Sharhi:’HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’.
Published: 2nd, December 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ‘Sharhin bayan labarai, wand ani tahar amin zan karanta.
A cikin shirimmu na yau zamu yi Magana dangane cewa, shin gaskiyar ne ‘HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin HKI a karon farko a hukumance, ta bada sanarwan cewa, tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar, kuma wannan Babbar barazana ce kuma hatsari ne ga samuwar kasar kai tsaye.
Sanarwan ma’aikatar yakin HKI dangane da wannan ta ce, tana fada da karancin sojoji kimani 1300 a dukka rassan sojojin kasar kama daga kananan sojoji har zuwa manya. Bayanin ya kara da cewa ma’aikatar tana fama da karancin sojoji masu mukamin kanar har guda 300 a cikin rundunoninta gaba daya.
Har’ila, rahoton ya kara da cewa kashi 30 na kwamandojin sojojin kasar masu manya-manyan mukamai zasu yi ritaya a shekara mai zuwa. Sannan wasu kashi 30% na sojoji na ko ta kwana da kuma wadanda suke aiki na dindin din a cikin sojojin kasar suma zasu yi ritaya, ba zasu sake komawa cikin sojojin haramtacciyar kasar ba.
Rahoton ya kara da cewa, kashi 37% na sojojin suna son ci gaba da aikinsu a rundunonin ta, wanda ya nuna cewa adadin ya kara yin kasa idan an kwanatnta da shekara ta 2018 wanda ya kai kashi 58%.
Sannan tambaya ta gaba itace, menene dalilan da suka kawo karancin sojojin a cikin HKI ?.
Masu Nazari sun bayyana cewa matsalar karancin sojoji a HKI yana komawa daga asali zuwa ga matsalolin tsaro da kuma tattalin arziki. Yaki mai tsawo musamman a cikin shekaru biyu da suka gabata, da gajiya mai tsanani ya rage kodayin sojojin da kuma iyalansu ci gaba da wannan aikin.
A cikin rahoton da ma’aikatar yakin HKI ta fitar ta bayyana cewa, kashi 70% na matsalolin da sojojin haramtacciyar kasar suka fuskanta sun hada da tsawon yakin da suka kutsa cikinsa, wanda ya wuce lokacin da yakamata su yi.
Banda haka a cikin shekaru biyu da suka gabata, yakin ya tsananta kuma yayi tsawo ta yadda sojojin da iyalansu sun kasa hakuri fiye da hakan.
A bangaren tattalin arziki kuma, tsadar rayuwa a cikin kasar ya kai ga sojojin da kuma iyalansu sun ga cewa shiga harkar kasuwanci ne kawai zai fiddasu daga matsalolin tattalin arzikin da suka shiga musamman bayan yakin shekaru biyu da suka gabata. Don haka albashin da suke samu a aikin soje ya yi kasa sosai ta yadda ba za’a iya kwatantaci da wasu ayyuka wanda ba na soje ba.
Sannan tambaya ta gabata ita ce, karancin sojoji a cikin rundunonin HKI zuwa ga me yake nuni? Wannan a fili yake, kuma hatta a cikin rahoton da ma’aikatar yakin ta fitar ta yi nuni ga wannan al-amarin. Inda take cewa, matsalar karancin sojoji a rundunonin haramtacciyar kasar ya kai ga barazana ga tsarin cikin gida na kasar, kuma dole ne gwamnati kasar ta dauki matakan da suka dace, don magance ta , da gaggawa.
Ta kuma kara da cewa ratayar kashi 30% na kwamandojin sojojin kasar yana nuna zuwa ga matsalolin gudanarwa a cikin rundunonin sojojin kasar da kuma matsalolin horar da sabbin sojoji.
Masana suna ganin wannan matsalar tana iya zama barazana ga HKI musamman idan ta sake shiga yaki da kungiyoyi ko kasashe masu gwagwarmaya da ita a yankin. Kuma idan haka ya faru raunin sojojin HKI zai bayyana a fili a duk wani yakin da zata shiga nan gaba a yankin Asiya ta kudu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar December 2, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa ( Ritaya) A Matsayin Ministan Tsaro December 2, 2025 Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa December 2, 2025 Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu. December 2, 2025 Iran Bata Taba yin Watsi Da Diplomasiya Ba Amurka Ce Ke Kai Mutane Bango December 2, 2025 Shugaban Kungiyar ECOWAS Ya Gana Da Shugaban Mulki Soji Na Kasar Guinea Bissau December 2, 2025 An Bude Taron Bikin Cika Shakaru 41 Da Kafa Kungiyar Tattalin Arziki Ta ECO A nan Tehran December 2, 2025 Araghchi: Halayyar Amurka ce yin matsin lamba maimakon diflomasiyya a dangantaka ta kasa da kasa December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tana fama da karancin sojoji rassan sojojin kasar karancin sojoji a kara da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu.
Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka tafi gona domin yin roron wake lokacin da aka afka musu.
NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a JigawaYa ce: “An fara kai hari ne ga mutane 15, wasu sun tsere, wasu kuma aka sake su ba tare da sharaɗi ba. Amma har yanzu mutum 11 suna hannun ’yan bindiga, kuma sun buƙaci a biya su kuɗin fansa na naira miliyan biyar,” in ji shi.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Talata, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazavar Jama’a/Sanga, Hon. Daniel Amos, ya bayyana satar mutanen a matsayin mugunta da rashin tausayi, tare da yin Allah-wadai da kai hari kan talakawa masu aikin halaliya.
“Muna buƙatar kara tsaurara tsaro, yin amfani da dabarun bayanan sirri, da ɗaukar matakan gaggawa da haɗin gwiwa domin kwantar da hankalin jama’a da kuma ceto waxa0nda aka sace,” in ji shi.