An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa
Published: 2nd, December 2025 GMT
Majalisar Dattawa ta sanar da aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta waɗanda suka haɗa har da na tsaro da na tattara bayanan sirri, sakamakon ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban Majalisar Dattawan, kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman na yau Talata.
A sabbin sauye-sauyen da majalisar ta aiwatar, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa.
An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi daga kujerar kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri a makon da ya gabata.
Haka kuma, Sanata Mustafa Musa daga Yobe ya karɓi ragamar shugabancin kwamitin tsare-tsare na ƙasa.
A ɓangaren kwamitin Sojin Sama kuma, Sanata Osita Ngwu daga Enugu wanda shi ne mataimakin shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa ya zama muƙaddashin shugaban kwamitin bayan rashin lafiya ta hana tsohon shugaban ci gaba da aiki.
Majalisar ta ce waɗannan sauye-sauyen na da nufin ƙarfafa aikin sa ido da inganta duk wasu hanyoyin ɗaukar mataki kan batutuwan tsaro da ke tasowa a faɗin ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamitoci Majalisar Dattawa shugaban kwamitin
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas : Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.
Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda ya tanadi dakatar da yaki da kuma cika alkawarinta.
Hazem Qassem, ya fayyace cewa ci gaba da neman gawarwakin fursunoni, duk da wahalhalun da suke fuskanta, yana nuna cikakken jajircewar kungiyar ga yarjejeniyar.
A wata hira da ya yi da Al Jazeera, ya kara da cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda ke kawo cikas ga aiwatar da ita.
Kakakin ya jaddada cewa ci gaba da neman gawarwakin fursunonin Isra’ila, duk da mawuyacin hali, yana nuna cikakken jajircewar Hamas ga sharuddan yarjejeniyar.
Hazem Qassem ya kuma yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa gwamnatin mamaye lamba don ta cika dukkan wajibai, gami da bude hanyar shiga tsakanin Rafah da kuma ƙaddamar da mataki na biyu na yarjejeniyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani December 1, 2025 Tawagar ECOWAS za ta je Guinea-Bissau, bayan juyin mulkin soji December 1, 2025 Ministan Harkokin Wajen Turkiya Ya Isa Birnin Tehran Kuma Ya Gana Da Takwaransa Na Iran December 1, 2025 Pezeshkian: Makiya na neman kawo cikas ga ci gaban kasashen Musulmi December 1, 2025 Maduro Ya Gargadi Amurka Game Da Hankoron Mamaye Rijiyoyin Mai Na Venezuela December 1, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Isra’ila Yayin Da Natanyaho Ke Neman Afuwa Kan Batun Cin Hanci Da Rashawa December 1, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Saudiya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran. December 1, 2025 Lebanon: Sakon Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma December 1, 2025 Ireland Ta Sauya Sunan Wurin Shakatawa Daga Na Shugaban “Isra’ila” Zuwa Na Shahidiyar Falasdinu November 30, 2025 Gaza: Sau 590 “Isra’ila” Ta Keta Tsagaiwa Wutar Yaki November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci