Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
Published: 3rd, December 2025 GMT
Daga Ali Muhammad Rabi’u
An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri.
An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin.
A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin.
Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma su rika kai rahoton duk wani abin da suke zargin zai iya haddasa fitina ga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a makarantar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru
Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata.
Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata.
Jami’an tsaro sun yi dirar mikiya kan masu goyon bayan Chiroma, kuma sun kashe mutane da dama sun kuma kama wasu Anicen Ekaney ana daga cikin wadan da aka kama a birnin Duala a ranar 24 ga watan Octoba. Kuma Ekane ya zargi jami’an tsaro da kwace maganin Oxigen dinsa, wanda ya jefa rayuwarsa cikin hatsari, sannan daga karshe lawyansa ya bada sanarwan mutuwarsa a yau Litinin a tsare a hannun jami’an tsaron kasar. Kafin haka jam’iyyarsa ta bada sanarwan cewa, kwace maganinsa wanda Jami’an tsaro suka yi zai jefa rayuwarsa cikin hatsari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tawagar ECOWAS Ta Bar Guinea – Bissau bayan da shugaban kasar yayi barazanar korarsu Da Karfi December 1, 2025 Yawan Yahudawan Da Suke Ficewa Daga HKI Sun Nininka Har Sau 100% December 1, 2025 Gaza: Fiye da Falasdinawa 350 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun bayan tsagaita wuta December 1, 2025 Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta December 1, 2025 Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci