dangote Za Ta Mika Tataccen Mai Lita Biliyan 1.5 A Watan Disamba December 2, 2025 Ramaphosa ya yi watsi da barazanar Trump na ware Afirka ta Kudu daga G20 December 2, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165 December 1, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164 December 1, 2025 Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya December 1, 2025 Paparoma Leo Na 14 Yana Ziyarar Aiki Na Kwanaki 3 A Kasar Lebanon December 1, 2025 Kamaru: Madugun Adawa Ya Rasu A Gidan Kaso December 1, 2025 Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu.
Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna.
’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa masu ibada a KogiSarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi.
A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya hau mulki ya juya musu baya.
Ya nuna damuwa cewa mutane da dama na zargin gwamnonin da rashin yin aiki, alhali suna fuskantar matsin lamba.
Sarkin ya shawarce su da su rika karɓar ƙorafe-ƙorafe masu amfani tare da gyara inda ya dace, domin hakan na taimakawa wajen yanke shawara mai kyau.
Haka kuma, ya yi kira da a ƙara samun haɗin kai a tsakanin gwamnonin, inda ya ce hakan ne zai taimaka wajen inganta Arewa da daidaita ƙasa baki ɗaya.
Sarkin Musulmi ya tabbatar wa gwamnonin cewa sarakunan gargajiya na tare da su, kuma a shirye suke ba su goyon baya a kowane lokaci.
Ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnoni da sarakunan gargajiya su riƙa gudanar da taruka akai-akai domin tattauna matsaloli da yanke shawara tare.
A ƙarshe, ya ce sarakunan gargajiya za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa da Najeriya gaba baki ɗaya.