Aminiya:
2025-08-13@16:05:28 GMT

Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki

Published: 13th, August 2025 GMT

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba.

Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a.

Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno Lafiyar Tinubu kalau – Soludo

An yanke wannan hukunci ne bayan majalisar ta karɓi rahoto daga kwamitin karɓar koke-koke na jama’a, wanda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa, ya jagoranta a zaman ranar Laraba.

Majalisar ta kuma umarci ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta jihar da ta bai wa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar damar riƙon muƙamin shugaban har sai an kammala bincike.

A cewar rahoton, an zargi Yau da haifar da rigima tsakanin shugabannin siyasa da kansiloli, bayar da kayayyakin gwamnati ga magoya bayansa, rabon takardun shiga makarantar Dangote da takin zamani ba tare da adalci ba.

Hakazalika, an zarge shi da sayar da takin gwamnati sama da farashin da aka amince da shi na Naira 20,000 ba tare da sanar da kansiloli ba.

Har ila yau akwai zarge-zarge da suka haɗa da rashin gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen shiga daga kasuwanni da kuɗaɗen harajin dabbobi, sayar da rumfunan kasuwa ba tare da izini ba.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da raina dattawan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki, da kuma yin amfani da kuɗaɗen ƙaramar hukuma ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamitin ya zauna da ɓangarorin biyu a ranar 11 ga watan Agusta, inda shugaban ya musanta wasu daga cikin zarge-zargen amma ya amince cewa ya ƙara Naira Naira 2,000 a kan farashin takin zamani da gwamnati ta amince da shi.

Bisa ga sashe na 55 na dokar ƙananan hukumomi ta shekarar 2006, kwamitin ya tabbatar da dakatar da shi domin gudanar da cikakken bincike.

Sannan ta umarci a miƙa dukkanin takardun kuɗi da na gudanarwa na ƙaramar hukumar cikin kwanaki bakwai.

A zaman majalisar na ranar Laraba, wanda kakakin majalisar Ismail Falgore ya jagoranta, majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dokoki Shugaban Ƙaramar Hukuma Zarge zarge zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Ƙarin Kasafin Kuɗi Na 2025

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tattaunawa da amincewa.

 

Bisa wasikar da bangaren zartarwa ya aika wa Majalisar, ana neman amincewar ta kan ƙarin kasafin kuɗi na kimanin Naira biliyan 170 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fadin jihar.

 

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya bayyana cewa bangaren zartarwa yana neman wannan ƙarin kuɗi ne domin gudanar da ingantattun ayyuka da za su amfani rayuwar al’ummar jihar.

 

Bayan tattaunawa, ‘yan majalisar sun mika kudirin ga Kwamitin Majalisa kan Kasafin Kuɗi domin yin bincike da shirye-shiryen aiwatar da dokokin da suka dace.

 

A wani labarin kuma, majalisar ta karɓi wasika daga bangaren zartarwa mai ɗauke da sunan Barrista Saidu Yahaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC).

 

Nadin nasa ya biyo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Barrista Muhyi Magaji Rimin Gado.

 

An mika sunan sabon shugaban zuwa ga Kwamitin Majalisa kan Ƙorafe-ƙorafe domin ci gaba da tantancewa da gudanar da matakan doka.

 

Majalisar ta dage zaman ta zuwa washegari Talata 12 ga watan Agustan 2025.

 

Khadijah Aliyu

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Rano Na Tsawon Watanni Uku
  • Shugaban Tinubu Ya Rantsar Da Farfesa Dakas James Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki Ta Kasa
  • Wani Bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Karbe Mulkin Jihar
  • Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025
  • Yajin Aikin NLC Da TUC Ya Gurgunta Ayyukan Gwamnati A Taraba.
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Ƙarin Kasafin Kuɗi Na 2025
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
  • Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19